39

1.9K 255 79
                                    

Tun daga lokacin da Hajiya ta lura da halin da danta yake ciki bata sake yarda ta barshi ya zauna shi kadai ba indai yana gidan to yana falo tare da ita ko kuma yana harabar gidan suna fira, a ganinta sakewarsa zai taimaka masa fiye da kadaicewar da zai yi shi kadai yana tunani da saka kansa a damuwa.
  Kamar yadda ta saba masa after dinner suna zaune dinning ta dauko masa zancen aure domin shi ne abunda ta fi son taga yayi a yanzu ko zai rage masa damuwa har ma ya kawo masa farincikin samun wata haihuwar.

“Tun kwanan baya na maka magana akan aure kace zaka yi tunani ba ka ce min komai ba”

Ya kurba ruwan da ke gabansa kadan yana dan murmushi.

“Hajiya bana son zancen aure a yanzu”

“Saboda me? If saboda ni ne zaka iya zama a wajen gidan nan da matarka, and ba zan cilasta maka auren Ikilima ba, sai ka dauko budurwa da kake so ka aura”

“No ba wai Budurwa ko bazarawa ba, a halin yanzu mace bata gabana, ni ban ki na mutu a haka ba”

“Saboda me? Ni bana son ganin jikanka ne? Ku kadai Allah ya bani ai zan so ku yi aure ku yi juri'a da yawa ba kamar ni ba”

“Kawai ina ganin kamar idan na sake haihuwa rasata zan yi, ni kuma bana son abunda zai sake kasani a damuwa yanzu”

Hajiya ta yi murmushi.

“Baka da karfi zuciya sai kace ba namiji ba”

“Hajiya ba zaki san abunda nake ji ba, babu wanda zai shiga a irin halin da nake ciki a yanzu ace be samu kansa a damuwa ba”

“Yes dole na ka damu an sani ai, amman ka rika sassautawa rayuwarka, ita daman rayuwa tana tafe da kalubale kala kala, wani mai sauki wani mai wahala, sai dai duk halin da zaka shiha ka rika tunawa akwai wadanda suka fika shigarsa, idan arziki ne akwai wadanda suka fika, idan talauci ne da damuwa akwai wadanda suka wankeka suka shanye, kai mata kawai ka rasa sai ya kuma uba, akwai wata macen da na gani na ita tana da uwar a raye uba a raye dukan ya'yanta suna nan, amman kalubalen rayuwar da ta shiga ko kan akaifarta baka shiga ba, tun daga lokacin da na ji labarin matar nan abun ya tsaya min a rai”

“Indai har tana da kowa a raye mi zai saka ta a damuwa”

Har Hajiya ta bude baki ta fara labarta masa labarin Halimatu sai ga Siyama ta dauko fuskarta dauke da damuwa taja kujera ta zauna tana fadin.

“Ni kam i don't think zanje gaskiya”

Ahmad ya kalleta.

“Why? Saboda Baby bata nan? Mu da Hajiya za mu je kamar yadda muka saba a kowace shekara”

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya bar dinning table din ya nufi hanyar da zata fitar da shi daga falon zuwa part dinsa. Hajiya ta kalli yarta cikin kwarin guiwa tace.

“Idan ba mu karfafa masa ya manta da komai ba, taya za mu taimaka masa wajen tunawa da abunda zai tsaya masa arai, a kowa ce shekara shi yake bada kaso 50 a cikin dari na wannan wasa da ake na children day, 25% daga kamfaninsa ne, 25% daga makarantarsa ne, sauran al'umma da kamfanonu su dauki 50%, taya mutun zai yi wannan aiki kuma ya kasa halarta taron da yake talarta duk shekara, saboda kawai yarsa ta rasu sai yace ba zai je ba”

“Nifa ban ce kar yaje ba”

“Shi kike nuna masa mana saboda babu Baby Namra sai ya kasa jurewa ya nunawa duniya yana cikin damuwar rashinta har yanzu, ya kamata ki karfafi dan'uwanki shiga irin abubuwan nan zai rage masa damuwa, ko a lokacin dq Baby take raye wannan children game din yana cikin abunda tafi so fiye da komai a rayuwarta,to yanzu dan bata da rai kike tunanin mahaifinta ba zai je ba?”

“No Hajiya ina jin ba dadi ne, kusan every year tana cikin mutanen da suke bada award wa wadanda sukai nasara, kuma tana zaune tare da shi....”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now