Page2️⃣

108 3 0
                                    

"Assalamu alaikum "cewar Alhaji Ahmad
"Wa'alaykumus salam "cewar Alhaji Umar daga daya bangaren
Gaisawa sukeyi ,Cikin mutumtawa da girmamawa .
"Your son came to me with an important discussion,wai shi baya son wanchan yarinyar ,wai bata da tarbiya and she lack manners,tohmm nidai a ganina gwanda a Nemo masa wata ,Dan nima upbringing din gidansu bai mun ba "cewar Alhaji Ahmad

Cikin dogon nazari da tunani Alhaji Umar yace"tohmm Masha Allah, nima dama wallahi I wasn't happy with the way her father treated us at all,yasa duk Gwiwata ta sage ,tohmm gaskiya ya kamata a duba da kyau "

"Masha Allah , Ina me sunan anty , how far with her masters, ta gama?"
"Nooo tana hanya ,saura progect work"
"Ina jin baka tsaida mata da wani mijin ba ?"cewar Alhaji Ahmad cikin Zullumi
"Aaaaa tukunann ,ko zanba ma 'danane "
Murmushi yayi cikin Jin dadi yace "gaskiya dana fi kowa jin dadi "

Shima dariya alhaji Umar tayi cikin Jin dadi yace "Send him to me first,kafun ya taho kadunan "

"Insha Allah zan fada ,Allah huta gajiya "

Alhaji Ahmad yana sauke wayan cikin murna ya kuma 'daga wayan ya kira Aliyu ,
Dauka Aliyu yayi ,ya isar masa da sakon cewa alhaji Umar nason ganinsa tau InshaAllah zanje qiiiittttt ya kashe wayar...

******
ALIYU
******
Wajen karfe 5
Tunani Aliyu ya shiga yi gameda neman shi da Alhaji Ahmad keyi daga karshe  yaga bazai iya kawo Sai Chan ya tuna kilan maganar da yayi ma Abbie ne,aiko daya ji dadi kuwa ,yasan daddy da fahimta Tashi yayi ya shirya  tsaf, dressing yayi in a plain white captan kayan sun mashi kyau sosai sabida shi ma'abocin white and blue  ne kuma suna mishi kyau sosai , Iwhatch din shi ya dauka ya daura a hannu ,gaban madubi ya koma yayi spraying body dinsa da perfumes and cologne masu 'kanshi  da sanyi ,dakin daukar qamshi yayi gabaki daya😌.......

Fitowa yayi ya dau motar shi ya kama hanyar zuwa gidan Alhaji Ahmad din yana driving dinshi ba gudu sosai qira'a ce take tashi acikin motar ga 'kamshi  turare daya gauraye motar gabaki daya...

Parking motar shi yayi a bakin gate din gidan Alhaji umar horn ya farayi mai gadi ya fito ya leqa sannam ya bude mashi gate din shiga yayi gidan da motar sa bayan yayi parking ne ya fito

gate man ne yazo suka gaisa cikin mutunci sai Aliyu yace masa yayi mashi sallama da Alhaji haka kuwa akayi saiga

Alhaji ya fito suka gaisa amsawa yayi cikin sakin fuska .
Cewar alhaji Ahmad "Ahhhhhh Aliyu  'Dana  kaine haka shigo ciki mana ai nam gidanku ne ".
Kwantar da Kai Aliyu yayi shikanshi yaji kunya kamata yayi kawia ya shiga ,shiga sukayi parlor bayan sun gaisa da Abba Abinci aka kawo mashi da drinks yaci ya koshi yana yaba dadin abincin😋😋😋😋 ....

"Abu turab kana jina ?,alhaji Umar ya kawo karanka,maganar baka son ,wanchan yarinyar da muka nema maka ,hope dai lafiya?"

Kana haidar yayi da kanshi ,bai ma kanshi muguntaba ,ya zauna ya zayyanema daddy Komai da Komai ,
Jin jina Kai daddy yayi cikin gamsuwa ,sanan yace"ehhh gaskiya tunda abun yazo da haka ,dole a fasa aure,tohmm shikenan , I shall discuss the issue with alhaji Umar  "

Cikin jin dadi  haidar ya ringa godiya
Bayan daddy  Ya gama yima haidar bayani akan shawaran da suka yanke akan hadashi aure da fatima

Gabansa yayi mummuna faduwa ,Amma ya daure  yace babu Komai 

Mikewa daddy yayi ya kira Fatima   tazo yana neman ta

hijab dinta ta dauka ta saka shi har qasa ta fito parlor duk tanajin wani iri gabanta Sai faduwa yake yi .

Mamaki ta fara daga daddy ya kirata sai kawai gabanta ya shiga faduwa , Allah yasa lafia tace a zuciyarta ,tana fitowa kuwa ta tarar da baqo sallama tayi ta gaida kowa guri ta samu gefen kusa da daddy  ta zauna.

"uhhhhhmmmm uhhhhmmmm "sukaji anyi Daddy  ne yayi gyaran murya

magana ya farayi kamar haka "ba komai ne yasa na tara ku anam ba saidan muhimmiyar magana da zamuyi "sunan Aliyu ya kira ,dago kanshi yayi Abba ya fara magana Aliyu nasan kanada hankali da tarbiya kai yaron kwarai ne kanada kirki, and above you have the best of manners, kamar mahaifin ka dan haka nida mahaifin ka muka yanke shawarar hadaka da yar uwar ka gatanam ina fatan zakayi mana biyayya dago kanshi yayi

yace "InshaAllah Abbah zanyi maku biyayya"cewar Haidar cikin rawan murya .

"Alhamdulillah Abba ya furta Allah yayi maka albarka nayi matukar jin dadi sosai "
bayan ya gama ne ya juyo ga yar shi fatima .......

Halin rayuwa 💙🤍Where stories live. Discover now