Sai da suka gama tsara komai da lauyansa, sannan ya taso tare da shi suka shigo falon Hajiya, a lokacin 8 har da yan mintuna na dare. Da kansa ya tura kofar falon ya shiga Barrister na biye da shi a baya. Hajiya na zaune kasan center carpet Siyama ta dora kanta saman cinyar Hajiya ta lumshe ido kamar mai bachi, alhalin ba bachin take ba tsabagen ciwo kaina ya saka ta a gaba da damuwar rashin Baby Namra.
Barrister ne yai sallama Hajiya ta amsa mi shi tana kallon danta, ramarsa ta yanzu har ta fi ta dazun da jiya ga wani rashin kuzari da yake fama da shi, ko be fada mata ba ta san abunda ya kawo lauyansa a gidan, ta saurari duk wani abun da Gwarzo da Barrister suka fada mata da kuma yadda suka tsara shigar da karar, bata katsi hanzanrinsu ba har suka yi suka gama, bayan barrister yai mata sallama ta kalli Gwarzo tace.“Idan ka raka shi ka zo ina son magana da kai”
Ta okay ya amsa mata sannan ya mike tsaye suka fice tare da barrister. A harabar gidan ma sun kusan awa daya suna tattaunawa kamin yai masa sallama ya sake dawowa falon Hajiya ya zauna. Shiru shiru Hajiya bata ce masa komai ba tana da kallon plasma dake falon, har sai da ya kagara da kansa yai magana.
“Hajiya kin ce akwai maganar da kike son yi da ni?”
Juyowa tai a hankali ta kalli gefen da danta yake zaune a saman cushion.
“Zaka iya tuna lokacin da mahaifinku ya rasu?”
“Eh”
“Kana iya tuna silar mutuwarsa?”
“Ciwon suga ne”
“Matarka fa?”
“Hadarin mota ne”
“Miyasa ba kai karar likitan da ya duba mahaifinku ba a lokacin da ya rasu? Miyasa ba jai karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarka ba?”
Kallon rashin fahimta yai mata, why Hajiya zata bijiro masa da wannan maganar? Taya zai yi karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarsa? Taya zai yi karar likitan da ba shi ya kashe mahaifinsa ba?
“Fada min? Ko kuma ka fi son Baby Namra ne akan mahaifinka? Ko kuma ran Baby ya fi na Matarka daraja?”
“Ba... Ko... Daya...”
Ya amsa kamar ana matso maganar daga bakinsa.
“Then why zaka yi karar matar nan Gwarzo? Miyasa kake son dora mata laifi? Kana da wata hujja da ke nuna cewar ita ta kashe Baby Namra?”
Wani dogon numfashi ya ja ya sauke, sai a yanzu ya fahimci inda zancen Hajiya ya dosa.
“Saboda matar bata da mutunci ko kadan, kuma a yadda take da zafin zuciya zata iya aikatawa, kuma idan har bata aikata ba miyasa suke jin tsoro ita da iyayen?”
“Da zaka ji labarin matar nan da ka tausaya mata, kaddara ce ta fada mata kuma mahaifiyarta tai min rantsuwa....”
Saurin saukowa yai daga saman kujerar yana hade wani bakin abu daya tsaya masa a makoshi.
“Hajiya dan Allah? Bana son na ji duk wani abu da ya shafe ta, ba ina kokarin kai kararta ba ne saboda na danne mata hakki no hakki yata nake kokarin kwatowa?”
“Wace hujja kake da ita wacce ta nuna maka cewar matar nan ita ce ta kashe Baby? Haba Gwarzo ya kake neman zautuwa akan mutuwar da ba yau ta saba bakuntarka ba?”
Sakin baki yai da mamaki yana kallon Hajiya miyasa tai saurin canja har take kokarin hana shi bayan ita ma a da tana goyon bayan karar?
Siyama ce ta tashi zaune ta tana kallon Hajiya da mamaki.“Hajiya be kamata a kyale wannan maganar ba, taya zata kashe Baby kuma a barta?”
Hajiya ta daka mata matsawa.
YOU ARE READING
GOBE NA (My Future)
General FictionBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...