Page1️⃣3️⃣

37 3 0
                                    

Islam ce ke serving dinsu abinchi a dinning area ,duk sun zauna

Fatima "woohoo yau zanchi abinchin angel after so many years ,gaskiya nayi missing abinchi "cewar fatima happily,duk Wanda ya ganta yau yasan she's extraordinary happy.

Aliyu ya dago yana kallon fatima with a smile on his face ,seeing how happy his wife is ,sannan yace "gaskiya nima na kosa naci abinchin nan ,na manta yaushe Naci tuwo , sis-in-law yau kina da babban kyauta "

Murmushi kawai islam keyi ,batayi magana ba .kawai she's not comfortable standing behind Aliyu ,but she have to endure .

"My baby ,is our indomie ready?"cewar islam tana tambayan intee dake kitchen .

"Yes anty , kizo ki juye mana "cewar inteee

"Okhh baby "

Islam ce ta futo ita da intee da bowl din indomie dinsu .

Dariya fatima tayi take cewa"yanxu angel har yanxu bakya cin tuwo,so da kike Sudan haka kike cin Indomie idan aka yi tuwo kenan ?",
"Noo snacks nake ci ,anty Summy sau biyu take bari na Ina cin indomie a week ,kuma mijinta yana son tuwo ,shiyasa nake nawa girkin kawai,idan kuma ina school anty ke dafa min "
"Ayyah anty Summy tana da kirki Ai "cewar Fatima tana zuba tuwo a baki .

"O my God! Gsky ukhty wannan tuwon first-class ne, nayi bala'in missing girkin ki." cewar fatima tana santi, tana lumshe eyes tsaban dadin abincin. Shi dai Aliyu sai kallon ta yake, spoon fatima ta dauka tayi spooning tuwo da miya tace ma Aliyu "Sweetheart, you've got to taste this. Oya haaa" murmushi yayi ya bude bakin nasa tasa mishi tuwon.

Islam dake parlor tare da intee tana satar kallon su Fatima da Aliyu dake kan dinning table, taji zuciyar ta tayi wani irin tsinkewa da fatima ta ba Aliyu abincin a baki. 'Dauke idanuwan ta tayi daga kallon su ta maida shi ka abincin ta. Sai kuma ta sake 'dagowa dan son ganin reaction din Aliyu game da girkin nata.

Aliyu shi ma lumshe idanuwan nasa yayi tsaban dadin abincin, yana ayyana wa a ransa a ce dai Fatima was not exaggerating, girkin yayi dadi sosai. Ba da ban ma ya ga tuwo miyan ku'bewa bane a zahiri, da idan aka rufe masa ido zai ce wannan ba tuwo.

Dariya Fatima tayi ganin reaction din Aliyu, daga gani tasan abincin ya masa dadi.
"So how was it? " ta tambaye Aliyu.
"Heavens! " ya fada yana jinjina kai. Ya kalli islam din dake kallon sa a parlor. Nan da nan suka janye idanuwan nasu, dukannin su gaban su na faduwa. Amma dai islam taji dadi sosai yana ratsa ta, ganin yanda Aliyu yaji dadin abincin.

~~~~~~~~~~~
Kwanar islam uku a gidan fatima.
Yau ya Kama Friday .

Wajen 8 after dinner , Fatima was not her self bata jin dadi ,Amma ta ringa daurewa ,
Shi kuma aliyu yana da assignment da aka bashi a wajen aiki sai ya musu sallama ya wuce study room ,while fatima da islam suka Cigaba da fira ,wajen 9 islam suka wuce daki ,haka Itama Fatima .

Wajen 9:30  Fatima taji wani ciwo ciki ,cikinta yana murdawa ,gashi aliyu yana study room ,her phone is not close to her balle ta kira shi ko islam ,Juyin arziki ta kasa , duk tayi mugun zufa ,tun tana daurewa ,har abun yafi karfinta ,gashi ta kasa yin screaming, karfinta duk ya kare .

Cikin ikon Allah Sai ga intee tazo da gudu tana cewa"mommy plss kice na antyna tare zamu koma ,ita zata rikeni "

Cikin tsananin ciwo fatima tace "Insha Allah intee da ita zaki rayuwa ,ita zata zama maihaifiyarki ,go and call her for me "

Cikin gudu intee taje ta kirawo islam ,tana cewa mommy is calling u tace dake zan rayuwa .

A Rude islam ta karasa dakin ganin yadda uktiy take ,gaba daya kamanninta ya bace .

Inteee ta wuce ta kira Aliyu ,Shima a rude ya shigo dakin .

Hospital suka nufa ,a hanya sai magana take ,su islam sun dauka zafin ciwo ne ,Amma ita fatima tasan me take cewa .

Bayan an shiga da ita ,abun yaci tura ,kusan awa biyu ,doctors basu futo ba .

Su islam da intee Sai kuka sukeyi ,shi kanshi Aliyu daurewa yake yi ,dazai samu daman kuka ,daya dade dayi .

Doctor ne ya futo babu annuri ko daya a fuskanshi ,ya kalli Aliyu yace ya samesa a office  .

Tafiya Aliyu yake Amma kaman yana counting steps .
A haka har ya shiga office din doctor .

Kallonsa doctor yayi na kusan 30seconds sannan yace "mr Aliyu Ahmad ,Matarka ta haihu baby boy Amma Allah ya masa rasuwa ,and Itama ta kamu da ciwon zuciya ,Allah yana barazanan da rainta, she's in a very critical condition, she needs your prayers right now.

Wani irin 'daci Aliyu yaji yana shiga ran sa, ya rasa inda zai sa kan sa. Ji yayi komai ya tsaya masa cak. 'kafafuwan sa ne suka jawo zuwa hanya fita, koh lura da su islam da ke son masa magana suji ya halin Fatima ke ciki bai yi ba. Samun kan sa yayi a harabar masallacin, koh ma ya akai ya shigo masallacin oho, alwala yayi ya shiga masallacin, ya shiga yana rokon Allah. He can't imagine loosing Fatima, he just can't loose her!..................

Halin rayuwa 💙🤍Where stories live. Discover now