Babi na Ashirin Da Tara

3.5K 377 70
                                    

☆29_Biki, Bidiri, Bired'e!!!☆




Mamy ta hadasu da wata kawarta da take zaune a garin Abuja. Suna hada events na biki kala-kala a sassa da kuma fadin Najeriya. Bayan kwana hudu da sanya ranar bikin, suka tsaya a Abuja din inda suka kwana biyu suna ta shirye-shiryen abubuwan da zasu yi, ana kuma aunasu da gwada musu duk kayan da zasu yi amfani dasu, hatta da underwears da zasu yi amfani dashi sai da aka ware musu. Su Muhajjatu yan rawar kai, yawanci komi nata ita ta zauna tayi designing dinshi. Biki take shiryawa ita da Mamanta na garari wanda zai yi tambari a fadin Najeriya. Sai tayi rashin sa'a su sauran amaren basu da wannan tsari da ra'ayin. Biki suke so suyi simple, mai sauki da kuma rashin hayaniya.
Nan fa ra'ayi ya bambanta, abin kamar zai kawo rigima ma. Da kyar dai suka yi maslaha, events din biki suka koma hudu a maimakon takwas da Muhajjatu ta so ayi.
Bayan sun gama rounding up din komi, Muhajjatu ta juya Lagos domin zuwa taci gaba da shirye-shiryen abubuwan da zasu yi acan, su kuma suka koma Kano wajen Mamy.

Da yake a mota zasu tafi, bayan sunyi sallama da Hajiya Lailah sun kuma dauki hanya, ta nemi direba daya tsaya a supermarket ta dubawa su Ihsan sweets din tsaraba. Ita da Al-Ameen da Iman duk suka shige shagon, suna shiga kowa ya nufi bangaren da yake son yin sayayya. Ita kam kai tsaye wajen su chocolates da snacks ta nufa, ta daukar musu irin wadanda suke ci da kuma wanda suma zasu ci a hanya.
Bayan nan sai ta tsaya a aisle din kayan kwalliya. Ta tsinci turaruka da roll ons. Wani dankunne da sarka da suka ja hankalinta, ta dauki har kala kusan hudu zata ba kannen Abbas mata. Zasu dauki kusan sati daya a Kano kafin su wuce Daura, don haka bata tsaya yiwa yan Daura din tsaraba ba.
A wajen biya suka hade su duka, bayan sun biya kudin aka zuba musu kayan a cikin leda, kowa ya dauki nashi suka fita daga shagon.

Kamar da wasa sai suka yi kicibus da Baba Yar Dudu a bakin titi. Suka kama baki a tare cike da tu'ajjibi da mamaki, Yar Dudu tace, "ikon Allah! Yar nan kece kuwa?".
Bahijja ta rungumeta tana dariya, tace, "nice mana Baba! Dama rai kan ga rai?".
Suka matsa gefe suna kara gaisawa sosai saboda ababen hawa. Yar Dudu tace, "kwanaki naji ance baki koma gida ba barinki nan, wai kin bata. Kin dawo lafiya dai ko?".
Ta gyada kai tana murmushi, "wallahi kuwa, kin san mutum da kaddararsa. Ina su Momcy da Safeenah kuwa?".

Yar Dudu ta kama baki, "ke rabani! Ai bayan tafiyarki abubuwa suka kara rincabewa Zayyan yayi halin a cikin gidan, rashin adalcin yayi yawa na kasa dauka. Ni kuwa na bar aikin. Amma ina jin labarinsu a cikin unguwa. Yanzu yaron ai yana gidan yari, kamar daurin shekaru sha nawa naji ance an mishi? Wata yarinya karama ya yiwa fyade a makaranta, sai yayi rashin sa'a diyar hedimasta din makarantar ce. Shari'a har gaban alkali in gaya miki!".
Bahijja ta kama baki, "Baba da gaske?".
Ta gyada kai, "ina gaya miki fa! Uban ma ai yayi ritaya in gaya miki, jirginshi aka harbo da rikon kama-karya da yake wa mukaminshi. To da korarshi zasu yi ma, sai aka tausaya mishi yayi ritaya".

Ta girgiza kai cikin jimami, a ranta koda wasa bata tausayawa Zayyan ba saboda tasan ya cancanci fiye da haka. Allah kadai yasan iyaka adadin mutanen daya batawa rayuwa iyayenshi suka dinga rufewa.
Tace, "to yanzu Baba a ina kike aiki ne?".
Tace, "ai yar nan yan share-sharen bakin titi ne muka samu muke tattabawa haka nan, kinsan abin tsufa ya fara kawo min, ba duka gidan aiki suke daukarmu ba".

Bahijja tace, "ai dama yakamata ki zauna haka nan ki huta kuma. Lokaci ya ja".
Ta bude jakarta, duk wani kudi dake ciki sai data lalube ta mika mata, tace, "ga wannan, ki samu ki zauna a gida kawai kina yin sana'arki zai fi Baba!".
Yar Dudu ta tafi zata zube kasa tana mata godiya, Bahijja tayi saurin tarota, "haba Baba! Meye haka kike yi? Ki bari don Allah!!".
Tace, "kai wannan diya, yadda kika ji kaina, Ubangiji Allah Ya ji kanki. Allah Yayi albarka Ya jikan iyaye". Bahijja tayi murmushi, "ameen Baba!".
Sai data bata lambar wayarta sannan suka rabu da alkawarin zasu dinga waya suna gaisawa.
Ta shiga mota inda su Iman suke jiranta, suka dauki hanya suka tafi.

WANI GIDA...!Where stories live. Discover now