👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA*👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
Haske Writers asso 💡
*BABI NA SHA ASHIRIN*
Kafin ta kwanta Sai data tabbatar ta sallami yaran bayan ta sanyasu sunyi addu'a kowa ya kwanta,sannan tadauki Abba tawuce zuwa dakin bbn amir. Cikin Pampers ta shirya Abba ta sauya Masa Kaya masu nauyi sa'annan itama tashirya cikin Daya daga cikin kayan baccinta,tun Tana shiryawar tagama tafiya da bbn amir din,Allah ya Sanya a lokacin abban yayi bacci,saboda haka ba Bata lokaci Suka Lula zuwa duniyar ma'aurata. Fadar yadda Daren ya wakana man Bata bakine,kewa ce ta hadu da gyara,Sai bbn amir din ya tsinci kansa cikin wata duniya ta daban,zai iyacewa bai taba tsintar kansa cikin wanna situation din ba. Koda asuba da Suka tashi salla bayan ta hada musu ruwa Mai dumi sosai sunyi wanka,saiya rasa me zayace Mata,Tana zaune gefansa Tana lazumi "Allah na gode Maka,na gode Maka Allah da baka barni na wulaqanta wannan kyauta Mai daraja daka yimin ba,halima.....Allah yayi Miki albarka sau babu adadi" sassanyar murmushi tasaki,wani farinciki itama Yana ratsata,ba shakka farinciki Miji shine farincikin duk wata mace tagari "Amma banjin zan sake gangancin barinki ki dauki hutu Koda 'yan hudu xaki Haifa,na fuskanci wani horo kamar Kika yimin a fakaice"idanunta tajuya kawai Tana dariya,kusan zata iyacewa ya canka.
A lokacin zuciyarta na cike taf da qunci da kuma kishinsa,Bata da wata hanyar da zata baiwa jiki da zuciyarta hutu a sannan Banda ta sallama musu Shi,ta gama karantar next level da rayuwar gidan nasu ta fada a nutse kafin tasan hanyar da zata bi ta magance komai, beside ma Tana da buqatar hutun na haqiqa a halin da take ciki Don tasamu ta rabu da cikin dake jikinta lafiya,alhmdlh koma meye kwalliya ta biya kudin sabulu dari bisa dari. Hirarrakine masu Dadi Suka biyo baya tsakanin ma'auratan,wadanda Suka qara musu wata qaunar juna dakuma fahimtar juna din.
Bayan wani lokaci bbn amir din yakoma yasake kwanciya kafin lokacin fitarshi,bata bari takoma ba saboda tasan akwai shirin yara makaranta da sallamar maigidan da gidan kanshi,don haka gari na qara sha tafita ta kama ayyukanta bayan ta tabbatar da duka yaran sunyi sallah
Bakwai da rabi na safe kusan komai ya kammala,don yaran duka sun shirya kowanne kuma da abincinsa na tafiya makaranta,yau dinma mai adaidaitanne zai kaisu,saboda haka ta sallamesu suka wuce ba tare data bari sun tada bbn nasu ba,sai data gama dasu sannan tadawo ya kama sauran abubuwan da suka rage matan.
Takwas da rabi rufaida tashigo kitchen din inda take wanke wanke tana raba idanu,kusan tun sassafen takula da cewa idanunta biyu,da alamu kuma baqin kishi ya hanata sukuni ne,kallo daya tayi mata ta dauke kai,idanun rufaidan kawai sun isa shaida maka bata samu isashshen bacci ba,kamar zata saki dariya saidai idan tayi hakan tasan cewa kamar ta siyawa kanta raini ne,don haka saita dauke kai taci gaba da abinda take.
Qerere take tambayatta abun kari,bawai don zataci ba,ta tanbaya ne don tace bata gama ba ko babu kodai wani abun makamancin hakan ta tada bala'i cikin gidan wanda zai tada bbn amir din ba tare daya shirya ba,saidai kafin abun takaicin da hannu ta mata nuni da inda natan yake ba tare data dubeta ba,sanda ta isa daki taga yadda ta shirya break fast din sai baqinciki ya kamata
"Wai ita komai sai tayi wanda yafi nawa,duk yadda nake haqilo da qoqari amma saitayi wani abun daya wuce hankali,yanzu don Allah yaushe ka tashi ka sallami yara ka gyara gida kayi wadan nan soye soyen,bayan kitchen din ma dukka kayan abincin nasu yayi low sosai,saboda wannan yanayin na batan kayansu bbn amir din" haka tazauna tana cizon yatsa.To kusan dukka kwanakin da mmn amir tayi na girkinta babu abunda ta tsinta sai bacin rai da baqinciki,don a yanzun sam mmn ummi ma bata gabanta,mmn amir din tafi tsaye mata a rai,babu ma kamar ranar da bbn amir din yatashi babu ko sisi a hannunsa yasa mmn amir din tabata kudin cefanen abincin gidan gaba daya,ranar ji tayi ina wuta ta sanyata.
ESTÁS LEYENDO
HANGEN DALA ba shiga birni ba
Historia CortaTSUMAGIYAR KAN HANYACE,KAMA DAGA MATAN AURE ZUWA 'YAMMATA