🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*WATTPAD *@ MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰🅿➡5⃣
Amarya Anisha zaune take ɗakin auntyn nasu wacce take kishiyar maman ta ana ta aikin murje mata jiki da dilka wacce auntyn ce keyi suka jiyo sallamar baban nata a parlon yana kwala kiran antyn,
dole ta aje ta wanke hannun ta a bathroom ɗin dake ɗakin ta fita tana faɗawa Anisha ta jira ta,
Fitar ta yayi dai dai da kiran daya soma shigowa wayar ta dubawa tayi 💘A tagani a rubuci a screen ɗin wayar murmushi ta saki kafin ta daga cikin siririyar sanyayyar muryar ta tayi mashi sallama tare da gaidashi lokaci ɗaya,,
Tana jiyo ajiyar zuciyar daya sauke kafin ya amsa mata murya a sanyaya wanda ita da kanta tasan akwai chanji sosai tattare da shi,
Shiru sukayi dukkan su na tsahon mintuna tana jiran taji ya magantu kamar yadda ya saba don ita takan rasa wace irin hirar zatayi masa koda yana ranta bata iya furtawa,
hakan shikuma Abeer ya tsunduma tunanin ta inda zai iya fahimtar da ita maganar janyewarsa ga ɗan uwansa wanda yana da tabbacin komai hakurin ta ba lallai ta fahimce sa ba balle ta amshi maganar sa in kuwa harta iya masa wannan alfarmar tabbas yasan zai tsunduma rayuwar ta cikin kunshi kamar yadda ya jefa tashi rayuwar musamman rayuwa da Azhar duk da yake ɗan uwansa amma yasani akaran kanshi mace yarinya kamar Anisha ta aure shi tabbas zata fuskanci ukuba da bakin cikin aure kafin tayi nasarar janyoshi gareta on har tayi dacen hakan in kiwa bata yi kenan hakan yana nufin ya shagoranci shigar ta cikin wani na kunci har ƙarshen ryuwar ta,anya kuwa wannan soyayya ce yake mata?,anya zai iya yafewa kansa kuwa?,Ajiyar zuciyar ya sake saki fiyeda da na farko wanda ya fara ɗaga hankalin Anishan har bata san sanda bakinta ya buɗe ta tambayeshi lafiya ba sakamakon ta na wacce bata tambayar mutum abu koda kuwa waye inhar baka furta mata ba,
"Lafiya kalau My Nisha kawai na kasa bacci ne tun jiya ina mafarkin kasancewar mata gare ni wanda nake ganin kwanakin nan biyu tamkar shekara dubu gareni,tamkar wanan ranar an kankareta cikin shafin rayuwata Nisha ina matuƙar kaunar ka sosi fiyeda yadda zan iya nuna maki amma ke naga kamar ba haka bane gareki please ki gayamun yaya darajar soyayyar ta take gareki"ya jefo mata tambayar cikin matuƙar karayar zuciya dake masa wani irin bugu wanda shi kansa yasan zuciyar sa bata da cikakkiyar lafiya tun a daren jiya,ta riga da ta tarwatse kamar yadda yake da yaƙenin tata zata iya tarwatsewar,,
Mirmushi ta sake wanda yana iya jeyo sa wanda yake ƙara dilmiyar da zuciyar sa gareta da sanya zuciyarsa sanyaya a duk halin dayake ciki banda yau domin kuwa ayau sai yaji zuciyar tasa nauyi ta sake masa hakan yasanya shi saɗa jingina sosai da fuskar gadon sa zazzafan hawaye ya biyo fuskarsa,,
Duk yadda takeda nauyin bakin wurin amsa masa irin waɗanan maganganu a yau sai ta tsinci kanta da son faranta mashi"maiyasa zaka yi mun wannan tambayar awannan lokacin bayan kasan ba lallai duk abunda zan faɗa ya iya bayyana abunda ke cikin zuciya ta ba ina roƙon zuciyar ka data ƙara hakuri na kwanaki biyun nan don ji da ganin irin yadda matsayin ka yake gareta"ta ƙarashe maganar tana rufe fuskar ta da ɗayan hannu tana sauke numfashi tamkar wacce aka tsora ta,,
YOU ARE READING
ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)
Mistério / Suspensetsantsan makirci mai cike da kulli mai matuƙar sarƙaƙiya