MR BELLO..!

4.5K 124 8
                                    

*MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*NA*

*JANAFTY*💕
*Wattpad:Janafnancy13*

_*Bismillahir Rahamanir Rahim in the Name of ALLAH the most  Beneficient the most mercerfull praise be to Allah lord of the words.....*_

_Assalamu Alaikum my Follow fans,am starting my new Book i ask ALLAH subhanahu wata"ala to guide me throught and make me it sussufull till End Ameen ya Allah_

*Copycats are not allowed to transform this book by any means without the prior written permission of the writer.Immediate action will be taken if caught❌*

_⭐DEDICATED TO:  *Bashir Sufyan Sardauna* and *Nazifi yarima*..❤️ Tanque Dudes For ur All Support and Concern,...Sakallahu Fil jannah Allah ya bar zumunci Ameen_

_SHIMFIDA_.....

        *🅿️1*

*GGUSS KWATAR-KWASHI*

A haraban Babbar Makarantar ta GGUSS,Goverment Girls Unity Secondry School Kwatar-kwashi Dake Tsakanin Dajin kwatar-kwashi Zuwa Gusai,Da Misalin karfe 10:30am na Safe.

Daga Cikin Babban Filin Haraban Makarantan Na Hangi Dabilai Birjit ba Adadi mata ne Zallah Ta Ko"ina Suna Yawo Wasu Suna Tsaye da Tarin Akwatunsu da Jakunkunansu Wasu kuma Suna ta Tururuwan Shiga Doguwar Mota Fara mai Dauke da Tambarin GGUSS KWATAR-KWASHI, gefe daya kuma Kowaccensu Tana Sanye da Uniform ne Ajikinta wasu Nasu Wando light green ne Both Riga da Wando da Dan kwali sai Farin Hijabi Ayayinda Wasu kuma ke Sanye da Dark green din Wando sai Both Farin Riga da Da'n kwali da Hijabi.

Ayadda Haraban Makarantan ta Rikice da Hayaniya da Murna da Iface ifecen Dalibai zaka Fahimci Hutu ne Daliban Suka Samu Tun ma Ba Daga yadda Wasu Iyayen Daliban keta Zuwa Daukan yaransu Wanda basu yi Rigister da Motar Makaranta ba, Ayayinda Wasu ke Ta Fitowa Bakin Get din Mkranta ga masu Mashi nan suna ta Daukansu Zuwa inda zasu Hau Mota Zuwa Gida.

Dagachan bangaren Na Hangi Wasu Yanmata su Uku Tsaye Abakin Wata Bishiyar Dalbejiya Dukkansu Gabansu Akwai Tarin jakunkuna,da Sauran Tarkacensu masu yawa, sakamakon Wannan Hutun Third term ne karshen Zagon karatunsu na Jss 3 sai Shiga SS1 Kenan,Suna Sanye da Uniform dinsu na Junior,light green both Riga da Wando da Dankwali sai Hijabi Fari,Dukkansu Ukun Tsawonsu Daya Sai dai kuma Biyu Daga Ciki Farare ne Tas,Sai Ta Ukun Wacce ke Tsakiyansu Baka ce Sulub ammh Bak'inta bamai Duhu bane mai haske ne, Wanda Ke Shining,Doguwa ce Mai Karancin Girman Jiki,Fuskarta tana da Fadi Ammh ba Sosai ba,Tana da Manyan Idanuwa Masu Dauke da Gashin Ido Zarara sai Karamin bakinta Wanda Yake Baki baki,Ashekaru Dukkansu bazasu gaza Shekaru goma Sha Shidda ba Daga Kallon Farko Zaka Fahimci Zallar Kuruciyarsu Alokacin.

Daga bayansu sukaji Ance " *ANEESA...* atare Suka Waiga dukkansu suna Kallon Daya Daga Cikin Senoirs dinsu Jidda Madaki Wadanda Suke Kan Zana Jarabawarsu ta Fita Ma'ana WAEC,Saboda Haka Su Suna Makaranta basu Azuwa Hutu sai Sun kammallah Neco wanda kuma bazai yi ba Sai ya Tattara ya koma gida.

Itama din Sanye Take da Uniform dinsu na Senior,Dark green da Farar riga da Hijabi,Kyakyawan Gaske ce Gata Fara gata Doguwa mai Dauke Da Daran Daran Idanuwa masu Haske Cikin Siririyar Muryanta tace"Aneesa Plz D'an zo na ganki...'Tafada Cikin Yanga Wanda ya Zame mata Halitta.

Jin Abunda tace yasa Aneesa Ta kara Hade Ran Kamar Wacce Aka Aikoma da Sakon Mutuwa Sabanin Sauran kawayenta da Fuskarsu ke Washe na Farincikin Zasu koma gida yau,Cikin Sanyi Jiki da Takun Bacin Rai Aneesa Ta Nufi Jidda tana Fadin" *S. JIBIYA,B.KAITA* Kujirani bari na Dawo.."Jin Haka yasa S.jibiya tace"Ok *A.BUKAR BULAMA*..."Tafada Tana bin Aneesan Da Kallo kafin Ta Maida Kallonta kan B.kaita Suka hada ido Suna Kunshe Dariya.

Aneesa kamar bazata Taka kasa ba Haka ta Rinka jan kafa Zuwa Wajen Jidda Dake Tsaye tana Jiranta Tana karisowa ta Riko Duka Hannayeta Cikin Salon Muryanta tace"Aneesa Don Allah karki manta da Alkawarinmu Kinji.."Tafada Tana Sakarmata Fararen Idanuwanta.

MR BELLOWhere stories live. Discover now