🅿9⃣

71 6 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

  🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
      
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*

WATTPAD *@ MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰

🅿➡9⃣

Sosai Sa'ad ya dage  tare da maida hankali sosai wurin karatu har ya kammala digree ɗinsa a fannin siyasa,a makarantar ne Allah ya haɗa shi da Mammi.

Asalin iyayen Mammi sun kasance yan garin kano ne suma,Mammi wato Hamanatu ta kasance ƴa ɗaya tilo a wurin iyayen ta wanda suka jima da aure ba tare da sun sami haihuwa ba har mahaifin Mammi ya soma neman  wani auren  don yana son ganin tsatson sa shima,tun daga nan ne ƙawayen Mama suka sanya ta akan hanyar bin gidajen malamai har da wurin bokaye inda da ƙyar aka samu cikin Mammi tayi kuma nasarar dakatar dashi daga zancen ƙara aure,tun daga wannan lokaci Mama ta maida akalar nasara da rashin ta a wurin bokayen ta komai ya faru ko ta ke yunƙurin yinsa sai da faɗar bokaye,

Ƙarfin jini da nono ba wasa ba hakan ya sanya Mammi tashi da halayyar  da ta fi na Mama sosai wanda ko soyayyar Sa'ad ɗinma kusan da taimakon bokaye ta karkato hankalin sa gare ta saboda kyauwunsa da ƙuɗinsa duk da mahifin ta daidai gwargwado yanada arziƙin sa,,

Basu sami wata matsala ba daga bangaren iyayen kowa kowa cikin hukuncin ubangiji akayi aure sukayi zaman su lafiya,
Inda Mammi ta cigaba da karatun ta daddy ma yana karatun tare da kasuwanci wanda yake irin na mahaifin sa,yana kuma taɓa siyasa ƙadan-ƙaɗan.

Suna zaman su lafiya da yake Mammi macece mai tsananin wayo da iya ƙirsa akan abunda take so ko a waje netake mu'amala da mutane bata fitowa fili da duk wani mugun nufin ta zata kwantar da kai ta nuna maka tsananin ƙaunar ka take,hakan ta kasance tsakanin ta da Hajiya mahaifiyar daddy wacce ita sam Mammi bata kwanta mata a rai ba saboda samun labarai akan mugun halayyar su ita da uwar ta amma da yake Mammi tasan kanta hakan take kwantar da kai take bin Hajiya duk da tsananin faɗa irin nata har sai da ta samu mallake Hajiyar.

Arziƙi sosai ya soma ɓullowa da Daddy saboda faɗawar sa siyasa sosai ga kasuwancin da yake shi ɗin akwai ilimin zamani sai yake haɗawa da hulɗa da ƙasashen waje wurin sayo kaya har da saidawa ma,
Rashin haihuwa shine abunda itama yaso ya kawo mata matsala a zaman nasu wanda a lokacin suka tasanma shekaru bakwai babu koda ɓatan wata balle ɓari har ta kaiga sanya ran haihuwa,hakan ya sanya ta dagewa wurin bin bokaye babu ji babu gani tare da babbar ƙawarta wato karima,har Allah ya haɗasu da wani shahararran ƙasurgumin malami marar tsoron Allah a chan cikin wani ƙauye Biyumne dake cikin ƙananan ƙauyukan maiduguri,

Cike da ƙwarin gwiwa suka shirya tafiyar inda babu wacce ta samu matsala wurin mijinta saboda an riga an gama malleke su kamar yadda suka samu tabbaci a labarin irin aikin bokan haka suka samu inda ya ba Hajiya Hama magani yace tayi wanka na kwana uku kullum kafin ta kwanta da mijinta tabbas ba zata wuce watan ba zata samu ciki,godiya sosai sukayi masa inda ta zube maƙudan kudaɗe,

Har sun miƙe zasu tafi boka ya tsaida su,ya soma wani sabon surkullen inda ya dauki ɗan lokaci kafin ya dakatah yace wa Mammi lallai mijin ta zai ƙara aure nan da sati biyu,kuma aure ne wanda zai iya sanadin ta har ma da abunda zata haifa,

Tun kafin boka ya rufe baki Mammi ta soma girgiza kai cikin rashin gamsuwa da gasgasta abin da boka ya faɗi,lokaci ɗayata shiga tsananin tashin hankali da firgici da jin abin da bokan yace wanda har ya sanyata mantawa da sharuɗɗan shi daya soma gaya masu.

Cikin tsananin  tashin hankalin ta soma faɗin"ƙaryane ƙaryane wallahi sa'ad bazai taba iya yi mun kishiya ba wallahi,wannan sam ƙarya…"

"Ƙeeeeh!hajiya tashi kubar wurin nan ni zaki ƙarya ta,ki ƙaryata aiki na,ku tashi ku bace mun daga gani tun kafin kamannin ku su sauya"ya  ƙarashe maganar cikin tsananin hargowa da ihu da razani wanda ya sake razana su suka miƙe jiki na rawa Hajiya karima ta kwashe jakunkunan hannun su tai gaba tabar Mammi wacce har ta juya sai kuma ta dawo ta zube gwiwa ƙasa ta soma roƙonsa ya taimaka mata,

Tsawar dai ya sake daka mata yace baya taba taimakawa in har aka yi kokwanto akan aikin sa balle ita data ƙaryata shi,dole haka ta miƙe ta tafi cikin tsananin tashin hankali take taka ƙafa sa'ilin da shi kuma ya shigaba da jefan ta da kalamai masu ɗaga hankali wanda take jinsu tamkar wuta yake watsa mata"dole mijin ki zai ƙara aure,dole zata haifa wanda yafi naki,kuma itace silar baƙin cikin ki da mutuwar ki har da ta abunda zaki haifa"har tabar cikin jejin nan yana sake jaddada mata irin musibu dake cikin auren wanda hukuncin ubangiji ne kawai ya sanya zuciyar ta bata buga ba,haka ta tadda ƙawarta suka hau motar su suka nufi gida.

Kai tsaye gidan Mama suka wuce da ƙyar suka iya kwantar ma Mammi hankali akan zasu nemi wasu malaman tunda bashi ƙaɗai ba ne boka a duniya,dole ta hakura ba wai don ta hakuran har cikin zuciyarta ba illa dai tana fata kamar yadda yadda suka ƙarfafa tan mafanin haihuwar yayi aiki,
duk yadda taso danne ranta kasawa tayi ko yaushe tana cikin damuwa da tashin hankali duk da Daddy ya tabbatar mata da babu wani aure da yake nema bayan ita bai taɓa soyayya ba amma ta kasa samun nutsuwa kullum maganganun boka yawo suke mata a zuciya suna sanya mata fargaba a zuciyarta kullum Mama da ƙawarta  tafe suke gidan malamai,amma hankalin ta baya gamsuwa da duk abin da bokayen ke faɗa.

_Bayan sati biyu_

Duk yadda bawa ya ɗauki al'amarin ubangiji ya zarcen nan kamar yadda mutuwa ke riskar bawa a lokacin da bai shirya ba,haka kamar yadda arziƙi ko talauci ya kan saukar wa bawa lokaci ɗaya haka kaddara mai kyau ko akasin ta ke cimma bawa a lokacin da bai sani ba hakan ce ta kasance ga Alhaji sa'ad haske wanda a yau dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren sa da Asma'u kamar yadda boka ya tabbatar a nashi tunanin wanda Allah ne ya bashi ikon yasan da hakan ya kuma hanashi sanin hanyar da zai iya dakatar da wannan aure kamar yadda so saboda ubangiji bai kadarci zai iya yin hakan ba,bawai kuma tabbatar wasshi  ce ta sanya dole akayi auren ba illa hakan yana cikin kaddarar Asma'u da Sa'ad na tabbatuwa a ƙarƙashin ni'ima ɗaya ta aure wanda dukkanin daga Asma'un har Alhaji Sa'ad ɗin basu tsammata  ba.

Haka aka ɗaura aure suka tattaro tare da tawagar ƴan siyasar su da sukaji ɗaurin aure gidan mai martaba sarki yola Alhaji lamiɗo haruna usman wanda akayi bikin ƴar sa a ranar,

Daddy bai iya sauka gidansa ba sai dai gidan Hajiya ya zarce da Amarya Asma'u wacce daga ita sai kayan jikinta ƴar atampa ce marar tsada da mayafi wanda shima kallo ɗaya zakayi masa kasan yaji jiki bayan koɗewa dayayi,,q

Kamar yadda yake ta tsoro sai kuma Allah ya taimake shi Hajiya ta amshi Asma'u hannu bibiyu duk da baiyi mata bayani ba ya ce sai dare zai zo suyi maganar gaba ɗayansu.

Haka ya wuce gida yana addu'ar Allah ya kawo mashi mafita lamarin yazo mashi da sauƙi,a gidan ma kasa samun nutsuwa ya yi kwata-kwata saboda sanin halin Mammi duk da yana ganin ita ɗin mai saukin fahimta ce sai dai shi kanshi yasan yayi mata laifi babba na yin auren ba tare da sanar mata ba musamman in ya tuna sati biyu da suka wuce data ritsa shi akan zancen ƙarin auren amma ya tabbatar mata da ba aure zaiyi ba,yasan baza ta taɓa fahimtar shiba zata yi tunanin boye mata yayi,

Washe gari da safe ya ɗauki Mammi su ka tafi gidan bayan gaishe gaishe ya soma sanar masu abin da ya faru kamar haka,

*Mrs Noour ce*🥰

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)Where stories live. Discover now