☆12_Sanyin Idaniyarta!☆
Acan cikin kuryar dakinta, Anty Ummah ce ke ta kaiwa da kawowa, hannuwa rungume a kirji tana jijjiga cikin zurfin tunani.
Saudah ta banko labulen dakin ta shiga da sauri tana mai kwala mata kira, "Mama! Mama!!".
Ta tareta a tsakiyar dakin, "lafiya? Ya aka yi ne?".Tace "Mama wallahi har yanzu Baba yana zuwa gidansu shegiyar yarinyar can! Yanzu ma na ganshi ya shiga gidan, da ledar gasasshiyar kaza da lemu a hannunshi, kuma wallahi ya jima da shiga gidan. Sai gajiya fa nayi da jiranshi na taho!".
Anty Umma ta kama haba tana jujjuya kai, tace "wai wannan Halima din wace irin masifaffiyar nanatacciyar mata ce? Ta bar cikin gidan ma ba zata taba kyaleni in sarara ba? To wallahi da sake! Da alama aikin Malam mai Kogi ya fara sanyi, matsiyaci!, dama tunda ya bukaci kudi na hana shi nasan cewa sai ya nemi ya bata min aiki. To yayi kadan wallahi!! Ni nan nafi karfin kowane dan iska!!".
Tayi shiru tana ajiyar numfashi kamar wata macijiya, Saudah kuwa binta take yi da kallo cike da adoration, ba karamin burgeta uwar take yi ba. Saboda bata taba bari wata matsala ko wani mutum ya takata, ta ko wani hali sai tayi maganinshi. Wanda a ganin Saudah a lokacin, ko kuma ta abinda aka koya mata ta gani, wannan shine ultimate rayuwa mai dadi da kuma burgewa.
Ta kalli diyar tata, tace, "ki shirya, gobe zamu je nan kasa wajen wani sabon malami, ance aikinshi kamar yankan wuka. Lallai zanyi maganin wannan matsala da take shirin kunno min kai a take, ba tare da bata lokaci ba!".
Saudah tayi tsalle tana tafa hannu, "wallahi Mama shi yasa nake matukar son ki! Sam ba ki yin sanya!".
Tace, "ina zan zauna ina kallon ruwa har kwado yayi min kafa? Mijina tun kafin ya dawo gida in ganshi ya wuce can gidan wasu yan iska, ai babu ni babu zama sai naga na raba su kamar yadda gabas ta rabu da yamma!".
Saudah taci gaba da kodata tana kara fasa mata kai.*
Washegari a can cikin kauyen Yarima Jatau dake Mai'adua, can cikin daji inda bukkar da malamin yake kadai kake iya gani, sai kuma shukoki da daji daya zagayesu. Mashin din daya daukesu can ya ajiyesu saboda rairayi yayi yawa. Haka nan suka daba a kafarsu, tafiyar kusan mintuna arba'in a cikin rairayi, amma basu saraya ba.
Baba yana fita itama ta sabi gyale ta fita akan cewa Saudah data kwana da zazzabi zata kai asibiti saboda kada ma yayi fadan kin zuwanta makaranta.
Suka je suka tarar da uban layi kamar wasu masu ganin annabi. Haka suka zauna suka bi layin nan suma. Sai wajen azzahar sannan aka musu iso zuwa wajen Malamin.Zaune a gabanshi ita da Saudah, bayan sun gama bashi labari akan abinda yake tafe dasu. Malamin ya baza wasu irin duwatsu a cikin rairayi a kasa yana wasa dasu a ciki. Sun dauki kusan mintuna biyar, bai ce komi ba sai kai da yake gyadawa kawai.
Can ya dago yana kallonsu da wasu razanannun idanuwa da suka sha kwalli bakikkirin!.Yace "hakika abinda kuka zo dashi ba karamin aiki bane, ina so ku san cewa gabadaya bukatunku ayyuka ne ja, masu matukar ban wahala. Lallai sai kun dage, kun kuma kara zage damtse. Domin kuwa a halin da ake ciki yanzu, duk wasu ayyuka da kika yi akan matar wannan sun fara warwarewa, kiris ya rage komi ya lalace!".
Anty Umma ta zabura ta dafe kirji tana salati.Ya fara nuna mata duwatsun dake cikin rairayi yana mata bayani, yace, "kinga wannan...?", wani dutse ne dake can karshen rairayin, kiris ya hana ya sauka kasa, sai wani a can tsakiya, shi kuma yana daf da wani babban dutse wanda ya banbanta da sauran.
Ya nuna mata babban dutsen yana cewa, "...mijinki ne, wannan kuma..," ya nuna na tsakiyar, "matar ce. Sai wancan...", ya nuna mata na karshen wanda ya kusa fita daga cikin sauran, yace, "ke ce. Kin kusa fita daga cikin rayuwarsu gabadaya idan baki yi da gaske ba".Zuciyarta ta hau dakan uku-uku, tana zare idanu. An riga an gaya mata ayyukan mutumin kamar yankan wuka haka suke, idan ya fadi magana to fa babu haufi, sai ta faru.
Tace, "to yanzu Malam me kake gani yakamata inyi?".
Ya daga mata hannu, idanu a rufe yana kara baza duwatsun daya hargitsa. Don haka ta kama bakinta ta tsuke.
KAMU SEDANG MEMBACA
WANI GIDA...!
RomansaTana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika. Ta...