🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA**Mallakin*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*WATTPAD *@pheeymarrh*
Email@ pheeeymarrh@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰🅿➡4⃣
A matuƙar firgice Azhar ya farka gaba ɗaya ya birkice dukkanin ilahirin jikinsa rawa yake"not again"ya furta cikin tsananin damuwa da tashin hankali wanda bai taba shiga irin saba,
a firgice ya juya gefe jin an dafa ƙafaɗar sa,nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin ɗan uwansa ne Abeer ya hawo gadon fuskar Abeer cike da damuwa da tashin hankali yace"whats wrong with you bro,mai yafaru ne haka"ya ƙarashe maganar yana miƙa masa ruwan gorar dake hannunsa wanda yaje ɗauka ya sha bayan gama wayar shi Anisha sai kuma ya tsinkayi ihun Azhar ɗin wanda ya sanyashi shigowa a guje,
Ƙarɓa yayi ya ƙafa kai ya soma,tas ya shanye ruwa wanda yake mai matuƙar sanyi dukda yadda yaji daɗi da sanyin ruwan hakan bai hana nutsuwar shi rashin dawowa ba kuma har lokacin zuciyar sa bugawa take fat fat fat cikin tsananin sauri tamkar wanda yayi gudu,
"Lafiyar ka kuwa ko Mammi zan kira ne"Abeer ga sake jefo masa tambayar har lokaci yana dafe da kafaɗar shi,
girgiza masa kai yayi a hankali alamun eh yana zame bayan sa yajingina da pillow,runtse idanun sa yayi yana son nazari akan mafarkin amma zuciyar shi na tsorata shi kamar kullum,jinin daya tuna yana zuba a hannun ta yasake ƙara tayar masa da hankali cije lips ɗinsa yayi na ƙasa"wace ce wannan take bibiyana haka"ya jefowa kansa tambayar dayasan koda zai shekara ɗari ne bazai samu amsar ba,"My Azhar" ya tsinkayo miryar Mammi tana kiran sunan shi cikin tashin hankali,buɗe idanun aa yayi yana duban ta ba tare da ya iya amsawa ba ,bayan ta daddy ne da Hajiya dukkansu a ruɗe suke,
zama Mammi tayi kusa dashi tana kwantar da kanshi bisa ƙafaɗar ta,gorar hannun ta tabuɗe ta kafa masa a baki alamun yasha tana shafa kanshi da ɗayan hannun,
Ƙaɗan ya sha ya cire bakinsa dukkan su suna masa hannu,"Sannu Azar kaji miyagu sun tasa ka gaba tun kana ƙanƙanin ka,da da girman kane da sai ince ko wata ka haikewa take bibiyar rayu..."
"haba Hajiya,Haba don Allah"Daddy ya katse hajiya daga zantukan datake ransa a ɗan bace ya cigaba da faɗin"don Allah ki bar wannan maganar ki duba halin dayake ciki mana a duk sadda yaron nan yake kasar nan bashida kwanciyar hankali abun yafara bani tsoro kuma tin yana ƙankanin sa dole zuwa gobe zan nemi malamai su bincika min shi gas...""Aa Daddyn"Mammi tayi maza ta katse shi cikin tsananin tashin hankali"ka bari a cigaba da wannan ɗin tunda inyasha yana samun lafiya please kasan malaman nan wasu duk macuta ne kawai karka manta irin wahalar da mukayi tayi tun yana ƙaramin sa a vanza har saida Allah ya haɗamu da wannan mai tsoron Allah,hakuri zamuyi mucigaba da mishi addu'a kawai"ta ƙarashe maganar cikin tsoro tana fatan daddyn yayi na'am da maganar ta,
Ajiyar zuciya daddyn ya sauke mai nauyi da tuna irin magungunan da sukayi tayi kama daga na asibiti har na gargajiya amma a banza"shikenan Allah ya yaye masa"ya furta cikin sarewa duk da yadda zuciyar shi takeson sake nema ma Azhar ɗin magana amma bayajin zai iya musa ma Mammi maganar ta,
Ameen" suka amsa dashi dukkansu banda Azhar daketa haɗa gumi sai dai rawar jikin nashi dayayi sauki,
Kwantar da kanshi Mammi tayi akan pillow ta miƙe tana faɗin bari akawo masa abinci don nasan ba lallai in yaci ba sai ya kwanta,,
YOU ARE READING
ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)
Детектив / Триллерtsantsan makirci mai cike da kulli mai matuƙar sarƙaƙiya