Babi na Goma Sha Takwas

3.4K 334 52
                                    

☆18_Mahaifiya!☆


Fiye da awanni biyu ana ta faman aune-aune da gwaje-gwaje. Daga wannan dakin a kaita wancan, Mamy ta damu matuka. Gata ita kadai a wajen. Sai can gab da magriba sannan Alhaji Bamanga da Mukhtar suka karasa asibitin. Ta kama hannun mijinta daya zaunar da ita a gefe yana lallashinta tare da tausar mata da zuciya. Mukhtar ne yaje reception yana tambayar yadda ake ciki, aka ce mishi ya saurara. Don haka ya koma wajen su Mamy suka cigaba da zaman jiran tsammani.

Ba'a jima ba aka maidata dakinta na da, yayinda Likita ya nemi ganinsu. Babu bata lokaci suka nabba'a a gabanshi.
Ya shafa kanshi cike da nuna alamun daurewar kai da gajiya, yace "magana ta gaskiya ita ce duk wasu gwaji da zamu yiwa kwalwarta da kanta domin mu ga wata cuta da take da ita ko wani abu, munyi, amma sakamakon duk lafiya lau yake nunawa!".

Mamy tace, "me hakan yake nufi?".
Ya girgiza kai, "ban sani ba. Amma zamu yi monitoring dinta, mu kuma sake yin wani gwajin don ganin abinda muka yi missing. Idan hakan ya cigaba da faruwa then I'm afraid, aikin ba na asibiti bane gaskiya. Yanzu dai munyi mata allurar barci wadda zata iya kaiwa gobe tana barci, don haka zaku iya shiga ku ganta".
Jiki a sanyaye suka mishi godiya suka wuce wajenta.
Tsaye suka yi su duka a gefen gadon nata suna kallon yadda take ajiye numfashi daya bayan daya. Hannunta inda taji ciwo an sanya plaster an danne. Tausayin baiwar Allahn ya cika musu zukata. Me ya sameta ne haka ita kam??!.

Da lokacin sallar magriba yayi Alhaji da Mukhtar suka fita yin sallah, ita kuma Mamy tayi tata a daki. Tana nan zaune tana lazumi har Safeenah ta karasa asibitin.
Bayan sunyi sallah, su Mukhtar suka koma. Nan suka yi sallama da Safeenah suka tafi gida.

*

"Tunda har yanzu babu wani labari, me zai hana ka komawa bakin aikinka? Gwara mu fawwalawa Allah dukkanin lamuranmu Abbas. Zamanka anan bashi da wata fa'ida ko nasaba".
Mama take fadawa Abbas a ranar litinin da yamma, bayan ya dawo daga yawon nashi daya zame mishi ka'ida a kullum.
Al-Ameen ya wuce makaranta tun a jiya, Iman ce dai take kan hanya a cikin satin, idan ta samu yadda take so.

Yace, "da hutu naso dauka?", ya karasa fadar cikin alamun tambaya, kamar shima bai san menene dai-dai a gareshi ba.
Mama ta jima tana kallonshi, kafin tace cikin tausasawa, "saboda me Abbas? Kana tunani zamanka anan zai sa ko ya hana abinda Allah Ya riga ya kaddara zai faru? Ko kuwa kana tunanin zai dawo da Hajjo daga inda ta tafi ne?".

Yayi shiru kanshi a kasa, bai ce komi ba. Saudah tace mishi ita bata gaji da ganinshi ba har yanzu har ta shawarceshi da daukar hutu koda na sati biyu ne. Kamar kuma yadda Mama tace, sai yake gani kamar idan ya zauna a gidan Hajjo zata iya dawowa a kowane lokaci. Shi fa har lokacin bai cire tsammani da dawowarta gida ba. Gani yake yi a kowace safiya zata iya zuwa ta kwankwasa musu kofar gida. Baya so yayi missing wannan lokaci mai muhimmanci sam!.

Mama taci gaba da cewa, "a ganina da ka bar wajen aikinka ka zauna kana ta walagigi daga wannan titi zuwa wancan, ka koma wajen aikinka mana. Ko babu komi kaga acan zaka dinga yin ayyuka da sauransu nan fa?".

Ya gyada kai a hankali, shi yasa dama aka ce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni ba zai iya hangoshi ba. Duk da cewa a wajen Saudah yake yini, literally, amma kadaici bai taba barinshi ba dai-dai da kwarar zarra. Kila komawarshi wajen aiki can do good to him. Ya yaye mishi kewa da kadaici dama duk wasu kananun damuwoyi da suka mamaye mishi zuciya.

Yace, "haka ne Mama. In Allah Ya yarda zan koma bakin aikina. Zuwa ranar laraba sai in koma, tunda dama ba'a riga anyi approving hutun nawa ba har yanzu".

Mama tayi dan murmushi cike da jindadi da farinciki, tana alfahari da yadda Abbas yake matukar girmamata da duk wata shawara tata a gareshi.
Tace "yayi kyau. Allah Yayi maka albarka, Allah Ya baka duk abinda kake so, Ya kare min kai daga sharrin duk wani abin ki da makiya!".
Yayi dan murmushi cike da jindadin addu'arta a gareshi, yace "ameen Mama... Bari in leka wajen Mus'ab abokina. Zamu je nan Dan-Nakola dashi".

WANI GIDA...!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt