16

2K 240 31
                                    

Milk shadda ce a jikinsa sai farar hula, fuskarsa na ta sheki kamar shi ne angon ga wani kamshin tutare da yake mai sanarda zuwansa tun kamin ya iso. Abu biyu ne babu a tare da shi walwala da sai kuma yar ramar da yai kadan. Da sallama ya shigo falon Hajiyarsa sannan ya zauna da bismillah, kamin ya mika mata gaisuwa daga inda yake zaune. Sai ta amsa masa tana ta kallon yanayinsa yanayin da ya sauya masa tun sati biyu da suka gabata.

“Hajiya ta sai yanzu ake karyawa?”

Ya fada yana kallon kofin tea da ke hannunta.

“Aa yau da dumamen tuwo na karya sai yanzu na ke shan tea”

Be sake cewa komai ba ya maida hankalinsa a gurin tv da ke kunne.

“Ba kaje aiki ba yau ko kuma ba a aikin ne yau?”

“Zan je yanzu, Suwaiba na kai gidan Abdulhamid, daman ta matsa min tun kwanaki baya tana son zuwa na hana ta sai yau dai na kai ta”

Har lokacin da yake maganar be kalli gefenta ba. Yana shirin mikewa tsaye ta ce.

“Jiya Mal Dalhatu ya zo nan”

Da sauri Abdallah ya juyo ya kalleta jin ta ambaci mahaifin Halimatu.

“Mi ya kawo shi?”

“Yace yana ta son ya zo yai mana godiya be samu dama sai yau saboda yanayin jikinsa”

Dan murmushi yai ya kawardar fuskarsa.

“Baba Karami akwai karfin hali, miye abun godiya a ciki ai yi wa kai ne”

“Yi wa kai ko kashe kai? Akan me za ka dauki nauyin irin wannan dawainiyar haka? Ya fada ko ruwan da aka sha a gurin wunin nan kai ka kawo su”

Cikin muryar da ke bayyana rashin jindadinta tai masa maganar hakan kuma ba karamin mamaki ya ba Abdallah ba, domin be taba ji ko ganin ta hana su yin wani aikin alheri ba musamman abunda ya shafi yan'uwa.

“Akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka dauki nauyin hidimarta? Har da wani daukar yara ka saka su makarantar kudi ina ruwanka ba su da uba ne?”

A karon farko ta yi masa maganar a tsawace tana dire kofin tea da ke hannunta da karfi.

“Ban yi dan wani abun ba Hajiya, a gaban ki Alhaji ya bar mana wasiyar taimakon yan'uwa da mabukata, kuma tun ba yau ba idan za ayi biki a gidan Baba Karami mu na yi masa abu mai nauyi saboda mun tashi mun ga Alhaji na yin haka kuma ya mana wannan wasiyar, ba hidimar aure kawai ba har abincin da za su yi ke da kanki kin sha daukar abu daga nan ki aika musu balle kuma mu da muke jininsa”

“Ba alheri na ke hana ka yi ba, wannan karon ka yi alherin ne a gurbin da be kamata ka yi shi ba, akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka nuna mata kula har da duniyarka”

“Hajiya idan Halimatu ta auri Abdulhamid kamar ni ta aura, ni da Abdulhamid duka daya ne kuma.... ”

Hannu ta daga masa.

“Na fika sanin wannan kai da shi duka ni na haife ku, ina magana ne kawai akan abunda yake bayyane ni na san Abdulhamid ba son Halimatu yake ba, ita ta janyo ra'ayinsa ba kuma saboda kowa ba sai dan kai”

“Haka ya fada miki?”

“Ba sai ya fada min ba, ni na san waye ďana, be taba zo min da maganar wata mace ko son yin aure a wannan yanayin da yake ciki ba sai a wannan lokacin, mutumen ma da neman lafiyarsa ya saka a gabansa? Rana tsaka ya zo min da zancen auren nan idan ba ita ta nuna masa ba taya za ayi ya kawo wannan tunanin a ransa? Kuma ya rasa mace aure sai Halimatu bazawara? Mai yaya hudu yana saurayinsa bayan kuma ba iya komai yake ba Allah yasa dai tsakani da Allah zata zauna da shi”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now