🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*Story
&
Written by
*MRS NOOUR (PHEEYMARRH)*WATTPAD *@Pheeymarrh*
Email@ *Pheeymarrh@gmail.com*بسم الله الرحمن الرحيم
*Ya Allah ina rokon ka ka bani ikon farawa da kammalawa cikin amincin ka,ka sa mu amfana da abubuwan dake ciki(ameen)*🤲🏻
🅿➡1⃣
Zufa ce ke yanko mata ta ko ina na ilahirin sassan jikinta musamman goshinta da fuskarta wanda ya soma jiƙa ɗan ƙaramin mayafin dake yafe bisa kanta saboda tsabar rudewa da jin abunda amintaccen kuma yardajjen bokan nata ya fada,
Muryar ƙawarta hajiya ƙarima ita ta ƙatse ta daga dogon tunanin data keyi tunda taji bayanin boka wanda yaso tarwatsa zuciyarta ta buga,
"Mulki ke hannunka mai tukunyar mulki ka gafarce mu bamuda wanda zai share mana wannan kukan sai kai hajiya tayi kuskure ayi mata afuwa domin hajiya bata da inda ake share mata hawaye da bakin ciki kamar nan ɗin gareka boka mai tukunyar mulki mai iko akan komai ayi mana afuwa yadda kace hakan za'ayi boka"
hajiya karima ta ƙarashe maganar tana daɗa ranƙwafawa haɗe da ɗukar da kanta gareshi cike da tsananin tsoro da fargaba akan kuskuran da babbar aminiyar tata Hajiya Hama ta aikata na musantama boka akan duban dayayi masu,,Ita kanta hajiya Hama dake zaunen dukkannin jikinta rawa yakeyi tun razananniyar ƙarar da bokan ya sakar mata wacce take cike da ƙaraji da hargowar daya girgiza bishiyoyi da duwatsun da ke zagaye da su,
hannun ta na dama ta ɗago da kƴar ta goge zufar dake jiƙe kan goshin ta zuwa fuskarta,tana haɗiyar yawu da ƙyar cike da fargaba ta buɗe baki tana ƙara kwantar da kai ta soma faɗin "ayi hakuri a gafarceni nayi kuskure mai girma boka mai tukunyar mulki, ka taimakeni kamar yarda ka saba akoyaushe banaja da umarnin ka, ko aikin ka wannan ɗinma na shiga ɗimuwa ne sosai dajin bayanan ka har tunani na yaso gushewa" ta ƙarashe maganar cikin tsananin fargabar kozai hakura ɗin domin ta sani muddin ka musa ko kayi kokwanto akan aikinsa to koda kuwa biliyoyin kuɗi zaka bashi bazaiyi aikin nan ba,
ita kuwa a yadda ya binciko mata tabbas idan har bai taimaketa ba ta shiga uku ta lalace batasan ina zata dosa ba domin shi kaɗai ta dogara dashi,,
!shekaru talatin baya da suka wuce kin aikata irin wannan kuskuren wanda ya haifar maki da mummunan fushi da hukunci na don haka a yanzu ma dole zan hukunta ki wanda zai zama na ƙarshe don haka ku tashi ku bani wuri aure dole za'ayi domin kun ƙarya doka ta,
don haka kuje bayan auren ku dawo duk abunda za'ayi a lokacin za'ayi,don haka !!!ku bace min da gani!!!
Ya ƙarshe maganar cikin tsananin fushi da ɗaga muryar daya haifar da tasowar wani irin baƙin hayaki ta kowanne barayi na cikin jejen,,Jiki na matuƙar rawa suka suri jakunkunan hannunsu tare da ajiye masa wata ƙatuwar baƙar leda wacce maƙodan kudaɗe ne cike a cikinta, suka soma tafiya cikin tsananin sauri da gudu gudu tamkar zasu tashi sama,
tafiyar kusan minti talatin sukayi cikin jejin, babu wacce ta iya cewa ko a acikin su saboda tsabar tashin hankali da fargaba haɗe da tsantsar damuwar dasuke ciki,
har suka isa ga danƙareriyar motar dake ajiye a inda suka parker ta,,
hajiya karima ita tayi ƙarfin halin amsar key motar ta budewa hajiya Hama ta shiga kafin ta zagaya ta shiga itama ta zauna takalman su dake zube a motar hajiyar karima ta dauko ta miƙawa hajiya Hama nata kafin itama ta sanya nata (domin dokace ta boka ba'a sanya takalmi cikin kungurmin jejen ),
Tafiyar awa biyu ta kai su cikin babban garin na Maiduguri,inda babu bata lokaci suka isa baban filin jirgi dake garin,private jet ɗin hajiya Hama da suka zo a ciki a yanzu ma shiya ɗauke su zuwa babban birnin tarayyar wato Abuja,
YOU ARE READING
ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)
Mystery / Thrillertsantsan makirci mai cike da kulli mai matuƙar sarƙaƙiya