BABI NA HUDU

2.7K 346 7
                                    

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️
     _Ba shiga birni ba_

©️®️ *safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA HUDU*

   Gidan babu kowa yayi shiru  kasancewar yaran dukka sun wuce makaranta maman ummi tana dakinta wanda tun sape bata gilmawarta ba itam tana nata dakin saidatagama kintsa duk abunda xatai na ayyukanta sannna ta dauko kudin da baban amir yabata sannan tanupi dakin maman ummi akwance ta tarar da ita  tana kallo ummi najin sallamarta tararrafo gunta tadauketa tana cewa xoki naushi dan uwanki na ciki yadda kikasaba sannann tai sallama takarasa parlourn tashi tai maman ummi tai tazauna fuskarta babu walwala maman amir takarasa  tasamu daya daga cikin kujerun parloun tazauna tanacewa muntashi maman ummi murya acushe ta amsa tanacewa lafiya lau to madallah tafada tana mika mata kudin dake dake hannunta amsa tai sannan tace wannan kuma namaye maman amir tadubeta tace kayan siyayyar yarane jiya baban amir yabasu"
"Jiya da yaushe?"
"Sanda kike can kina sake kashe kanki wajen mijinki,mmn ummi bakyajin magana,amma Allah yagani nayi iya abinda zan miki,shine shaida" daga haka bata jira taji me zata fada din ba ta miqe tafice a dakin.

     Da kallo mmn ummin ta bita takaici na cikata,wato kudin siyayyar 'ya'yan nata ma yafi qarfinta?,yafi qarfin yabata da hannunta saiya kaiwa kishiyarta?,qwafa taja ta dauki kudin ta irga,saita rabasu biyu tana ayyana abinda zatayi dasu,rabi kawai zatayi musu siyayyar dasu,saura kuwa zubin adashinta zatayi dasu,ribar qafa kenan ta fada cikin ranta.

********   ******    *********

"Wallahi wallahi babu shegiyar da zanwa girki,girki?,ni nace ka qaro auren kenan,idan sunsoma su rube saboda basuci abinci ba" ta qarasa maganar tana kashe famfo gami da daukar botikin wankanta tashige bandaki ta banko qofar.

     Shuru ne ya ratsa tsakanin baban amir da mmn amir dake tsaye cirko cirko,bacin ran mmn ummi yana kamashi qwarai da gaske,cikin halayen datake masa bai taba ganin daya daga ciki mmn amir ta gwada masa ba,koda a sanda take neman auren maryam din,kunya duka ta dabaibayeshi,musamman daya tuna sanda babu kunya ba komai ya baiwa mmn amir kudin cefanen abincin 'yan jeran mmn ummin a wancan lokacin,yace lallai ta girka,a sannan batajin dadi ta gaya masa amma yarufe idanu ya caccaba mata magana,yana ganin kamar tsabar kishi yasanyata tace bata da lafiya qalau take,baiso akai girkin gidansu ne,azo aga kamar bai isa da gidanshi ba,ko kan gidansa ba a hade yake ba,kasa magana ya motsa zaibar wajen
"Ka kawo kawai sai ayi kamar na wancan karon" yajuyo yana dubanta,farinciki ne qasan zuciyarsa,saidai yana ga bai mata adalci ba ayadda tayi nauyi haihuwarta nan da satittika ya bata abincin masu jere,ga wadda takw ziqau ma tace ba zatayi ba inaga ita
"Ki barshi kawao,zankai can wajen gwaggwo sai ayi a kawo musun" ko daya batason yakai wajen mahaifiyarsa kafa wata sabuwar maganar kuma ta bullo,tasan halin surukar tasu qwarai da zafin rai da fada,,wani sabon bacin ranne kawai
"Babu damuwa,tunda anyi wancan wannan ma bazai gagara ba" kai yake jinjinawa,qimarta da nauyinta na kamashi,a sanyaye yace tabiyoshi daki ta karba.

     Kudi ya irgo masu yawa ya miqa mata,ta amsa tana dubanshi tare da kallon kudin
"Sauran kiyi amfani dasu" ya furta yana kallon idanunta,godiya tayi masa kana ta miqe ta fito,sai data nutsu ta lissafa kudin da zai isa ayi komai,sauran canjin suna da yawa ba laifi,data lissafa taga sun kai mata kudin datake na cikon da zata sauya plasma dinta.

********   *****    ********

      Zaune take a falon qafafunta na amiqe,gefe wata matace wadda a qalla ba zata wuce shekara talatin ba,kana kallonta zakaga kamar da suke da mmn amir,hira suke jifa jifa har dayar ta jefo magana kan gidansu mmn amir din
"Yaushene tariyar amaryar taku ne?"
"Saura kwana goma inajin ko sati,don cikin satin nan masu jere xasuxo" baki ta tabe sannan tace
"Wannan karon kamar ba kishiya za'a miki ba anty halima,shi kuma mijinku haka Allah gada masa" itama nata bakin ta tabe
"To yaka iya da abinda yafi qarfinka?,idan fada yafi qarfinka ai wasa kake maidashi samira,wancan karon da hankalina yayita tashi me aka fasa?,meye kuma ya sauya?,tunda ya gingimo yakuma dauki aniya aisai ka tayashi da idanu da kuma addu'a ko?" Kai ta girgixa
"Haka yake,amma banga kina wani shiri ba" qaramin murmushi tasaki
"Nice kuwa me shiri,amma yanzu ta abinda yake cikina mu rabu lafiya nake tukunna,bama wannan ba,bari na dauko miki kudin plasma din nan ki tafi dashi,yanzu abinda ya rage kawai kiyi xancan labulayena da mutumin,kudin sun samu shi nake jira,yayimin masu kyau sosai don Allah kalar kujerun,zan dauko miki dinkunana ki tafi dasu duka ki ajemin"
"Amma dai anty halima aiko kala biyu kya dauka ko saboda zuwan amarya"
"Xan dauki uku ma,amma nikam yanzu batasu nake ba,ta lafiyata nake"
"Allah dai ya raba lafiya"
"Amin amin,don Allah idan baban abba zai barki kizo mana jibin ki tayani girkin 'yan jeren,yaran duka suna makaranta kya tayani zama ma"baki samiran ta kama
" au wannan karonma keya hada da girkin?,bai baiwa waccar ba taji yadda kikaji?"
"To meye a ciki?,ko nayi ko banyi ba zaikai wani guri ayi,kuma a hadamu duka a zaga,sannan kuma babu wani abu da zai fasu,kinga ni mubar wannan xancan don Allah muje na lissafa abinda yarage na baki" daga haka ta yunqura tamiqe samiran ta bita tana sake jinjinawa juriya da qarfin halinta.

HANGEN DALA ba shiga birni baWhere stories live. Discover now