MR BELLO..!

1.4K 50 3
                                    

*MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
         
             *🅿️5*

"""Mutuwan Data Girgiza Zukata Gabadaya,Daga Muhammed Har Hassatu da Direbansu Allah yayi Musu Rasuwa nan Take kuma da Abun yafaru kabiru Aka Kira Aka Fara Sanarmawa..

Sun Nuna Alhininsu da Kuke kukensu na Rasuwar Muhammed Haka Mutanan Yola Suka Samu Lbri  tun kamar kar Daada Taji lbri Sai Jikinta yakara Rikicewa Shi Kuwa Muktar Daga Kaduna Aka Daukosa Zuwa gida Harda Bello Wadanda Suka zo Suka Iska Mugun Lbrin Rasuwar iyayensu Sunyi kuka kamar Ransu Zai Fita Domin Sun Shaku da iyayensu Sosai Koda Dangin Hassatu Suka Nemi Sanin Komai game da Dukiyar Muhammed Sai Su Muhammed Suka hada baki da Ma"aikatan Kamfononin Tare da Accountans Din kamfafonin Muhammed marasa Tsoron Allah Domin alkarukan Makudan kudi su Abba kabiru suka yi musu alkawari matukar suka goya musu baya

Su suka taimaka wajen Hada Jawabin Karya Wajen Cewa Kamfoninsu Biyu Sun Ci Bashin Wani Kamfani Domin Farfado Dasu To yanzu Kudi Sun karu kan Kamfanonin kuma Babu Riba ya Tabbata Kamfanin Daya Hada Hannun Jari Dasu zasu karbi Wadanan Kamfanonin Guda Biyu Domin Biyan Kudin Da Sukayi Asara Hakan bai Isheshi su ba,Haka Suka Dinga Kawo bayanan karya da Mahintan Ma"aikata Harda karya n Bashin Banki na Wajen Miliyan Talatin da Biyar Dangin Hassatu Suna ji Suna gani bayani ya Tafi kan Duka Dukiyan Muhammed Wai batashi Bane Sakamakon yana Da Hannayen Jari masu yawa kuma basu kawo Riba ba Illah Binsa Bashi Da Sukeyi.

   Muktar na gani Ammh bashi da Ikon Mgana Bello ne mai Zuciyan Shi Kuma yana Karami ne Lokacin Sunaji Suna gani Abba Kabiru da Abba Garba Suka Hamdame Dukiyarsu Daga Karshe sai Duka Kamfanonin mahaifinsu ya Dawo Tsakaninsu Shida Abba garba da Sunan bayan Anyi Gwanjonsu Suka Siya Duniya ta Dawo Musu Sabuwa Hajiya Sahura da Hajiya Karima ba Wacce bataje Makka da Ummura ba Suna ta Facaka da Kudin marayu su da ya"yansu basu taba Tunanin cewa Cin hakkin da ba naka ba wani Nauyi ne wanda ko bayan ranka sai ya tambayeka ba.

Muktar da Bello ko ba Wanda ya kara bi Takansu Domin Dangin Hassatu Na yola bayan anyi bakwai Suka Koma,sunyi kokarin abasu yaran Hassatu su tafidasu wajen Daada ammh Abba kabiru yace ba wannan mganar yara suna karatu bazasu  lamunci katse musu karatu ba,suka rabu akan su zasu rike yaran suna ta kukan karya Dana munafunci nan ko mugun Nufi ne da Tsabar mugunta ke cin ransu kamar Abba kabiru yaji labari yafi Abba garba Dora buri Bisa Dukiyar da bako zufanshi wajen Tarata.

Daada bata zo ba  tana chan Babu Lafiya,Su da gidan ubansu Ammh Sun Rasa Dukkan gata ba Wanda yayi Tunanin maidasu Makranta Shi Bello Bai koma Negrian Turkish Academy ba Shi kuma Muktar ba"a Maidashi NDA ba Ammh Hashim Tuni Abba Kabiru ya Turasa Kasar Spain yana Cigaba da Karatunsa.

Wahala Rayuwa da Matsi ba Wanda Basu gani ba,Acikin Gidan da Ubansu ya Gida da guminsa ba,Abinci ko Sai dai indan Sun Rage,suna Rabe raben kankaran kanzo ko ma"aikatan gidan sunfi suvgalihu da Daraja watarana ma sai wanda ma"aikatan suka rage ne suke samu wani lokacin sai dai muktar yaci girma ya barma Bello,saboda tsausayin kanin nashi Wani lokaci haka zasu zauna suyita kuka Bello yana ganin dashi ne keda girma da Shekarun ya muktar wlh da su Abba garba sungane basu da wayau sai dai kash shi Muktar yana Da sanyin Hali irin na mahaifinsa sam komai za"a musu acikin gidan baya Daga kai Bello ne Wani lokacin ke Tubure musu,Tuni suka gano yaron zai iya basu matsala wata rana suka Fara Tunanin yadda zasu maganinsa.

Abba Kabiru ma saboda Samun waje Shashen Mahaifinsu ya koma Shida Iyalanshi Kasim dasu Zubaida Ana Ta Cin Duniya Da Tsinke Cikin Kwanciyar Hankali Muktar da Bello Aboy Quaters Suka Koma Kwana Hatta da Masu bama Fulawa Ruwa Asallamesu Da masu Wankin Motoci domin kaf motocin mahaifinsu Data Mahaifiyar suvdata muktar din Duka ko Abunda ba"a so basu barsu dashi ba.

Bello da Muktar su suka koma wanke motoci da bama fulawowi ruwa wani Lokaci Bello ke nuna Taurin kai Sai yaki yi Haka  Abba Kabiru zai Ta Marinshi Ammah yakiyi,Yana da Saurin Saka Abu Acikin Ranshi Shiyasa komai yakasa Bacemai Hajiya Sahura ko da Hajiya Karima ba irin Wahalan da Basu ba su ba Kamar basu Taba Saninsu ba,Sunsha lakaba ma ya muktar sata,Mussmman Bello da ya cika bakar Zuciya yafi muktar shan wuya agidan Hatta da su Zubaida dake yara Suma Sun Iya Wulakanci Musamman ga Muktar Wanda baya da Fada da Hayani Wani Lokacin bello ke kwatanshi Shiyasa Duk yafishi shan Wahalansu, Cikin Shekaru uku Suka Chanza Kamanni Rayuwarsu Duk ta lalace Kamar basu bane ya"yan Hutu ba Tuni Hashim ya Dawo ya Zama Saurayi dayake yana da girman jiki Har yafara Aiki da Kamfanin da Abba Kabiru ya Hamdamai Wai Muktar ne ke Budemai get in zai  zai Fita Yau ya Hau Wannan Mota gobe ya Hau Wannan yana Cin Duniyarsa da Tsinke

MR BELLOWhere stories live. Discover now