Page1️⃣5️⃣

42 2 0
                                    

babu Wanda yayi yunkurin daukanta,Dan babu wani mai natsuwa a cikin duka su hudin ,doctor ne da nurse suke kokarin ceto rai islam ,Wacce bata San a wata duniya take ba .

Fadin irin tashin hankali da family din suka shiga
Baa magana , Amma duk a cikin wannan tashin hankalin haka aka dauki gawan fatima aka mata sutura aka Kai gidan gaskiya (gidan da kowa da kowa sai yaje ,shugaba ko mai mulki ,Mai kudi ko Talaka , Ya Allah jikan wanda suka rigayemu gidan gaskiya ,ya Allah yasa tamu tayi kyua )

Islam tana hospital bata San ankai fatima ba , bayan su daddy sun dawo daga Kai fatima suna taho nan , tunda ita fatima nata ya kare ,Sai ayi jinyar Mai rai ,
Yan sudan sunso zuwa ,daddy ya hana yace su mata addua kawia bazaayi zaman makoki ba .

Iyayen Aliyu duk sunzo daga kaduna ,da kannensa da kowa kowa .

Ranar wanna family din sunyi kwanar bakin ciki ,Sai dai kawia ayi ma fatima addua .

Bayan kwana daya da rasuwan fatima aka sallamo islam daga asibiti ,Amma har lokacin batayi ma kowa magana ba ,Sai dai tabi kowa da ido Amma bata cewa Komai .

Aliyu shima baci ba sha ,babu yadda baayi dashi ba Amma yaki cin Komai .

Ganin haka yasa daddy cewar su shirya kawia su wuce zaria harda Aliyu .

Kamar yadda daddy yayi ma marigayiya fatima promise,haka suka shiga daki shida Aliyu suka dakko takaddan data rubuta guda uku ,daddy yasa a Aljihunsa ,suka rufe gidan suka kama hanya zaria .

~~~~~~~~~~
Sun isa zaria wajen 4pm ,bayan sunyi sallah , suka futo palour ,intee  tana kwance a jikin islam , sai
ya Mahmoud da ameer a jikinsa da matansa a kusa dashi ,Sai hajiya fatuu ,da Aliyu .

Daddy ya futo da letters din da fatima ta rubuta musu .Ya dauko na farko yaga an rubuta momyn intee(islam), Sai na biyu kuma papa (Aliyu)
Na karshe kuma my one and only dad .

Jiki a Sanyaye daddy ya mika ma Aliyu da islam nasu .
Suma jiki a sanyaye suka amsa ,kowa ya samu waje ya fara karantawa .

*ISLAM*
Jikinta yana rawa ta koma gefe ta bude ta fara karantawa kaman haka
_*"My dearest angel,
Seven years ago I made a promise to you,
Nace miki duk inda crush dinki yake, inshaAllah zan je in Nemo miki shi.
Seven years ago I unknowingly geopardised that promise.
Na aure miki crush dinki ba da sani na .
Had I known Aliyu was your crush, da koh na me zai faru bazan taba bari daddy ya aura mn shi ba
How stupid I was! I should have known that duk wannan ciwon da kika rinka yi, bana missing dina kadai bane, na heartache, kaico na! Na sa hankalin duk a harkan biki, da har ido na ya makance ya kasa ganin heartache da ke cikin idanuwan  ki, senses dina ya kasa sensing zuciyan ki da ke karerayewa. How stupid I was ! Da har zuciya ta  bai fahimta ba, sanda kika dai na mn maganan crush dinki bayan an sa rana da Aliyu.
I'm so sorry angel, so sorry. Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mn, I never meant to hurt you, I never meant to break your heart. InshaAllah zan cika miki alkwarin da na daukan miki, inshaAllah keh matar Aliyu ce.
Ba sai nace miki ki kulan mn da inteesar ba, I know you'll always take care of her.
Bissalam, my angel_.
Ukhty loves you so much *"
Wani irin kuka islam ta fashe dashi ,cikin sauri ta haye sama dakinta ,ta bude drower din da ta saka diery dinta a ciki ,ta dakko sa duk yayi kura ta bude , duk page din da fatima ta karanta Sai da tayi   signing da seen ,alaman ta gani .

Kuka islam take kaman rainta zai futa ,kukan da Batayi bane take yi yanxu .
Tayi dana sanin rubuta wanan diery din .
Sallama ya Mahmoud yayi ya shigo dakin letter din ya bude ya karanta ,dukda bai gane Komai ba sosai ,ganin diery din da islam ta yardashi a kasa ya dauka ,ya kusan 5min yana karantawa .sai lokacin ya gane komai .shiru yayi na wasu yan lokaci kafun ,ya dago islam dake kwance a kasa tana kuka ,bai ce mata Komai ba ,Sai dayi kuma 10min zaune ,ya bata time tayi kuka ,Dan tana bu'katar yin kukan .

Gyaran murya yayi cikin sanyin murya ya fara magana "islam kina jina ,kiyi hakuri kina da ciwon zuciya bana son  damuwar nan ,ta miki yawa ,wannan letter din bana son Aliyu ya gani a yanxu ,ke kowa ma bana son ya gani ,kuma karki fada ma kowa ,kaman yarda yar uwarki take son ki aure Aliyu Insha Allah zaki auresa ,kodan inteesar " ya fada sannan  ya kuma nunfasawa sannan ya Cigaba da cewa
"Zanyi tunani sosia sosai ,Insha Allah zuwa gobe zamuyi magana ,and plsss ki cire damuwa ,Fatima kuma adduan mu take bu'kata ba Komai ba "ya fada tare da mikar da ita ,bakin toilet ya kaita yace ta wanke fuskanta ,zuwa tayi ta wanke fuskanta sanna suka fita palour .

*ALIYU*
Tunda ya amsa letter a hannun daddy jikinsa yana rawa ,Amma  babu Wanda zaiyi ,fita palour din yayi ya Shiga Motansa ya bude letter din ya fara karantawa kaman haka
*~'''_
*"miji na abun alfahari na  Wanda ko wace  mata zatayi alfahari da Kai ,duk son da nake maka ,Amma Ina 'daga ido na kalle inteesar Sai naji sonka kaman daga suna ne kawia ,babu Kalman a dictionary , ban taba tunanin zan fada kogin son ka ba irin wannan,  unlike in fairytales my heart didn't skip when I first set my eyes on you, but slow and steady na durmaya cikin tekun son ka. I know our parent made d best option na hada mu aure,being married to you was the best thing that ever happened to me, thank you for giving me the best moment of my life,and duka muna alfahari dashi auren ,kuma nasan basuyi regretting ba , ni yau gani nima zan zaba maka mata Wacce tafini Komai ,Wacce Insha Allah bazaka taba regretting, wacca zata zame maka sanyin idaniya, wacca zata so with all heart, someone that would take care of our inteesar wholeheartedly, Insha Allah,ko Wacce Zaka ji a wajen daddy Insha Allah,
I love u so much first love._'''~*

Wani uban zufa ne ke keto masa ,kaman yayi  wanka da ruwa ,tunani ya fara Wacce fatima take son ya aura ,bayan ta tafi tabarshi ,a nashi tuanin bazai kuma aure ba ,daga mutuwarta da kwana daya kuma ,ace har ta masa mata .

Jiki a sanyaye ya koma palour din.

*DADDY*
Yana gama mika musu letter din ya haye samansa ,Sai da ya dakko ruwa yasha sannan ya samu bakin gado ya zauna ba dakko letter din ya warware ya fara karantawa..............................

Halin rayuwa 💙🤍Where stories live. Discover now