SOYAYYATA DA SHI

56 2 0
                                    

💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
     ( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )

*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*

*RUBUTU DAGA ALƘALAMIN......* ✍️

       ✨ *RAHMA SABO USMAN*✨

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*  ☀️
    ( *_Home of eloquent and trusted writers of the nation_* )

*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*

Bayan sun idar da sallar ne,ta janyo jakarta haɗi da zaro handout za ta fara karatu Zainab ta tsada ta ta ce,"amma kin manta da ya ce za ku yi magana." Ɗan taɓe baki ta yi sannan ta ba ta amsa ta ce,"kin san shaf na manta,so na ke in ɗan duba chemistry ɗinnan kafin mu shiga next lecture kwana biyu sam ba na boko." Ta na kaiwa nan ta miƙe tsaye haɗi da turawa Zainab jakarta bayan ta zare wayarta a kai ta na cewa,"zauna ki duba wani abu kafin na dawo mu yi discussing." Ba ta jirayi amsarta ba ta yi ƙasan benen da sauri domin ita ma ta ƙagu da ta ji me zai gaya mata.

Kamar ko yaushe a riƙe da phone ɗinsa,ta tarar da shi ya na latsawa. Ba ta ko yi sallama ba ta nemi guri ta zauna kusa da shi ta na faɗin,"to mrs phone ana kanta kenan." Sai yanzu ya ɗago idanu ya kalleta ya ce,"babu sallama?" Murmushi kawai ta yi ba ta tanka masa ba sai ma ta canja topic ta ce,"ka ce za ka sanar da ni wata magana." Wayarsa ya mayar aljihu ya ɗanyi shiru na tsawon wasu mintoci ya na ƙarewa fuskarta kallo.
Hararshi ta yi ta gefen ido ta ce,"ni fa ba na son kallo." Muryarta ya kwaikwaya ya ce,"ai ni ma ba kallonki na ke ba,ka wai ina tunanin ta ina zan fara ne." Dariya ta tuntsire da ita har ta na tafa hannuwa sannan ta ce,"faro ta sama kawai malam."

In a serious tone ya ƙara zuba mata idanu bayan ya ɗan muskuta da zamansa,ya na facing ɗinta ya ce,"A'isher ina sonki,so na gaskiya wanda babu namijin da ya taɓa yiwa mace a doron ƙasa.
Sonki ya yi min mummunan kamu tun a ranar da na fara tozali da ke,ranar da ku ka fara lecture kin zo nan gurin amma ba ki lura da ni ba. Nutsuwarki,murmushinki da kuma uwa-uba shigarki ta kamala su ne su ka janyo hankalina har na ji na tsunduma cikin kogin sonki tare da fara linƙaya ba tare da na farga ba.
All those crisis da su ka rinƙa faruwa a tsakaninmu ni na yi creating ɗinsu intentionaly wasu kuma sun gibta bisa ƙaddara." A razane ta ɗago ido ta kalle shi"yess." Ya furta ya na ɗaga mata gira sannan ya cigaba da faɗin,"tun a ranar na ke son in yi miki magana amma na rasa ta ina zan fara domin tun da nake ban taɓa tosting budurwa ba a rayuwata hakan ya zame mini very difficult to approach you ban san ya a ke ba.
Har ku ka shafe ku ka ka shafe tsawon two weeks ku na lecture kullum na kan zauna a can." Ya yi nuni da hannunsa wani guri mai duhuwar flowers a ɗan nesa da gurin kaɗan sannan ya cigaba,"a ranar na zo zan mi ki magana na ga kin yarfata ni tun daga nan tsoro ya shige ni.
Na ayyana cewa ba zan samu abinda na ke so ba,the other followed day tun six na fito a gida ina zaune a bakin a Gambo Sawaba domin na san a can kike ina jiran fitowarki domin na bayyana mi ki *SOYAYYATA* amma sai hakan ba ta samu ba domin kafin na ankare kin yi nisa gaggawar tuƙa motata na yi haɗi da biyo sahunki a hankali. Har mu ka ƙaraso bakin faculty ɗinnan na sona na bayyana miki a keɓantaccen guri amma ke sai na fahimci kallon ɗan iska ki ke yi min,yanzun dai gani a gabanki ina roƙonki da ki ba ni gurbi a cikin zuciyarki." Gabaɗaya jikinta ya gama mutuwa da jin kalamansa,duk wata gaɓa da ke cikin jikinta ta gama yin na'am da saƙonsa sai dai mishkila ɗaya wata ɓoyayyiyar zuciyarta na tunasar da ita cewar ba musulmi ba ne hakan ba zai taɓa yuwuwa ba. Amma ina so ba ya jiran lokaci ko kuma yadda ta wani keɓaɓɓan ɓangare wanda ba shi da tasiri saman zuciyarta na mata barka a matsayin wadda tafi kowacce mace dacewa a duniya kar ta sake ta yi wasa da damarta domin bature kan ce "it comes only once in life." Domin haka cikin fatali da shawarar da ƙasan zuciyarta ke bata,ta yi murmushi ta ce,"tabbas kunnuwana sun yi marhabin da jin wannan zazzaƙan zance daga bakinka,wani sashe na zuciyata ya yi na'am da hakan. Gangar jikina ta yi maraba da saƙonka sai dai kash ƙasan zuciyata na gargaɗina da kar na amince da kai domin mu na kan maban-banta addinai duk da baka sanar da ni hakan ba amma na ji a wata kafa ta daban." Girgiza kai ya yi ya ce,"da fari na ji daɗin yadda gangar jikinki ta amince da buƙatata da wuri haka ba tare da ta wahalar da ni ba,ita kuma ƙasan zuciyarki ki ba ta haƙuri ki kuma lallashe ta ki sanar da ita cewa zan shigo addininta in dai har ina da rabo kafin mutuwata." Kallonshi ta yi ta ce,"gaskiya wannan ba hujjabace in har ka na son *SOYYAYATA* da kai ta tafi dai-dai dole ne ka musulunta domin ba zan yi soyayya da kai ba alhalin kai ba musulmi ba ne." Riƙe mata hannuwanta biyu ya yi ya ce,"ki yi min afuwa ki saurare ni ki ji ko ni wanene kafin ki yanke wannnn ɗanyen hukuncin a kaina."

*MU HAƊU A SHAFI NA GABA.*

SOYAYYATA DA SHIWhere stories live. Discover now