p sixth

83 9 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻


  🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
      
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*

WATTPAD *@ pheeymarrh MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰

🅿➡6⃣

"Baba bana son auren nan don Allah a barshi bana so Ba ba"ta ƙarashe maganar kuka na cin ƙarfin ta wanda har sheɗewa takeyi,

Dukkansu tsura mata idanu sukayi ba tareda kowa ya iya magana ba saboda mamakin abunda Anishan take faɗa domin kuwa komai kunyar ta da rashin son maganar ta kowa ya san irin tsananin soyayyar da take yiwa Abeer,

Baba ne ya dafa kanta cikin sigar lallashi ya soma faɗin"maiya faru ne Anisha da duk hakurin ki kika kasa hakuri dashi ko kuwa akwai wani mugun abunda kika binciko gameda Abeer ɗin ko iyayen sa bayan abunda muka sani a kuma wannan kurarren lokaci Anisha,natsu ki gayamun zan san yadda zan dau mataki kinji"ya ƙarashe cikin kwantar da murya da lallashi ganin lallai da gaske take akan maganar data zo dashi,

Nan ta kwashe komai ta faɗa masu tana faɗin"wallahi bazan iya ba baba wanda ban taba ganinsa ba bai nuna ra'ayin sa a kaina ba taya Abeer yakeda iko akaina domin farin cikin ɗan uwansa wannan wasa da cin amana ne a soyayya"

Ni'ima ce ta miƙe tsaye ta ƙaraso wurin Anisha tana riƙe ta tace"wallahi bazai yuwuba anty talauci aiba hauka bane balle namu talaucin ai baikai fa mun fara neman taimako wurin su ba wallahi Aunty ina bayanki a hakura da auren duka idan har…"

"Keeh amshi nan,amshi nan nace ƴar banza"Baban ya ƙatse Ni'ima cikin fushi yana watsa mata hannu"Vavu abunda za'a fasa koda kwana ɗaya babu ɗari balle hakuri da Aveer ɗin da Azhar ɗin ai abu ɗaya yayisu uwar meye banbancin da ku yaran yanzu kun daurawa ranku soyayyar banza ta zamani,cha nake shi Abeer ɗin da kanshi ya hango maki farinciki tattare da ɗan uwan sa fiyeda shi kanshi don haka wannan ba matsala bace muddin zai baki ci da sha da rufin asiri,maza ku miƙe domin shirin partyn naku"ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya da nuna bacin rai,,

Ɗago Anisha Ni'ima tayi tana turo baki gaba ta rungume ƴar uwarta suka fice tana lallashin ta,

Auntyn ce ta kasa shiru tace"amma ya kamata daka tsaya ka duba wannan zancen tabbas bafa ƙaramar magana bace taya zasuyi wasa da hankalin muta…"

"Keh dakatah"baban ya katse ta cikin matuƙar harzuƙa"dakata mun nace uwarta ce gatanan ya nuna mahaifiyar Anisha wacce ke zaune tamkar bata ɗakin,uwar tace gatanan bata sanya baki akan hukunci naba sai ke uwar rawar kai saboda kinga na sakar maki ragamar ƴaƴan toh karki kawo min zancen banza akan wannan ɗan ƙaramin dalilin duk irin faɗi tashin danayi akan ganin takai matakin nan  indai ɗa ɗan gidanne wallahi kowaye shi basa zanyi zancen banza zancen wufo kenan,kuma wallahi wannan magana abarta a iya nan an gamata kar kusake koda wasa ku nuna cewar daman bada shi wannan yaron za'ayi ba tun farko"yana gama faɗar haka ya miƙe yana zan tsaki ya fice daga gidan,,

Auntyn ce ta juyo ga kallonta ga Mama tana dubanta a ranta tana faɗin wannan wace irin mace haka da komai zaka yimata bazata taba ɗaga kai ba balle ta nuna tasan kanayi"yanzu maman Anisha har a rayuwar ƴaƴanki vazaki taba ƙarɓa masu ƴancin suba haka zaki zuba idanu akanta rayuwar aure fa ake magana akai,rayuwa wacce ake fatan sai mutuwa kin gwammace ƴarki ta dawwama cikin ƙunci har ƙarshen rayuwar ta bayan kinji irin halayyar Azhar ɗin"aunty ta faɗa cikin vacin rai,

ƘARSHEN ALEWA (ƙasa)Where stories live. Discover now