Yadda kafarsa take taka kasa da karfi ya isa ya isar maka da cewar ransa a mugun bace yake, balle kuma kai arba da kyakkyawar fuskar nan tasa wacce ta koma kamar bakin hadari idanuwansa gaba daya sun gama canja kala daga fari zuwa ja. Wani irin nishi yake irin wanda bacin rai ya dannewa numfashi, gumi kawai ke karyo masa daman can haka yake idan ransa ya bace sai gumi da dannewar numfashi.
Tare da barrister suka isa gurin motar, sai ya kai hannunsa ya bude gidan baya inda aka saka Halima, hannunsa ya kai ya taba fuskarta zuwa hancinta dan tabbatarwa idan tana raye, tabbas yaji tana numfashi sai dai kana kallonta kasan bata cikin hayyacinta.“Wai hula suka saka mata”
Barrister Nuhu ya fada yana tsaye bayan Ahmad, dagowa Ahmad yai ya kalleshi da wata irin murya marar dadi saurari yace.
“Barrister ka shigar da karar matar nan da dan sandan da yai mata wannan abun, zan kaita asibiti yau yau nake son ka fara komai, ba zan iya yafewa ba, ba zan iya kyale wannan abun ba”
Yana fadar hakan ya zagaya zai shiga motarsa sai ga Inna da Husna sun iso.
“Mun gode Allah ya saka da alheri”
Be iya amsa su ba sai kawai yace.
“Asibiti zan kaita yanzu, asibitin Dr Nura za ku iya samun mu a can”
Yana fadar hakan ya bude motar ya shiga, yai mata key, kamin ya isa asibitin ya sake kiran wayar Halima duk da yasan bata hannunta amman yana son magana da Hafiza ne, akai sa'a wayar na hannunta domin ringing daya ta dauka.
“Hello, ke ce kanwar Lims ko?”
“Eh”
“A gabanki abun ya faru?”
“Eh komai a gabana akai, Mama ta hanani binsu ne can station din, baka ga wulakancin da sukai mata ba har waje suka fita da ita ba Hijab sai da na bita na saka mata mutane sai kallonta suke kamar ta yi sata, tun cikin gida ma yar sandar guda ta fara marinta”
Juyawa yai ya kalleshi Halima wacce idonta ke rufe sannan ya ce.
“Zan tura miki number wani barrister amman ki kira shi da line ki ba line Lims ba ki fada masa duk abunda ya faru zai shigar da kara akan case din”
“To ina ita Halima take?”
“Gata nan zan kaita asibiti”
Yana fadar hakan ya kashe wayar, ya sake waigawa ya kalli Halima, sai duk yaji tausayinta ya kara kamashi, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar, yana wani irin nishi kamar zai ciro zuciyarsa daga kirjinsa.
Yana kunna kai cikin asibitin wayarsa tai ringing kamar jiran kiran yake yai picking da sauri.“Barrister”
“Na'am Ranka yadade ina son na san cewar shin abunda ake zarginta da shi, bata aikata ba din gaske? Kuma bata da hannu a batan mutumen?”
“Bata da alaka da shi mutumen yana hannun DSS, bata da hannu a batan sa ko wata mu'amala da shi”
“To ya akalarka take da ita?”
Juyawa yai ya kalli Halima sannan ya amsa ma Barrister.
“Matata ce....!”
“Za a shigar da karar a madadinta ne ita kanta ko kuma....!”
Shiru yai for a moment, yasan dai kotu ba a mata wasa, kuma shi din be riga ya auri Halima ba, idan aka shigar da sunan shi din mijinta ne kotu ta gano babu auri a tsakaninsu zai iya kawo musu matsala, how he wish ace ya aureta, ya tabbatar da yau Hajiya ko Abdallah basu yarda ko yatsa sun daga sun nuna mata ba balle har su saka a kamata.
“A madadinta zaka shigar, mutanen nan sun wulakanta ta Barrister i want them to regret, su nemi yafiyarta da kansu kuma kotu ta yanke musu hukunci so that's su san ita ma din mai matarba ce, har marinta sai da yar sandar tai kanwarta ta fada min komai, zan tura mata number ka zata kiraka ta maka bayanin komai, an ji hular da suka saka mata ko criminal sai wanda ya kai kololuwa ake yi ma haka, it's just like plan sun tsara kasheta ne kawai Allah be basu sa'a ba”
ESTÁS LEYENDO
GOBE NA (My Future)
Ficción GeneralBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...