🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*WATTPAD *@ MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰🅿️➡️2️⃣1️⃣
Yadda taga Mammi na Safa da Marwa ta san babu lafiya,a tsorace ƙirjinta na dukan uku uku ta tsuguna daga nesa da inda take,tana faɗin"gani Hajiya"ajiyar zuciya Mammi ta sauke tana fatan ta samu abun da take so ta tabbata kuma duk cikin ma'aikatan gidan babu kamar ya Marwa wurin iya aiki da gulma da sa ido kai komai ma Marwa ta iya shi don ita kanta tasha raka Mammi wurin manyan malamai na ƙauyen su.
"Maza ki tashi ki nufi gidan Abeer kar ki tsaya sallama ko neman izinin ta ko na wani,in dai ba Abeer ɗin ne kika gani ba,chan cikin bedroom ɗin ta zaki shiga ki ɗauko min camara tana nan daga tsakanin saman drower a".
Jinjina kai Marwa tayi tana faɗin "toh Hajiya"ta miƙa da sauri ta juya"Marwa "Mammi ta dakatar da ita,juyowa tayi tana duban Mammi"kar ki bari a samu matsala na gaya miki,kuma wanna rawar jikin ki ajiye shi tun kafin ki fita daga ɗakin nan,muddin kika aikata wani kuskure toh tabbata karshen ki ne ya zo wallahi kin san ko Ni wacece da kuma mai zan iya yi"Mammi tana ƙarashe maganar tana zare mata idanu da jan kunne,"in Allah ya yarda baza'a samu matsala ba Hajiya"Marwa ta faɗa a sanyaye cikin aro jarumta ta fice daga ɗakin ta nufi na ma'aikatan ɗaya kasance na kwana su,mayafi ta ɗauka ta fice zuciyar ta cike da tamboyin da san bata isa ta samu amsoshin su ba,sai dai tayi alƙawarin bin diddigi don ta gane mai yake faruwa da amarya da ko cikakken sanin ta Mammi bata yi ba amma har ta fara jefen ta da mugayen abubuwa.
Yadda Marwa ta saki jiki tamkar ba wani abu ne ya kawo ta ba,bata yi wani mamakin ganin gidan babu masu tsaro ba balle ma'aikata ba,duk da lokacin garin safiya ne da yawan mutane basu tashi bacci ba, haka ya ke ga amarya Anisha wacce har lokacin maganin bai sake ta ba bacci take sosai,haka zalika ma gidan nata babu kowa hatta da maigadi bare ƴan aiki,har Marwa ta samu damar shigowa ta ɗauki abinda zata ɗauka ta fice,zuciyar ta na sake cika da tambayoyi da mamaki musamman ganin irin nannauyan bacci da Anisha keyi sannan gidan babu kowa,ga abubuwan da aka farfasa a ƙasa,ga jini da ya ɓarɓata ɗakin har zuwa parlor,da wannna tunanin ta koma gida ta nufi ɗakin Mammi da sallama ta tura kofar ta shiga.
A hanzarce ta juya daga kai kawon da take a ɗakin ta na duban hannun Marwa,hannun ta taciro daga cikin mayafi ta miƙa wa Mammi ƙaramar Camera tana faɗin"gashi Hajiya",
cikin sauri Mammi ta amsa tana juya ta zauna bakin gado tana sauke ajiyar zuciya.Tsaki taja da ƙarfi ta ɗauki wayar ta,layin Abeer ta soma nema rai a ɓace tana ayyana irin cin mutuncin da zata yi masa in ya ɗauki wayar tun kafin yazo,lallai dole in har ya kusnace matarshi ta chanza salo,dole zata ɗauki mataki kwaƙƙwara a kanshi da matar shi.
Sau biyar tana gwada kiran layukan shi amma shiru kowacce magana ɗaya ce a ke sanar da ita wayar a kashe take,dole ta hakura ta ajiye wayar.
camarar dake hannun ta tasoma jujjjuyawa zuciyar ta cike fal da mamakin da tambayoyin kan yadda wannan abu ya faru"shin dama Abeer bai je inda ta aike shi ba?,ko kuwa yana nufin a jiyan yaje ya gama ya dawo?,tsaki tayi tare da jefar da wayar gefe.
YOU ARE READING
ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)
Misterio / Suspensotsantsan makirci mai cike da kulli mai matuƙar sarƙaƙiya