Page4️⃣

77 4 0
                                    

Flash back
Shekaru 43 back .

Samari biyu ne a boys quarters din, da Umar da Ahmad. Aminan juna ne sosai, zaune suke cikin mutuntaka da yarda da juna. Duk kan su biyun dalibai ne a A.B.U, sun taso a gari daya ne, but there where not very close, sai da suka zo makaranta ne suka kara shaquwa sosai, har suka kama hayan gida daya.

Ahmad yana enginering ,while Umar yana karanta medicine ...
Ahmad dan maiduguri while Umar Dan niger republic ,dukansu iyayensu gudun hijira sukayi, dalilin haka sai suka zama a unguwa daya.

Dukda Iyayensu ba masu arziki ne bane ,Amma suna da rufin asiri .

Zamansu babu laifi ,suna studying sosai, suna dan hustling.
Basa zaman banza ,
Ahmad gyaran electic yakeyi ,hakan ya kasance duk tun yana gyara ma abokansa a hostel ,har ya fara gyara na kudi sosai sosai ,har hostel din mata yana zuwa yana musu gyara .
Daga hakane har cikin unguwansu ...

While Umar ,yana da ilimn addini sosia sosai ,islamiyya ya samu guda biyu a gefen unguwansu yana koyar da hadda ,da islamiyya .
Kuma yana saida books na addini dana boko ,har ya Kai yana rubuta books both islamiyya da boko ,
Tafiya yana tafiya ,ya fara organizing 'yan 100level da 200level private turorials na kudi......

Gaskiya basu tsaya nuna rayuwar karya ba ,kaman yan kaduna ,dukda a kaduna suka tashi ........

Haka dai rayuwa ta kasance musu
Bayan Shekaru 7

Ahmad harya gama service ,yana aiki abunsa ,
Shi kuma umar ,internship yake yi ,bai dade da gama karatun ba,shiya futo overall best a faculty dinsu ,ya karba kyautuka babu adadi ,harda scholarship aka basa ,na Cigaba da karatu a sudan ,yanxu kawia jira hake ya gama intenship da service sannan ya tafi.

Rayuwansu dai yana lafiya daidai Alhamdullah,
Har gida suka samu suka siyarma iyayensu
Suna zaman lafiya ,kaman 'yan uwan juna .

Idan 'daya bashi da abu ,'dayan yana taimakawa sosai sosai .

Bayan shekaru 5
Umar da Ahmad kowa ya samo matan, aure zasuyi ,
Ahmad ya samo mata 'yar Gombe da yaje wani aiki gombe ya gano ta ,kuma suka daidaita Alhamdullah.

Sai kuma umar ,'yar Sudan zai aura ,da yaje master's ne ya gano .suma suka daidaita .

Ahmad a garin kaduna zai zauna ya Cigaba da kula da iyayensu , while umar a ABUTH ya samu aiki ,so a zaria zai zauna da matanshi

A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah,
Bayan shekaru 20
Na le'ka su ahmad umar
Kaduna na fara zuwa anan naga Ahmad yana zaune da matanshi cikin kwanciyar hankali da 'Ya'ya
Aliyu Haidar ne babba ,Sai Khadija,Yusuf , hafsat

Rayuwansu cikin kwanciyar hankali

Umar kuma dai babu laifi 'ya'yansa uku
Mahmoud ,Fatima da halimatussadiya .
Matanshi ta rasu wajen haihuwar sadiya .
Fatima ne dashi suke raini sadiya .
Sau biyu yana 'kara aure ,Amma baya saa, suta malternating 'ya'yansa .

Ganin haka ne ,yaki yin wani aure ,har Sai sunyi aure ,sanan zai kara aure

Mahmoud da Aliyu ,suma abokai ne suma tare suka yi secondary ,sannan aka Kaisu England sukayi universty of Oxford.

Fatima da Khadija suka mate ,suna shiru sosai ,koda Khadija tazo university dinta zaria ,tare suka yi a gida Amma .khadija tayi aure hakama hafsat .

Ita kuma fatima tunda batayi aure ba ,shine ta daura masters dinta

Ita halimatussadiya sun bata shekaru 10 .
Ko autan gidansu Ahmad hafsat ,ta girmeta ,siyasa ita bata da 'kawa Sai yayarta fatima ,Itace uwar kuma best friend dinta........


*******
*Aliyu*
*******

Aliyu Ahmed
Dan saurayi mai jini a jiki, yana da kwarjini, da jini a jiki, ga zuciyan neman na kan sa, his dream is to be self established, dan ya taimaka those that are in need, economic ya karanta , ya dade bai samu aiki bane, shine yake aiki part time a administrative office din demonstrates secondary school , kuma yana dan bussiness din sa, Abban su yayi, yayi ya basa tallafi, amma yaki yarda , yace yafi so ya zama self reliant. Abinda ma yasa, ya fara samun case da wannan yarinyan kenan, sbd duk da shi dan masu kudi, shi bai da wani kudi sosai. Amma yanzu bussiness dinsa ya fara bunkasa, kuma wani company ma da ya basu CVs dinsa, sun ba shi offer.

*********
*Fatima*
*********
Fatima umar
Mace Mai zuciyar muslimchi , she is one in a million, idan zaa tara mata dubu ba lalle a samu guda Goma irinta ba ,pharmacy ta karanta ,yanxu tana master a clinical pharmacy,kuma mahaddaciyar alqurani.

Mace ce mai kyau, strong in heart and iman, very intelligent and loyal, ita ta Debo yan Sudan din duka ,kama take dasu ,mutane sukance tafi islam kyau ,tunda islam ita kuma da daddy take kama buzaye .

Tana da samari sosia sosai ,duk inda ta shiga Sai ance Ana sonta .
Amma bata basu fuska ,Sai tace ita matan aurene .
Bata da buri daya wuce islam ,ta dauka duka rayuwanta akan islam , she could sacrifice her self for her baby girl, ita burinta Sai islam tayi aure kafun tayi ,bata son tayi aure tabar islam,babu uwa .
Kuma islam yarinyace ,

Shiyasa da dady ya saka ta a gaba akan maganar aure ta birkice ,akwai wanda suke son aure ta .

********
*Islam*
*******

Yar budurwa Mai kyau da ilimi ,halimatussadiya sunanta ,sunar mahaifiyanta aka maida mata ,Ana haihuwarta mommynsu ta rasu ,
Shiyasa suke kiranta da islam ,Ita ta buyo daddy a Komai nashi ,hatta yadda yake magana haka takeyi ,itama tana da fada kamanshi ,suna mugun kama ,duk Wanda ya ganta yasan shine mahaifinta
Ko yanayin dariyarsu iri daya ,haka shima mahmud .
Wata sain haka suke zolayar Uktiy cewar Itace bare a cikinsu .

Tana ss2 a demonstration secondary school, Amma tace ma daddy zatayi jamb da Waec ss2.

Tana da kokari sosai sosai ,
Tana mugun son Uktiy dinta ,Dan bata son taga daddy ko ya Mahmoud sunyi mata fada, da take 'karama ,idan suka yi ma Uktiy fada ,gaba take yi dasu ,kuma bata cin abinchin
Har Sai sun bata hakuri

Sun tashi cikin tsantsar so da kaunar juna ,basa son abunda zai samu daya daga cikinsu ...........

Halin rayuwa 💙🤍Where stories live. Discover now