Page8️⃣

42 2 0
                                    




"Haba alhaji ,tunda muka zo garin nan baka bi ta kaina ba ,you left me stranded in the parlor, maimakon kamin bayani ,noo Ka barni ni daya ,kuma a gabana Ka wuce daki ,sanda doctor yazo sanna ka kuma futowa "cewar matan da suka zo da daddy me sunan hajiya fatu

Kai daddy ya rike ,shi wallahi ya manta da ita ,tunda yaji islam is very sick, gaba daya ya manta da wata "Haba hajiya I'm really sorry, na Dan shiga damuwa ne ,Marainiyan yarinyar nan ,da ko uwarta bata sani ba ,Amma Dan Allah kiyi min aikin afuwa "

Murmushin takaichi tayi "Sai tace tohmm alhaji 'dana kowa ne ,Allah ya bata sauki ,muje na duba ta "

Cikin farin ciki yace "muje na nuna miki daki ,kiyi wanka ,islam din tayi bacci yanxu"

Wacece *HAJIYA FATUU*
Doguwa ,fara ,tana mugun kama da daddy da islam .Itama cousin dinsu daddy ce ,wani soja ta Aura Dan Nigeria
Aiki ya Kaishi niger ya ganota ,ya aura ,daga baya kuma suka koma Abuja da zama ,shekarunsu 7 da aure ,Allah yayi aka kasheshi a wajen yaki .shine ta koma gida shekaran 2, bata 'taba haihuwa ba ,a gida aka sa daddy ya aureta ,yace "Sai yazo ",.shine wanan zuwan nashi aka saka ya aureta suka taho tare .

🔙

Tun daga lokacin taga yadda daddy ke kula da islam ,Sai abun ya 'bata mata rai ,har ta kullace islam din a rai,
Yau kwana uku da zuwanta ,Amma daddy bai samu lokacinta ba ,kullum a wajen islam yake yini ,dukda ta samu sauki ,kuma ya fuskance tana cikin damuwa ne sosai .
Amma ita hajiya fatuu bata zuwa gaida islam .
Islam idan ta sakko ta gaisheta bata amsawa ,Sai kawai ta futa harkanta (kunsan masu irin sunanmu basa daukar raini).

Sooo da daddare ranar islam ta sakko downstaie ta samu su daddy suna zaune da ya Mahmoud da hajiya fatuuu,
Sai islam ta gaida daddy da yaya Mahmoud, Amma bata kalle hajiya fatuu ba ,

Sai daddy yace"angel bakiga hajiya bane?"ya fada cikin daure fuska shi baya son raini !

Charab hajiya fatuuu tace"Ai alhaji bata 'taba gaidani a gidannan ba ,har cewa tayi ,idan ta warke Sai na har gidannan "ta fa'da cikin kukan makirchi .

Haba tunda dady yaga zahiri kuwa,ya fara 'fada ,ta inda yake shiga bata nan yake futa ba .

Hakuri islam ta basu ,Dan ita abunda yake damunta yafi wannan, she can't deal with any additional drama.

Ta wuce daki abunda ,daman abinchi ta sakko suci.

,bayan yan mintuna Sai ya Mahmoud ya Debo ma islam abinchi ya wuce dakinta ,ba tare da daddy ya kula ba .

Hajiya fatuu ,cikin 'kissa da kisisina ta wuce kitchen ta 'debo ma islam abinchi tace"alhaji bari na kaima 'yanmata na abinchi ,Ka mata fada tayi fushi ,bana son ta 'ki cin abinchin dare "

Tana hawa benen Sai ta tsaya bayan 5 min ta dawo palour tana share hawaye ,kallon daddy tayi cikin munafinchi ta fara cewa"Dan Allah alhaji kaje kaba islam hakuri ,ta dena mugun furici a kaina ,Wallahi Ina sonta da zuciya 'daya ,bansan yadda zanyi mata ba "

Rain daddy ya kuma baci ,cikin fusata ya Haura sama ,ya bude dakin islam , a cikin ya tadda islam tana kuka suna magana da Mahmoud ,ga abinchi a bisa cinyarta ta fara ci

Tusssss yayi yana kallonsu sanan yace"me kika cewa fatuu data zo kawo miki abinchi yanxu"ya fada yana kallon islam din

Shuru tayi bata ce masa Komai ba
Sai Mahmoud ne yace"daddy kaji na rantse maka ,hajiya bata zo nan dakin ba "ya fa'da cikin dacin rai

Shuru daddy yayi Sai kuma yace"tace kince ba'kya cin abinchi bla bla bla "

"Wallahi daddy bata shigo ba ,kuma daddy dazun ma sharri tayi mun ,Dan Wallahi kullum Sai na gaisheta ,Amma bata amsawa ,warning tamin idan na kuma kulata a gidannan Sai ta Illatani ta 'karasani tunda ba lafiya gareni ba "islam ta fada with full assurance.

Daddy yasan basa masa 'karya ,kuma ko islam tayi karya ,mahmud bazai goyi bayan karya ba .

Cikin doguwar nazari daddy yace "tohmm shikenan na ta saloon kenan ,zan kamata da hannuna ,bance kowa ya ce mata Komai ba ,duk abunda ta miki ,kar kice Komai ,idan na dawo ki 'fada min, Ai gobe zara zata dawo ,zansan abunyi "Ya 'fada tare da fita dakin yana jingina makirchi da hypocricy irin na mata.

*Washe gari da yamma *

Allah ,Allah take a Tashi islamiyya,ta wuce gida taga uktiy amarya, she can't wait to see her dearest ukhty, bikin saura 6days ,yau ta dawo daga sudan ,gaba 'daya hankalinta baya jikinta ,bata San me malamin kecewa ba .

"Halimatu,halimatu ,see me after the class"
Sai yanxu hankalinta ya dawo jikinta , ta amsa masa da "tohmm ustaz "

Bayan an tashi islamiyya ,cikin sanyin jiki ,taje ta samu malam ,Sai yace "sauri yake yi yanxu ,tazo da wuri gobe idan Allah ya kaimu ".

Tana isa gida ,da gudu ta shiga gidan ,tana kwallawa uktiy kira , Turus tayi ganinsu a palour tare da hajiya fatu,suna ta fira abunsu ,hankali kwance .

Sallama kawai tayi ,ta wuce daki abunda ,
Abun ya daurewa zarah Kai ,tana ta cewa"angel baki ganni bane ?" Amma Ina islam ta rigada ta wuce sama abunta .

Tana shiga daki ta fashe da kuka ,ta dakko waya ta kira ya Mahmoud "ya Mahmoud,yanxu na dawo islamiyya,naga uktiy da anty fatuu suna fira suna dariya ,Ina ta Murman ganinta Amma ko 'dagowa batayi ba😭"

Wani mugun tsaki mahmoud yayi sannan yace"ban 'taba sanin zarah bata da hankali bane Sai yau ,Sai tayi mata sharri hankalinta zai kwanta ,ki rabu da ita "cewar Mahmoud cikin bacin rai ,

Bayan wuce war islam daki ,cikin 'kissa ta kalle zara tace"Fatima kiyi hakuri ,islam bata son taga ko wani mutum dani ,Dan Allah kice tayi hakuri ya yafe min ,ko me nayi mata ,Wallahi Ina sonta tsakani da Allah , ko magana bata min a gidan ,har gaisheta nakeyi Amma bata amsawa, tasa tatta Mahmoud baya min magana a gidannan "

Idan rain fatima yayi dubu ya baci ,Mesa angel zata yi haka
Hakuri ta bama hajiya fatuu sanan ,tayi mata Al'kawarin zata yima islam 'fada

Dakinnasu ta nufa cikin baccin rai .........................p

Halin rayuwa 💙🤍Where stories live. Discover now