DUNIYA BIYU!!!

1.6K 140 33
                                    

Gefen wasu samari uku da suke ta faman tada hayaki kamar tashin duniya ta rakube, ta mikawa Bangis -mai shagon- kudin hannunta.
Tace, "magi mai tauraro zaka bani na talatin da aji-no-moto na ashirin".
Ya zuba mata a leda fara ya mika mata. Ta juya, wani daga cikin matasan ya fesar da hayakin daya busa, ya sauka akan fuskarta. Ta sanya hannu tana kore hayakin, tana tarin daya sarketa sakamakon shakar tabar da tayi har cikin makoshinta.

Ta bude idanunta dake mata zafi, babu mamaki ma sunyi ja, ta saukesu akan wanda ya aikata mata wannan ta'addanci.
Babu abinda ya dauki hankalinta a tattare dashi sai idanunshi, irin idanun dake nuna wuya da tsananin duhun rayuwa da suka gani, suka kuma jure. Duk rashin kunyar mutum, karya yake yace zai tsaga tsakiyar idanun mutumin nan yace zai mishi rashin kunya. Don haka ne yasa ta kame bakinta, 'yar Allah Ya isa din data dauko daga cikinta zata yi, ta tsaya a makoshinta. Ta sadda kai ta kara rabawa ta gefensu ta wuce.

Bata sani ba, wani abu game da wannan bakon mutumi da bata taba gani ba, seems nagging. Ta kasa fitar dashi daga cikin ranta. Dai-dai zata karya kwana, ta juya tana kara kallon tiredar.
Yanzu ya fito daga cikin tiredar, yana tsaye daga waje. Sai dai kaifafan idanuwan nan nashi suna kanta kyam. Wata irin kunya da faduwar gaba suka rufeta, musamman dan guntun murmushin da taga yana yi mata. Tayi saurin yin kasa da kanta, wani dan karamin murmushi itama yana ziyartar bakinta, kafin ta juya da sauri ta karya kwanar.

Labarin DUNIYA BIYU zai fara zo muku a ranar laraba 5/8/2020 akan naira dari uku kacal! Ba wai yabon kai ba, wannan ya bambanta daga sauran littafan da nayi a baya. Wane Ni da abokin babana! Wane Doctor Sheerah da a zatona da sauransu??
Wannan tafiya da zamu yi zuwa cikin duniyar da bamu taba shiga ba, cike yake da adventures masu van mamaki da daukar hankali, al'ajabi, soyayya da kauna masu tsayawa a zuci. Ba dai zan ce muku komi ba, sai kun shigo daga ciki kawai. Da kanku zaku bani labari.

Domin neman karin bayani akan yadda zaku samu wannan labari, ku duba profile dina inda ake cikin sakin somin-tabin labarin. Kada ku bari a baku labari!!!

WANI GIDA...!Where stories live. Discover now