🅿️➡️2️⃣5️⃣

41 6 2
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

  🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
      
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*

WATTPAD *@ MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰

🅿️➡️2️⃣5️⃣

Tunowa da tayi da abin da ya faru da ita ya sanya ta saurin buɗe lumsassun idanuta cire kanta tayi daga ƙirjin shi tana sakar mashi murmushin haɗe da sake fitar da wasu hawayen,
  Ƙasa tayi da kanta tana jin duk ta tsargu zuciyar ta sai lugude take yi ganin yadda ya tsare ta da idanu tamkar yana son gano wani abu tattare da ita.

Sake janyo ta yayi zuwa ga kirjinshi yana tattare hijabi ɗin dake jikinta,a hankali ya cire shi ya ajiye gefe yana sake ƙare mata kallo yana mamakin mai ya sanyata yin wannan ramar farat ɗaya,fuskarshi ya sake kawo kan Tata yana kokarin maimaita abinda yayi mata ɗazu,cikin sauri ta janye fuskar ta zuwa wani ɓarayin,sai da yayi jim kafin ya sanya hannunshi a gefen fuskarta ya juyo da fuskar tana fuskantar shi"nayi alƙawarin kula da su,hawayen ki ba abu ne da zan bari su zuba hakan na ba so Please let me"ya cigaba da lasar hawayen yayinda ita kuma take fitar dasu tamkar da gayya.

      Hannunshi ya sanya ya kamo kasan rigar ta ya buɗe a hankali yake shafa shafafen jikinta cikin kulawa,hakan ya sanya ta sake sake masa jiki tana jin abinda yake mata cikin ko ina na jikin ta har wani sanyi sanyi take ji yana lulluɓe ta,dole ta sake lumshe idanu tana jin ƙaunarshi sosai cikin jininta,cire hannunshi yayi yana zubawa lumsassun idanunta ido,yadda taji shiru ya sanya ta buɗe idanuwanta a hankali ta ware su kan fuskarshi,wani irin miyau ta haɗeye babu shiri na tsananin tsoron kallon da yake mata musamman yadda idanunwanshi suka sauya kala,ita ba yarinya bace kuma yanzu ilimi yayi yawa sosai babu jahilci ace wai mace bata san menene aure ba,shi ya sanya ta miƙewa daga jikin shi a hanzarce tana kokarin miƙewa tsaye.

Ruƙo tsintsiyar hannunta yayi yana buɗe mata haƙurarrun idanunshi,murya a taushe yace"zuwa ina kuma".
"em eh ruwa zan kawo maka bakaci komai ba ka daw....."saurin ƙatse ta yayi ta hanyar ɗora yatsar manuniyar shi a kan bakinshi ganin yadda duk ta daburce wanda hakan ya sake ƙara mata ƙima da girma a zuciyar ta yana matuƙar son wannan kunyar tata wannan shine abu na farko da ya ja ra'ayin shi akan son aurenta,bawai yana gudun aikata abinda Mammi ta sanyashi bane domin ya tabbatar da natsuwar Anisha har cikin zuciyarshi illah dai yana ganin hakan jahilci ne da kuma tonon silili wanda sam musulunci bai ce ayi hakan dole ba.

"ga ruwan wanka na haɗa maka"ta faɗa a sanyaye idanunta a ƙasa duk a ɗarere take tamkar ranar ta soma ganinshi,murmushin yayi yana mamakin sanda ta zare hannunta daga nashi har ta haɗa mashi ruwa wanka yana chan tunani.
      Har ya gota ta sai kuma ya dawo da baya yana rungume ta sosai a jikinshi ta baya,sunkuyo da kanshi yayi dai dai kunnenta cikin raɗa yake faɗin" waya gama maki amarya na aiki ehm?,its my duty na lura da ke bana son ki ƙara wahalar kun da kanki Please"

Shiru tayi ta kasa amsa mishi tana jin yadda numfashin sa ke shiga cikin uwar dodon kunnenta yayinda yake maganar"kina jinaaah"ya faɗa cikin fitar da iska,da sauri ta gyada kanta tana faɗin"uhm"sumbatar wuyan ta yayi kafin ya sake ta ya wuce banɗaki yana waiwayen ta yadda tayi still tamkar an dasa ta a wurin take ta ji hawayen ya ɓalle mata,a hankali take faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raju Allahumma ajirni fil musubati wa akhlifni khiran minha"dafe ƙirjinta tayi tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa cikin sauri sauri,da ƙyar ta iya jan ƙafarta ta ƙarasa bakin gadon ta zauna zuciyar ta cike da fargaba ta saƙa wanna ta kwance waccan wata zuciyar tana bata shawarar ta bayyana mashi abinda ya same ta yayinda wani ɓangare yake shawarar ta ta da kada ta soma ta,domin ba lalle ya yarda da ita ba,hannayen ta biyu ta ɗaga sama tana addu'ar Allah ya kawo mata ɗaukinshi da mafita,zamewa tayi ta kwanta bisa gadon har lokacin hawaye na zuba a idanunta,tana jin yadda cikinta yayi mata fayau har kulle mata yake yi,amma batajin zata iya sanya ko ruwa a cikin ta inba dole ba.

ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)Where stories live. Discover now