Na
QURRATUL-AYNWattpad@JannatQurratulayn
FITA TA FARKO
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.
Wannan labari kusan ya faru a gaske, sai dai sauye-sauye na tarin abubuwa daya samu saboda gujewa kace-nace ga al'umma idan har suna ko sunan gari ko jigon labarin ya yi shige da rayuwar wani ko wata ko wani shashi na mutum a gafarci alkalamina, ina rokon Allah ya dafamin cikin wannan gajeren rubutun da zan yi, ya amfani dukkan al'ummar da fadakarwa, abin da yake kuskure Allahu ya gafartamin amin s amin.
Godiya ga daukacin masoyana a duk inda suke a fadin duniya yauma gani tafe cikin sabon labarina Wanda na baiwa suna BAHAGUWAR RAYUWAR Allah ya bamu ikon bibiyar wannan labarin, ya bani ikon kammalawa cikin aminci amin.
>>>>>DASHEN LABARI<<<<<
Kauyen garin Tsamiya goma, mai suna MAINA dake karkashin jahar jigawa state, gari ne wanda Allah ya wadata su da ni'imar kasa wato noma, tare da tarin kiwo kala-kala, wanda duk Allah ya dora nasibinka akai zaka ga sun samu yalwatacciyar ni'ima ga dabbobinsu, tanan sukan yi amfani su sarrafa nonon dabbobin nasu wajen kaiwa bakin salati a kullum, rayuwa ce wacce suka taso a haka suna dasawa a junansu cikin yalwa da kaunar juna, sai dai abu guda daya tilo duk wannan ni'imar da Allah ya basu ya hanesu da sanin abu guda daya ne tal wato Alkibla, kuma duk da cikar garin da tarin al'umma da yalwatacciyar ni'imar da Allah ya basu an gaza samun mutum daya tilo mace ko namiji wanda zai yi wa al'ummar garin kyakykyawan mafarkin sama masu madafa, karni baya karni masu yawa sun shude suna rayuwa akan turba guda daya wato Al'ada wacce suka yi gadonta tun tale-tale tun karnin kaka da kakanni amma hakan bai taba damun wani a cikin rai ko damuwa da son sanin a wacce madafa suke ba?***
Gabashin almuri (maghriba) tarin matasan 'yan mata da samari ne gungu guda, cikin farfajiyar bishiyun itacen Maina wanda yake zagaye da wajen, tsakiya kuma fili ne mai dauke da rairayi mai yiyuwa garin ya amsa sunan MAINA ne saboda tarin bishiyun maina (Darbejiya) da Allah ya wadatasu da shi, gada da wake-wake kawai ke tashi a wannan filin, gefe guda kuma masu cinikayya ne kala-kala suke ciniki mazansu da matansu, mazan wasanni suke na burgewa wasu na wake tare da samarinsu, wasu kuma zallar mata ne suke wakokinsu cikin nishadi, daga can gefe jikin bishiyar Maina wacce tafi kowacce itaciya girma matashiyar budurwace zaune ta buga uban tagumi tana binsu da kallo daya bayan wanda ke lure da yanayinta kadai zai iya fawwalawa kallonsu take wasu kuwa zasu iya dauka haddar abin da ake yi a wajen take yi a zahiri kenan, amma a badini dukkan ragamar tunaninta kaf ba ya ga wajen yana can wata nahiyar wadda ita kanta bazata iya ayyana takamai-mai tunanin me take yi ba a wannan lokaci ba.
Wata siririyar budurwa wacce Bata kaita kiba da tsayi ba ta karaso da gudu zuwa wajenta, mayafinta daure a kugunta fuskarnan tasha kwale na zanan kwalli bakin nan ya ji uban jan jambaki tamkar zai zuba kasa, zama ta yi gefanta tana fadin.
"Ni kam Ishatu (Aisha) har tsayin wanne lokaci zaki dauka kina damuwa akan auren Dalladi ne? Ya kamata a ce kin mai da komai ba komai ba, ki aureshi ko babu komai zaki fita daga cikin jerin mutanen da ake ba da kwatance da su a cikin wannan garin".
Matashiyar budurwar ta dubeta da kulawa, fuskarta wasai babu nuna damuwa ko jin haushin maganar data fita daga bakin wacce Bata yi matsammani ba, illa tsantsar mamaki da ta dubeta da shi kafin ta ce.
"Haba Zainaba..! Ya kike tunani irin na sauran mutane? Ya kamata a ce kin yi tunani irin na mutane daban, a tunaninki ina damuwa ne akan auren Dalladi? Ko kusa ko kadan, bana tsoro bare shakka akan wannan auren, damuwata daya na rasa dalilin da yasa dangina tare mutanen gari suke ganin aibu akan cewar ni ce mace ta farko daya tilo data fara haura shekara ashirin da biyu a gida ba tare da aure ba, wacce riba auren wurin da suke yiwa 'yayansu ya tsinana musu? Tsayin lokacin da basan adadin wanda ya wuce cikin wannan muguwar al'adar ba, ada ina tunanin ke ka dai ce mai tunani irin nawa, sai kuma yau naga sabanin tunanina, Zainaba..!".
Ta sake kiran sunanta tare da rike hannunta a karo na biyu tamkar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru tana mai juya kallonta wajen da shewar gungun 'yan mata ke tashi ko tantama ba zata yi ba, tabbas tasan zancen gizo ba ya wuce na koki, suna zancene akanta, Zainaba ta fizge hannunta daga cikin na Isatu tare da mike wa a fusace da sauri Ishatun ta mike itama ta kamo hannunta tana girgiza mata akai alamun kar da taje wajen.
"Wai yaushe kika zama sanyi ne Isatu?".
"Yaushe kika zama zafi ne Zainaba?".
Murmushi suka sakarwa junansu tare da komawa suka zauna, yayin da aka fara shigowa da fitilun aci bal-bal filin saboda duhun almuri (maghriba) daya jima da mamaye gurin, kai kace jiran kadan suke tuni gurin ya sake kaurewa da wasanni kala-kala da ciye-ciye.
"Kina ganin rayuwarmu zata cigaba da tafiya a haka ne?"."Wai mene yasa a kullum kike irin wannan maganganun Isatu?".
Zainaba ta yi tambayar, yayin da Isatu tabi tarin gayyar samari da yan matan dake zaune wajen da kallo tana nazarinsu daya bayan daya ko wanne dake cikinsu harkar gabansa yake hankali kwance babu abin da ya damesu, Ishatu ta dawo da kallonta ga Zainaba da itama duban nata take yi kafin ta ce.
"Kawai ina ji a jikina kamar rayuwarmu da gyara Zainaba, sai dai ban san mene gyaran ba, bansan me zan gyaraba, ban kuma san wanda zai taimaka mu gyaraba, amma tabbas muna bukatar gyara".
"Gyara wanne iri? Kuma mene aibun rayuwar da muke yi a yanzu? Karki manta haka muka taso muka ga ana yi, kakan kakanninmu ma haka suka yi rayuwarsu to akan me yasa kike ganin kamar muna cikin BAHAGUWAR RAYUWA ne?".
"Ban da masaniya akan tambayoyinki domin nima abin da make tambayar kaina kenan a kullum har yau babu amsa, Amma na rasa dalilin da yasa zuciyata da ruhina kullum tambayarsu guda daya ce BA AKAN DAIDAI MUKE BA? KO WACCE RAYUWA CE DAIDAI WACCE TA DACE MU?".
NWA®
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Historical FictionKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa