👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA*👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
*BABI NA BIYAR*
Aqalla ya kusa minti ashirin tsaye gaban mudubin yana dudduba kanshi yaga inda baiyi ba a jikinsa,shaddace 'yar ubansu ya saka sky blue,ba abinda take sai sheqi da walqiya,hakan hular kansa itama babu abinda take sai daukar ido,komai na jikinsa daya sanya mai tsadane,kasancewar jin kansa da yake yaudin rana ce ta musamman,kuma yanason ya fitar da rufaida kunya ita da qawayenta ranar dinner din kamar yadda tace.
Wayarsa dake gefe ce tadauki burari,da hanxari ya dauka yaduba,rufaidan ce cikin hanzari ya daga ya kara a kunnensa,yayin da fuskarsa ta yalwata ta kuma wadatu da fara'a kamar wanda aka yiwa albishir an 'yantashi daga wuta
"Dear...inata jira fa"
"Karki damu baby ina kan hanya,ganinan zuwa karki fushi don Allah,yanzu ba lokacin fushinki bane kinsan ya...." Maganarshi ta maqale sanda yaga shigowar mmn amir dakin.Kanta tadauke kamar bataji abinda yake fada ba din na,shi yasa sam bataso ma shigowa dakin ba a irin wannan lokacin donta kaucewa ganinsa da kuma kaucewa ganin abinda zai motsa mata kishinta,saidai ba yadda zatayi Allah ya qaddara saitaji din.
Hakanan ya diririce,yar kunya ta saukar masa,saiya hau kame kame
"A'ah,mmn amir ba zaku bane?" Murmushin qarfin hali tasaki tana zama gefan sabon gadonshi sakamakon nauyin da takeji cikinta yayi,wanda ta tabbatar an sauya gadonne saboda amarya,saidai bata taba nuna masa ta gane hakan na,mmn ummi ce tayi qaura da kwana a dakin,tace dacan bai sauya saboda su ba saidon wata,to tabar kwanan dakin,tanajinsu amma bata saka musu baki ba
"A wannan yanayin da nake ciki hutu nafi buqata aiko?" Ta fada don ta baiwa kanta kariya,don tanajin koda ace lafiya lau take bataga abinda zaya kaita wajen bikin ba,kai yashiga kadawa
"Hakane kam,haka ne,Allah ya raba lpy"
"Amin,dama hajiyace tace kafin ka fita ka bada sauran kudin cefanen abincin wuni,saboda ba lallai ka kwana gida gobe ba ko saboda baqi,da sassafe kuma za'a je 'yan kaba a siyo kayan miyan"
"Toh...ba damuwa" ya saka hannunshi cikin aljihu ya fito da sabbabin kudi wanda ya tanada saboda liqi wa amaryarsa ya irgo ya bata,hannu biyu tasa ta amsa kana tamiqe ranta na mata suya,zuciyarta na zafi amma tana qoqarin ganin ta danneta ta hana mata tasiri,a hankali ta juya tafice,saiya bita da kallo kunya da tausayinta na ratsashi.Dakin mmn ummi tawuce donkai mata kudin saboda ita hajiyar tace ta baiwa saboda ranar tafado ranar girkinta.
Zaune ta can uwar dakanta,saman gefan gado tama fuskantar mudubi,saman gadon baje yake da kaya kala kala,daga na kwalliya zuwa na sakawa,da alama ta bajesu ne tana zaben wadanda zata sanya ne,ta kuma gama zaba din,don lace ne ta wareshi gefe hadi da mayafin da takalmi masu tsini,awarwaraye xuwa sarqa da dan kunne.
Cikin mamaki mmn amir ya qarasa shiga dakin gamida sallama idanunta a kanta,daga kai tayi daga shafa jambakin da take tana amsa mata sallamar sannan ta sake maida kanta,ta mudubin mmn amir take kallonta,tasha makeup sosai wanda tajima rabonta dataga tayi kwalliya irin haka
"Da alama fita zakiyi ko?" Mmn amir ta tambayeta cikin shakku,da mamaki ta waiwayo tana dubanta
"Ya kike tambayata kamar bakisan meke faruwa ba,wai tsayama,ba zakije bane banga alamun kin shirya ba?" Kai mmn amir ta girgiza cike da mamaki,saboda abinda yafarun kafin yau bata tsammaci mmn ummi xatace zataje partyn ba.Rufaida ce ta rarrabawa qawayenta number wayar mmn ummin suke kiranta suna zaginta tun randa sukayi hatsaniya da rufaidan ta wayar bbn amir din,a rana sai a kirata sama dasau talatin,data gane sune tayita mita har kunnen bbn amir din,toya danyiwa rufaidan magana,tace yace tana bata haquri,a hado da katin dinner guda biyu tace abasu tana gayyatarsu ai duka mijinsu ne.
YOU ARE READING
HANGEN DALA ba shiga birni ba
Short StoryTSUMAGIYAR KAN HANYACE,KAMA DAGA MATAN AURE ZUWA 'YAMMATA