BABI NA SHA BIYU

2.6K 266 17
                                    

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
_Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA DAYA*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*

*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_




Idanu suka hada da mmn ummi,sai kawai ta waske tana bata rai ta isa bakin tukunyar tasa hannu tabude murfin,ganin yadda tayi baqiqqirin saita saki tsaki,dai dai sanda bbn amir yashigo kitchen din saboda ya zaqu ya fita,yana neman makara ne
"Ina abincin?" Ya tambaya yana duban rufaida da tukunyar taliyar dake gabanta
Sautin dariyar mmn ummi ya karade kitchen din,wanda hakan yasanyasu dukka suka waiwaya suna dubanta,sai kuma ta gimtse kamar ba itace tayi dariyar ba,ta soma 'yan waqe waqenta tana ciro wasu fulasanta tana sauya musu waje.

Sosai rufaida ta qulu,ta sani sarai da ita take,amma sata a gidan barawo rance ne,kuma duk wanda yaci tuwo da ita miya yasha,ba zata lamunya ba,kuma saita fanshe dariyar data yi mata din
"Ka ganta qonewa tayi wallahi" ta fada cikin salon shagwaba tana wani yarfe hannu,wanda hakan ya qular da mmn ummi wadda kunnuwanta suke kansu
"Qonewa kuma?,garin yaya zaki dora taliyar da bata wuce minti takwas ko goma ta gama dahuwa harta qone?"
"Na dora ne bacci yadan rinjayeni naje na kwanta kanta qarasa".

Dariya mmn ummin tasake kwashewa da ita cikin salon waqa tace
"Kayan kitchen mama tasiya min,abinci dahuwar 'yan gayu,wani kalarma sai an dandana,ayye sama mata,mata" daga haka ta sanya kai tafice abinta tana sheqa dariya.

Sosai rufaida ta qarasa qulewa,a zafafe ta waiwayo tana duban bbn amir
"Kanajin matar nan ko?,nifa take tsokana,wallahi kaja mata kunne niba sa'arta bace,idan ba haka ba nixan dauki mataki a kanta dakaina" nan take yaji ranshi yabaci,ita sam bata abinda zaici da barna da kuma bata mishi lokaci take ba,sam bashi ya dameta ba?,bacin rai ya hanashi magana,sai kawai ya rabeta ya isa gaban gas din.

Qwai uku ya dauka ya fasa ya kada,yana neman frying pan ta qaraso wajen
"Ina maka magana amma kayimin banxa kamar bada kai nake ba?" Ta fada itama ranta yana baci sosai,tana ganin kamar ya wulaqanta ko kuma yana bayan cin fuskan da mmn ummi tayi mata kenan.

Kai ya daga ya dubeta kawai,sau tari a kwanakin nan idan tana wanu abu sai yaga kamar ba rufaidanshi daya sani ba,kamar wata rufaidan ce ta daban,sai yaga kulata ma bata bakine,tunda ita batasan ya kamata ko bai kamata ba.

Har yagama soyawa yajuye yadauka yawuce tana tsaye,shurunsa saiya sake bata mata rai gamida kuma tunzurata qwarai,fuuu tabi bayanshi dakin,ta sameshi zaune harya soma karyawa da ruwan tea din data dafa mishi,da kuma qwan data soya.

Kanshi ta tsaya cikin bacin rai,don tana jin ya kamata tanuna mishi bacin ranta sosai
"Ni zaka wulaqanta jibril a gaban matarka?,ni rufaida ni zaka yiwa haka,na kawo.maka qararta amma kayi kunnen uwar shegu da qorafina,wannan shine kulawa ta musamman da kayi alqawarin bani,shine darajar tawa da kace zaka daukaka fiye data kowacce diya mace?,jibril tunda nashigo gidanka nake ganin abubuwa na cin fuska da wulaqanci,dama haka kake?,ina duka alqawuran daka daukarmin?".

Kai ya tada ya dubeta
" ke bakisan kinyi ba dai dai ba?,bakisan abinda kikayi shi yafi cancanta ki maida hankali akansa ba ba wani shirmen banxa ba?,ga abinda yafi muhimmanci sam ke bashine a gabanki ba,kawai ta abinda aka miki kike na daukar miki fansa?,hakan shine dai dai a wajenki kenan?"ranta yasake baci,wato shi baima ga abinda akayi mata ba kenan,abinda aka mata din shine shirmen banza
"Amma dai aiko yaya kayi magana ko kodan saboda ta rainani,idan yaso mayi solving wannan issue din daga baya" shuru yayi yaba kallonta,wato bata fahimceshi ba kenan har yanzu?,sai kawai yamiqe daga cin abincin yana qoqarin danne bacin ranshi da mamakinsa,yadauki jakarsa da muqullin motarsa ya gewayeta yana fadin
"Saina dawo"
"Jibril" ta kirashi cikin bacin rai daya riqe mata wuya,amma saiya wuce baiko waiwayo ba.

HANGEN DALA ba shiga birni baWhere stories live. Discover now