Babi na Goma Sha Bakwai

3.7K 394 90
                                    

☆17_Arashi!☆


Falo ne madaidaici, wanda yaji kayan alatun rayuwa iri-iri. Idan wani ba da gaske yayi ba ya shiga cikin falon, zai iya cewa teleporting dinshi aka yi zuwa shahararren dakin sayar da kayan dakinnan na birnin Jeddah, wato 'shar sahr'. Kodayake in a sense, rabin kayan daga can suke.

Mukhtar ya tura kofar falon ya shiga, kanshi a kasa yana kokarin balle link din hannun rigar kaftani daya sanya, wata dakakkaiyar shadda dark green tana ta sheki da walwali.
Bai san da mutane a cikin falon ba sai da yaji an tabo bayan gwiwarshi. Ya daga kyawawan idanunshi masu haske da sheki, lokuta da dama idan ya kalli mutane dasu sukan yi zaton barci yake ji ko kuma daga barcin ya tashi, saboda yadda zara-zaran bakaken dogayen gashin idanun nashi suka kasance a lullube a koda yaushe.

Ya saukar da kallonshi akan karamar diyarshi Ihsan, yarinya yar kimanin shekaru bakwai a duniya. Zaune take tayi zaman dirshan akan tattasaun kafet dake zagaye da tsakiyar falon ruwan kasa da ratsin ruwan madara. Ta baza kayan wasa tun daga lego, zuwa jirage da motoci da dolls, tana wasanninta.

Dukawa yayi a gabanta yana dauke balallaiyar baby doll da tayi wancakali da ita, yace "babyna ya aka yi ne?".
Ta daga kai ta kalleshi, yatsarta manuniya data tsakiyar lume a cikin bakinta. Tace, "Daddy yau ma fita zaka yi?".
Yayi dan murmushi, "ehh baby, amma yanzun bada jimawa ba zan dawo!".
Kafa ta hau bugawa a kasa cike da shagwaba zata fara kuka, tace "ni dai yau sai ka tafi dani. Haka jiya ma kace mana mu jiraka ni da Yaya Raihan amma baka dawo ba!".

Tattagota yayi cikin jikinshi yana lallashinta cike da siga ta nuna kauna da tattali, amma fir ta nuna bata ma saurarenshi. Suna cikin wannan hali sai ga yayan nata Raihan ya shigo falon shima, hannu tallabe da kwallo daga ganin yanayin dattin da kafafu da kayanshi suka yi kasan daga wasa yake.
Mukhtar bai samu damar yiwa dan nashi mai kimanin shekaru tara fadan fita waje ba kamar yadda ya saba, saboda fatali da Raihan da yayi da kwallon, shima ya tafi ya kama hannun daddynshi. Nan da nan suka rikita shi.

Hannu ya kai ya shafa saman hancinshi in exasperation, kafin wata dabara tazo mishi. Ya kallesu yana murmushi, yace "to naji, zamu tafi tare daku. Amma kuje wajen Anty Safinah ta canza muku kaya tukun".  Aikuwa suka yi tsallen murna, suka tashi da gudunsu suka bi wata hanya inda zata sadasu da bangaren da masu aikin gidan suke
Dariya yayi a hankali take da kawar da kayan wasan Ihsan daga kan hanya kada wani ya taka ya mata barna, yasan ballin a kanshi zai kare.

Akan center table ya sanya hannu cikin wata karamar bowl da aka sak'a da zaren kaba, nan suke ajiye makullan motocinsu da bikes. Har ya dauki makullin wani bakin Yamaha, sai ya mayar ya dauko na sabuwar motarshi CZ34.

Hajiya Ni'imah, wadda aka fi sani da Mamy, tana kicin suna faman aikin gashin meat pie da samosa ita da Dije mai tayata aiki, duk cikin aikin tarar maigidanta Alhaji Bamanga Tijjani dake tafe daga birnin Lagos wajen kaninta, wata tattaunawa da suka yi game da wata gamayyar hadin giwar bude wani kamfanin siminti. Tana jiyo takaddamar da aka sha tsananin uba da 'ya'yan nashi, tana murmushi abinta.

Ya shiga kicin din, meat pie daya ya dauka ya kai baki yana ci cikin gyada kai, ya yarda Mamy daban ce in dai ta fannin girki ne.
Ta kalleshi tana girgiza kai, tace "kasan dai rigima kawai zaka hadani da ita idan yarannan suka gane dabara ka musu ko?".
Yace "ai shiyasa dama zan barsu tare dake, saboda ke kadai kika san yadda zaki yi taming wadannan little devils din".

Mamy tayi yar dariya, tace "Allah Ya shiryeka Mukhtar!! Y'ay'a biyu amma har yanzu ban ga ka fara alamun kimtsuwa ba. Ina zaka je ne haka kaci kwalliya?".
Ya girgiza kai, "ban sani ba wallahi. Haka kawai nake jin kamar ana mintsinina, fita kawai nake so inyi!".
Tace "to ka dai daure ka dawo da wuri. Tunda ka dawo daga Benin ka ki zama waje daya yarannan kuma suna bukatar su ganka a kusa dasu suma. Suna bukatarka".
Yasan gaskiya ta fada, ya gyada kai, "in shaa Allah Mamy. Gobe zamu je gidan zoo da amusement park dasu. Zan dai biya bashin da ake bina!".
Dariya ta sake saki, tace "hakan ya dai fi. Sai ka kama hanya kafin su dawo su hanaka fitar kuma".

WANI GIDA...!Where stories live. Discover now