Babi na Biyu

6.6K 534 29
                                    

02_Da...!

'I don't wanna live., forever...
Coz I know I'll be calling your name...,
And I don't wanna fit, wherever....
I just wanna keep calling your name....,
Until you come back home!'
          Zayn Malik ft Taylor Swift_I Don't Wanna Leave

Garin Daura wata Karamar Hukuma ce a cikin garin Katsina.
Mahaifinta, Alhaji Mamman dan kasuwa ne, ba laifi yana da rufin asirin shi daidai gwargwado. Gabadayansu daga wadanda suka gama karatu har wadanda suke kan yi, duk manyan makarantu na kuɗi suka yi.

Ita da sauran yan'uwanta sun rayu ne tare da matan Babanta su biyu, kasancewar sun rabu tun tana yar yarinyarta. Su uku kadai mahaifiyarsu ta haifa kafin su rabu da Babansu. Ita, sai babbar yayarsu Iman, (Zainab da ta kasance mai sunan mahaifiyar Baban), sai kaninta Imran. Amma mahaifinsu yana da wasu yayan daga wajen sauran matan shi. Saudat ita take bi mata, yanzu shekarunta goma sha biyar, tana aji uku a karamar sakandire, ita ce diyar Anty Ummah ta farko, sai yan biyu, Hassana da Husaina shekarun su goma, Amina da Khausar su duka yayan Anty Ummah ne. Anty Yaha tana da yaya hudu, Aliyu, Maimuna, Sa'adiya sai Assadeeq auta dan kimanin shekaru biyu.

Iman tana jami'ar Tafawa 'Balewa a Bauchi tana karantar Mechanical Engineering, itace babba a gidansu, yanzu tana cikin shekarunta na ashirin da hudu, tana aji uku. Imran yana makarantar gaba da firamare a garin Dutsin-Ma yanzu yana ajin shi na biyar, shekarun shi sha bakwai. Ita kuwa wannan shekarar ta shiga ajin farko a jami'ah bayan ta gama makarantar yanmata ta gaba da firamare a Kazaure. Shekarunta sha tara.

Rayuwar gidansu, rayuwa ce gata nan kadaran-kadahan, babu yabo kuma babu fallasa. Mahaifinsu ya tsaye musu tsayin daka akan karatunsu, sai dai fa na boko. Bata iya tuna lokacin daya biya musu kudin wata na Islamiya, wanda ta dalilin haka ne aka koro su daga makarantar. Mama ce ta tsaya tsayin daka sai data mayar dasu makarantar, kuma taci gaba da biya musu kuɗin makarantar. Sauran yaran kuwa iyayen su suka zuba musu na mujiya, shi yasa duk suka taso babu addini kuma babu tarbiya, saboda iyayensu basu tsaye musu sun koya ba, basu kuma koyar dasu ba, sannan basu dora su akan turba ta kwarai ba.

Yawancin lokuta idan Baba ya fita wajen harkokin shi baya dawowa sai dare, bai san wani hali gidan shi yake ciki ba. Ko da ya dawo daga kasuwancin shi baya wani tambayar abinda ya faru. Duk abinda matan shi suka zauna suka kulla mishi, shine magana kawai a wajen shi.

Wahalar da suka sha a gidan wajen matan Baba Allah kadai yasan irinta, musamman Anty Ummah. Sun sha wuya ta kin karawa a wajenta. Duka, zagi, sharri, kalen sata, babu wanda basu gani ba a hannunta har zuwa yau dake motsi kuwa. Tun Baban yana yarda da karerayin ta idan ta kulla, watarana ma ya same su ya musu duka na kin karawa, har yazo ya daina.

Dalili kenan da yasa tana gama JSS dinta ta takura aka kaita FGGC ta Kazaure, shima da kyar da jibin goshi Baba ya yarda bayan kanin Babansu, Baba Ibrahim ya sanya baki. Bayan nan ne shima Imran ya tafi makarantar kwana.

Mahaifiyarsu buzuwar cikin garin Damagaram ce, shi yasa gabadayansu zaka gansu farare tas dasu. Musamman Iman. Imran kuma ya dauko bakin mahaifinsu ne, idan ka ganshi kamar wani bakin balarabe.
Suna da dogon bakin gashi sidik, dogon hanci da dara-daran idanu farare tas da digon baki kamar an disa tawwada, duk da cewa nata idanun suna da sirkin brownish-ash, wanda ya zagaye bakin (double iris). Kirar jiki kam ta kowane fanni sai dai su godewa Allah, kirar nan ce da hausawa kan kira ta 'kalangu' ko ince 'kwalbar Coca-Cola'.
Mahaifiyarta su uku ne a wajen mahaifiyar su, babbar yayar su Saddiqa, Allah yayi mata rasuwa ta bar danta daya, Abbas. Sai mamarsu, Halima, sai kuma  Anty Zubaida wadda take aure a garin Kaduna.

WANI GIDA...!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora