_*HASKE A DUHU*_
_*Book one*_
_*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_
_*FITATTU SHIDA NA KUD'I NE*_
_*Follow me on Wattpad please*_@meeshalurv
*Page 16*
_*ABUJA*_
D'akinsa ta nufa da gudu Dan tana tsoron Kar abinda ya fad'a ya faru tanason jikan nata, ba tason wani Abu ya faru da shi, buga k'ofar d'akin nasa Amma Yana jinta yak'i bud'ewa Kiran sunansa take tana rok'anshi ya bud'e Amma yayi shiru ya k'yaleta Yana dariya domin ya rama abinda tayi masa, cikin muryar kuka tace d'annan kayiwa girman Allah kayi hak'uri ka bud'e min k'ofar indai fad'a ne Wallahi na daina yima maka Dan Allah ka bod'e."
Jin ta rud'e yasa ta dawo ya dawo bak'in k'ofa ya rik'e murya, kamar marar lafiya Mai jin jiki, yace "Nidai Hajjah Dan Allah ki k'yaleni tunda bak'i k'aunata kullum fad'a kike min kawai ki barni na mutum ki huta tunda Baki k'aunar ganina."
Wani tashin hankali taji ya dirar Mata taji cikinta ya murd'a saboda Bata k'aunar tashi hankalin Sultan itama halinshi ne ta tsana yanajin mutum Yana magana yayi Masa shiru kamar gunki, sannan gashi sai ya d'auko Abu duk abinda zata fad'a mishi ya Bari bazai Bari duk abinda yakeso shi zaiyi shiyasa take jin haushin shi suke yawan fad'a idan sun zauna Amma duk duniya ba Wanda take k'auna sama dashi.
"Kayi hak'uri d'an Allah Wallahi na daina Kuma indai aurene na amince za'ayi daga yau bazan k'ara fad'a ba indai hakan zai faranta maka Rai kaji shalele na Kuma Wallahi na daina yima fad'a ka yarda ka bud'e"
Shiru yayi sai can yace "nidai ban yarda ba kawai ki tafi tunda kin samu Wanda ya fini."
Jin furuncinshi yasa cikin ta ya k'ara murd'awa dama Hajjah Bata iya tashin hankali ba ko kad'an Bata k'aunar tashin hankalin Sultan yanzu ta rud'e ganin Haka da yayi yasa ta fara gudawa saboda ambatar zai mutuwa, itako batason taji Yana fad'in zai mutum duk sai ta rud'e.
K'ara murd'awa taji yayi cikin taji ba abinda take buk'ata sai ta zagaya toilet gashi k'afar ta rik'e cikin tashin hankali ta jin azabar ciwo tace "Wash" da k'arfi ta sulale k'ofar part d'insa tayi zama Yan bori..
Jin abinda ta fad'a muryarta da alamun ciwo yasa cikin sauri ya bud'e k'ofar, fitowa yayi Nan yaganta rik'e da ciki zaune k'ofar d'aki tana ganin fitowarsa yasa tace ya d'auketa ya kaita band'aki.
D'aukarta yayi chak yayi cikin d'akin shi da ita toilet d'insa ya kaita ciki toilet d'in bedroom d'insa ya ajiyeta janyo Mata k'ofa yayi cikin tausaya Mata Bai so abin ya Kai Haka ba shima d'an Dole yasa yayi Mata Haka yagaji da sababinta domin yanzu ko zata cigaba tunda halinta ne baza ta iya dainawa ba...
Wasa Wasa sai ka Hajjah na zarya cikin lokaci kad'an har jikinta ya saki Dole ya Kira docter d'in gidan yazo ya dubata ya d'ora Mata drip Dan samu k'arfin jikinta tuni sultan ya rud'e duk ya had'a zufa ganin halin da Hajjah ke ciki shi kanshi Abba ya Shiga tashin hankali, ganin yadda jikin Hajjah yayi cikin lokaci kad'an gashi yayi Mata tambayar duniya ta fad'a Masa abinda ya faru da ita har Haka ta faru tak'i fad'a saboda tasan tana fad'a zai hau Sultan da masifa ita kuwa duk Wanda zai tab'a jikanta baza ta k'yale ba ko Abba ne da ya haifeshi Bai Isa gata a kwance idan ta fad'a baza ta iya tare wa Sultan fad'an da Abba zanyi mishi da tagaji ma cewa tayi ya tafi taji sauk'i saboda da shigowar Mom ita Kuma Bata k'aunar ganinta ta tsaneta, shiyasa tace su tafi taji sauk'i sultan kad'an ya Isa yayi jinyarta ba sai sun tarar Mata ba (Hajjah ba dama Baki dai baya mutuwa har yanzu) can Safnah ma yashigo saboda Mom ta matsa Mata ita ko kad'an Bata son Hajjah saboda yadda ta tsaneta Bata son aureta da sultee ta yasa itama tayi mugun tsanarta ko da Mom tace Bata da lafiya taje ta duba ta cewa tayi "Allah yasa ta mutu Kar ta tashi" da "Ameen" mom ta ansa Dan itama ba k'aramin tsanarta tayi saboda yadda take Bata Mata aiki yanzu ne ma har ta samu tayi nasara akanta shiyasa ma tazo....
YOU ARE READING
HASKE A DUHU
ActionIta Duniya juyi juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar wahainiya k'addara na fad'awa mutum Mai kyau ko akasin haka, sai dai anason fatan samu cin jarabawar da ubanjiki yayi maka. Rayuwa ta na tafiya k'an tafark'in k'addara tun bansan miye duniya ke...