page three

83 9 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

  🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
      

Story
        &
          Written by
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*

WATTPAD *@pheeymarrh*
Email@ pheeeymarrh@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰

🅿➡3⃣

Sai bayan sallar magrib aka gama zana masu kunshin wanda yayi matuƙar kyau musamman na amarya Anisha wacce tsananin tsantsi da sulbi fatar ta dake shan gyara ya ƙarawa lallan kyauda fitowa fes a fatar ta,

A mota suka tadda shi yana jiran su har lokaci,murmushi Anisha ta sake tana sake jin soyayyar sa na ratsa jinin jikin ta,
tun kafin su karaso ya fito ya buɗe mata murfin ƙofar yana sakar mata murmushi,martani ta mayar masa tana sadda kanta ƙasa,
saida ta zauna kafin ya rufe ya zagaya ya shiga mazaunin driver  yayinda Ni'ima ta shiga baya ya ja motar suka tafi,

Har cikin gidan ya shiga dasu wanda da sauri Ni'ma ta buɗe murfin motar ta fita cikin zaƙuwa don jiyo hayaniya daga cikin gidan tana faɗin "ango saida safe su hajja  sun iso"

Murmushi sukayi dukkansu Abeer na faɗi"mu tashi lafiya"
Itama Anisha cikin zakuwa ta kai hannu zata buɗe murfin motar amma taji ta a rufe hakan ya sanyata maida jikinta baya ta jingina da kujerar tana kallon shi fuska a kwaɓe cike da shagwaba tamkar zatayi kuka,

Murmushi yayi yana kai hannu ya kama hannunta  yana jefanta da wani irin kallo wanda ya sanyata sadda natakwayar idanun ƙasa,murza hannun ya shigayi a hankali yama faɗin "tukwuici na kenan duk zaman danayi na tsawon awa huɗu zaki iya tafiya ba tare da na soma sanyawa lallen nan albarka ba"ya ƙarashe maganar yana kissing hannun ta,,

Cikin sauri ta janye hannun saboda yadda tsigar jikinta ke tashi tana jin wani irin baƙon yanayi a jikinta tun lokacin dayasoma murza hannun wanda wannan shine karo na farko daya soma riƙe mata hannu,da kyar ta iya bude baki cikin tsananin kunya tace "ai zaka gani harka gaji da gani ma"

Mirmushi yayi yana kauda kai gefe yace"banajin akwai wannan lokacin a iya tsahon rayuwa ta da zan gaji kona ƙosa da ganin koda farcen kine balle wannan kyalkyawan hannun da babu wata mace mai sa'a hallitta kamar shi"

Murmushi kawai ta iyayi ba tare da ta iya cewa komai ba saboda nauyi da kunyar sa datakeji sa'annan ita ɗin ba gwanar magana bace,

Buɗe mata kofaryayi yana faɗin" ki gaida baƙi duka"
ɗaga masa kai kawai tayi ta fice tana "saida safe"
Sai da ya bar gidan kafin ta juya ta nufi ciki gidan kai tsaye ɗakin baki cike da murna ganin ƴan uwa ta nufi hajja kakarsu ta zauna a gefen ta cikin murmushi ganin yadda hajja ta baje uban kaya tana dubawa wanda yake kayan lefe ne akwatina sets biyar masu taukar kyau da tsada waɗanda suka ji uban kaya masu matuƙar kuɗi,sai faɗin suke lallai Anisha tayi dace ,,

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Zaune suke dukkansu iyalan gidan a bangaren Hajiya ana hira sosai wanda kusan rabin hirar ta biki ce sukeyi,
a haka muryar Azhar ta ƙarade parlon yana faɗin "yanzu tsohuwar nan saida kika rigani zuwa duk sammakon danayi" sai alokacin aka lura da shigowar shi
harara Hajiya ta watsa mishi tana faɗin"har yau dai Azar bazaka sauya hali ba ace sallama tayiwa ɗan musulmi wahala sai dai ka afko kai tsaye tsagal tsagal da kayan jajayen fata kullum"
dariya sukayi dukkansu cikin sauri Abeer ya miƙe suka rungume juna da Azhar,kafin suka zube kan kujerar da Hajiyan ke zauna,
Abeer na faɗi" kai hajiya daga shigowar shi ko sannu bakiyi mishi ba sai mita kamar kullum"

ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)Where stories live. Discover now