👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA*👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
Haske Writers asso 💡
*BABI NA SHA BIYAR*
*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*
*ALKAWARIN ALLAH*
*DAURIN BOYE*
*KUNDIN KADDARATA*
*MUTUNCIN MACE*
*DANGANTAKAR ZUCI*
_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_
Dukka wadan nan abubuwan mmn amir batasan dasu ba,saboda tana cikin dakinta suna qarasa gyara kayansu amir a drower dinsu,bata ma sake ganin fuskar kowaccensu ba bare tasan da sauyin fuskarsu ba.
Baishigo ba kuwa dan halas sai bayan sallar isha'i,yaran sunajin sallamarsa gaba daya suka runtumo suna masa oyoyo,kowa ya maqalqaleshi,shima yayi mamakin ganin nasu,saboda baisan da dawowar tasu ba,hanifa ce cikin zumudi tasoma cewa
"Abba....zo kaga dakinmu yazama sabo,mama ta canza mana kayan daki" idanu yafiddo duk daya tsammaci quruciyarta ce kawai
"Kai haba hanifata,muje nagani" dai dai lokacin da rufaida tayi burum ta yaye labulenta tafito tana kallonshi
"Duk dakunan nan zaka wuce kasoma shiga nasu?" Waiwayowa yayi yana dubanta cikin mamaki,wannan bashine karon farko ba,sunsan tsarinsa,dakinta shine dakin da yake soma shiga duk sanda yadawo gidan,yayin da wadda keda girki kuma itace qarshe,daga ban zai wanka yaci abinci da sauran abubuwa
"Eh,ina nan shigowa bari nafito tukunna" daga haka yayi gaba zuwa dakin mmn amir.Wani sabon bacin ran ne yasake taso mata,wato namiji dai munafuki ne,shi yabada kudin shi yasa yana shigowa gidan yasoma shiga dakin kenan don yaga irin kayan,banda haka ta yaya zai wuce dakunansu yashige nata?,haka tasaki labulen takoma kan kujera taxauna tana dakon shigowarsa,ta rantse yau sai tayi masa tas,saita wanke ciki dabai.
Yatsanta ta ciza tanajin zuciyarta na suya,waita yaya ma?,me yasanya yake nuna rawar qafa akan wannan tsohuwar matar tasa mai haihuwa hudu zatayi tabiyar?,bata taba tunanin xataga kwatankwacin haka daga gareshi ba,amma koma meye wallahi sai inda qarfinta yaqare.
Sanda yashiga mmn amir din na qasa a zaune,ta dora qafafunta da suka kumbura saman abu mai tudu donta samu kumburin yasabe,fuskarta a sake da fara'a ta amsa sallamarsa tana masa sannu da zuwa
"Iyyeee,shi yasa hanifata tace nazo nagani,ashe mamanta amarya tazama" yafada yana bin dakin da kallo gamida leqawa,dariya tasaki
"Da gaske dai halimatu kin zama hajjaju,eh lallai kudi basa magana" yafada cikin dalon tsokana,wannan karonma dariya yasake bata sosai
"Kai bbn amir,wani yaji wannan zancan saiya dauka da gaske kake,kawai kudin 'yar sana'ata ne dana adashin dana shiga sai yanzu na dauka na hada duka da kudin tsaffin kayana,sai yaya mansur dayamin dan ciko"
"Ma sha Allah,ma sha Allah,Allah ya sanya alkhairi,yasa rai aka yiwa"
"Amin" ta amsa cikin jin dadi.Biyewa surutun su amir da suka dan jima basa tare yayi,sunata bashi labarin gidan inna,har yadanja lokaci ba tare daya sani ba,saida mmn amir ta ankara sannan ta fiddashi cikin dabara,amma duk da haka saida hanifa da usman suka bishi.
Da sallama itama yashigar mata kamar yadda yasaba,tana zaune ta gama cika ta gama batsewa,daqyar ta amsa idanunta kamar xai fado akanshi,ganin yaran tare dashi yasake tunzurata,cikin tsawa ta zazzare musu idanu kana tace
"Me kukazoyi?!,ku fice maza kubani waje,da wasu idanunki guru guru kamar anyi barin qwai" tuni yaran suka tsorata,sai suka wuce sumi sumi suka fice daga dakin,yayin da bbn amir yabisu da kallp har suke fice kana yamaida kallonshi kanta,yafuskanci fushi a fuskarta,hakan yasanya ya mata uzuri saboda baisan meya bata mata rai ba.
YOU ARE READING
HANGEN DALA ba shiga birni ba
Short StoryTSUMAGIYAR KAN HANYACE,KAMA DAGA MATAN AURE ZUWA 'YAMMATA