BABI NA SHA TARA

4.5K 342 48
                                    

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA BAKWAI*

*_ALBISHIR A GAREKU MA'ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA'ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K'AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO &  NA MISS XOXO*

*DAURIN GORO & NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*

GAME BUQATARSU ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER WAYAR

09032345899

Tsaye take a tsakar gidan hajiya hariran tazubawa sarautar Allah idanu,gabanta yayi mummunar faduwa sanda tagama irga kawunan ragunan da aka gama shigowa dasu,kai uku ras,kenan raguna ukun aka yanka duka?,kuma ita zata soya kenan?.

Bata gama wannan tunanin ba hajiyan tafito daga kitchen hannunta riqe da ludayin miyar da sai datayi kamar tamutu kafin tagama hadata
"La'ilaha illallahu muhammadarasulullahi,yanzu dama haka suka kwasheki suka kai mishi ke baki iya komai ba,yanzu duk yadda na tsaya kai da fata ina nuna miki yadda zaki hada miyar nan sai da kika tafka kura kurai?" Raita bata sosai,saboda itadai bata tabama qoqarin hada girki irin najiya ba
"Amma dai hajiya idan ba'acemin sambarka ba,ba'a tsinemin ba"
"Yimin shuru shashashar banza,daukomin ungurnu ta kwarara tun banjin kunya ba" gaba tayi kamar zata sanya kuka saboda azabar bacin rai,sai kuma ta dakata tajiyo tana kallon hajiyan
"Hajiya,wai dukka ragunan uku nakinne aka yanka kuma za'a soya?"
Sai data daga kai tayi mata wani kallo sannan tace
"Qwarai kuwa,an gayamiki nan gidan marowata ne?,duk wanda yashigo saiyaci yaqoshi,ban iya rowa irin taku ta yaran zamani ba" gabanta ne yafadi,wani gumi yasoma yanko mata,batasan ta furta
"Tashin hankali!" Ba,saiji tayi hajiyar tace
"Wanda ba'a sa masa rana ba" haka tagama tsaiwarta da sanyin jiki tanufi inda hajiyar ta turata.

Tun daga gyaran kashin dake cikin tumbi fa hanji ta raina kanta,haka takusa wuni bakin famfo quda yanata binta,ga baqi da hajiyar ketayi maza da mata cikin kwalliya,amma ita tana zaune tana bauta,ko abinci ta kasa kaiwa bakinta,ta qulu iyaka,baqinciki yakai mata wuya,ba ita tagama suyar hanjin ba sai sha biyu na dare,haka ta kwanta jikinta duka yana mata ciwo.

Washegari tadasa suyar nama,aitun ba'akai ko ina ba ta fuskanci bazata iyaba idan ba kasheta hajiyar kesonyi ba,saboda haka tasaki suyar tashiga bandaki tayi wanka tadawp daki tahau shafa mai.

Cikin masifa hajiyan tashigo tana dubanta
"Au sakarmin aikin kikayi?"
"A'ah hajiya fa,zafi nakeji nace bari nadan watsa ruwa sainafi jin dadi" saita sassauta fuskarta
"Saikiyi kiyi kigama ki koma kar wutar tamutu,don idan tamutu wani jidalin na sake kunnata yasameki"
"Wallahi saidai yasameki hajiya amma bandani" tafada cikin ranta.

Laqai laqai tadinga yi,harta saka kaya tana fakon hajiyar,sai data tada sallah sannan tadauki mayafinta ta yafa,dazu taga inda aka kawowa hajiyan barka da sallah,ya bankada tadauki dubu biyu a ciki ta zari takalmanta tafice ba tare da hajiyan tasani ba.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan jibril,a sannan maman ummi na daki ita da qannenta biyu da sukazo mata,mmn amir itama na nata dakin akwance saboda ciwon marar da taketa dan fama dashi lokaci lokaci,wanda a yadda takeji a jikinta ba zata wuce satin ba zata haihu,itama tayi baqin yammata biyu daga gidansu da suka kawo mata tuwon sallah,sai cinyar saa daga yayanta,wanda jin basuyi layya ba wannan karon yasa ya aiko mata dashi,dakai da qafa na rago,yaran na tsakar gida suna wasa abinsu sukaga shigowarta,sai suka bita da kallo,sun bude baki suna niyyar mata sannu da zuwa ta watsa musu harara
"Duk wanda yayi magana saina yanke bakin" hakan yasa sukayi shuru,tabude dakinta tashige abinta ba  tare da kowa yasani ba.

HANGEN DALA ba shiga birni baOnde histórias criam vida. Descubra agora