BABI NA SHIDA

2.6K 285 5
                                    

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA SHIDA*


     Tunda safiyar garin asabar ta waye tasake shiga fita hayyacinta,tunda ta idara sallar asuba ta kasa komawa bacci,sai zirga zirga da take tsakanin tsakar gidan soro zuwa nata dakin,idanunta kacokam yana kan dakin baban amir,wani mahaukacin kishi takeji,yanxu nan da wasu awanni kenan yaxama nasu su uku?,tashin hankali,saita dora hannunta aka tana neman inda zata sanya zuciyarta da ranta taji dadi,wani irin radadi da zugi gamida qunci takeji cikin zuciyarta,saita dauki wayarta ta kirayi hafsat.

Bugu hudu ta daga
"Ya akayi mmn ummi,mun tashi lpy"
"Babu batun tambyar lafiya game dani,tunda kin san babu ita,yaushe zaki shigo,wallahi hafsat jin gidan nan nake kamar wata qiyamata ko lahira"
"Karki damu ina sallamar babansu minal zan shirya na taho"
"Don Allah karki dade"
"In sha Allahu" aje wayar tayi tana furxar da iska daga bakinta.

Wayar tatace tasake ruri,data duba sai taga lambar qanwarta ce,ba jinkiri ta daga sai taji muryar mahaifiyarta,kuka ta sanya
"Meye haka maryam?"
"Umma yaune daurin auren fa?"
"Sai kuyi haquri ai,haka Allah ya dora muku"
"Don Allah umma kixo,don Allah"
"A'ah,nikam bazanzo wannan gidan naku ba,zandai turo miki ruqayya da zakiyya,sai yayarku duka zasu taho tare"
"Toh umma"
"Zasu taho miki da saqo,saiki sawa ranki haquri,tunda haka Allah ya dora masa" daga haka sukayi sallama,saita danji sanyi da maganar da sukayi da ummantata.

Qarfe takwas tasoma jin motsin yaran a tsakar gidan,tun cikin satin suma yaran ta sallamasu gaba daya,mmn amir ce keta hidima dasu,hattasu abun ya shafesu,ita kuwa maman amir ko a jikinta,saboda kai kawon yaran da kula dasu da takeyi ya dauke mata hankali gami da debe mata kewa da bacin rai,idan tana tare da yaran sai taji ta manta da wasu abubuwan.

Miqewa tayi ta isa bakin window tana leqen abinda yake faruwa a tsakar gidan,mmn ummin ce zaune saman kujera 'yar tsugunno,gabanta sabbabin shaddodine ruwan omo,saman cinyarta wasu daga wandunan yaranne tana saka musu tazuge,mubarak na tsaye a kanta da alama yayi wanka ya shafa mai yana jiran ta gama saka masa tazugen tabashi ya saka,yayin da mmn amir din ke aikin tana gyarawa  hanifa wankan da takewa usman.

Wani baqinciki da bacin rai ya kamata,wato har wani anko ya yiwa yaran na xuwa daurin aurenshi kenan,ita batama sani ba?,kafin tayi kowanne yunquri baban amir din yayi sallama yashigo gidan,hannunshi dauke da wata shaddar kalar ta yaran,da alama tashice ya amso.

Qurawa fuskarshi idanuwa tayi sanda yake qarasowa gaban mmn amir,fuskar da ada babu wata fuska da takeso da qaunar gani amma a yanzu babu fuskar data tsana take jin haushi da takaicin gani irinta
"Sannu da aiki maman yara" ya fada yana murmushi,har cikin ranshi kuma yanajin dadin yadda take shirya yaran zasu daurin auren tare dashi
"Yauwa" ta fada ciki ciki fuskarta sam babu wannan fara'ar daya saba gani,duk sai yaji jikinsa yayi sanyi,tayi qoqari matuqa kuma tana kanyi,yasani cewa baiwa Allah yayi masa da uwar gida,wadda ta tsaya kai da fata wajen ganin ta hade kan gidan waje daya,ya tabbatar da maryam ce uwar gidansa tofa sai abinda hali yayi,yasani sarai cewa suk maigidan da yayi rashin dacen uwar gida toya kade ya gama yawo,duk wadda zai aura daga baya mawuyacine idan batayi koyi da wasu dabi'u nata ba,uwar gida itace ginshiqin gida,itace kuma kamar turken mai gida da dukka wani ahu daya mallaka,idan ka dace a ita saika godewa Allah.

Yanayin dayaga fuskarta yasa ya gaza wucewa,saiya soma kame kame,inda daga bisani yac"wannan zaman bazaki gaji ba?,kawo tazugen na qarasa saka musu kije ki huta"kai ta kada
"A'ah,barshi kawai,aiba lokacin hutu bane yanzu koda naso na huta din" haka ya tsaya yana ci gaba da tayata gyara kayan yaran har kowa ya sanya nashi sannan ya shige dakinsa donya shirya shima,ta bishi da kallo tanajin wani bacin rai da kishi yana taso mata,ta dauke idanunta taba karanta "hasbiyallau la ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim".

HANGEN DALA ba shiga birni baWhere stories live. Discover now