“Abun nan fa ya wuce iya abunda kike tunani, Wallahi mutanen nan ba za du yi karya ba, kuma ga zahiri kina gani, abubuwa sai kara kwabewa suke”
Aminu ne yake wannan maganar yana shafa kansa cikin tsananin damuwa, hannunsa na dama rike da takardar transfer.
“Iko sai Allah, ni wani abun yana bani mamaki Wallahi, taya za ka biye maganar bokaye? Tun farkon fari ma mi ya kai ka gurin ya saka tsinbo? Da har za su fada maka karya da gaskiya ka yarda”
“Hajiya ai dubiya yanzu babu wanda yake zaune, ba maza ba mata ba kowa kuma yadda lamurran nan suka fara lalacewa ai dole na saka a bincika min, ba ni kadai ba ko Alfa da ya kai ni sai da abun ya daure mata kai”
“Allah kadai ya san gaskiyar wannan lamarin wata kila ma gurin malaminta ka fada, ko kuma shi alfan yana goyon bayanta ne, shiyasa suka hada kai ai maka haka”
“Babu wani zancen goyon baya Hajiya fa a zahiri kike ganin komai sai lalacewa yake”
“Kai fa baka iya tashin hankali ba, kai yanzu dan Allah Aminu har ka kawo maganar dawowa da Halimatu a gidanka? Mace da bata kaunar uwarka bata son yan'uwanka? Ka duba ja ga har kazafi tai wa Sadi fa? Wallahi har a bada ba zan taba son Halimatu ba”
“Hajiya abunda ba ki sani ba, ko wane dan'adam yana da good side of him kuma bad side, Wallahi Hajiya ba dan ina son dawowo da Halimatu ba, acire zancen arziki, Hajiya Halimatu ta fi Murja hakurin zama da ni, Halima ko bata son abu bata nuna, sannan ko fada nai mata ko na ci zarafinta sai dai tai kuka ta ba ni hakuri, and tana kokarin ganin ta gujewa bachin raina, zan iya tafiya inda nake so nai iya adadin kwanakin da nake so na dawo bata ce min komai, amman ban isa nai ma Murja haka ba Wallahi Hajiya, idan na dawo tara na dare Wallahi sai Murja ta yi min fada, amman a lokacin da Halima take nan zai iya kai wa 1 na dare a waje kuma ba zata ce min komai ba, Murja ta bi ta saka min ido akan komai nawa, ba ni d sukunin daukar waya na latsa a cikin gidana idonta na kai”
Hajiya ta saki baki.
“Ban gane idan kai dare tai maka fada ba? Uwarka ce ita? Ita ta aje ka ko kai ka aje ta da zata maka fada? Ita ba mata ba ce da ba zaka mata magana ba”
“Hajiya ba za ki gane ba ne, idan ranta ya bace, jikina har rawa yake Wallahi”
“To acan gurin malaman da kaje ba su fada maka komai akanta ba?”
“Me za su fada min? Ni yanzu ba ta nata nake ba, ta Halimatu na ke domin sun fada min matukar ban mayar da ita ba, ba zan taba ganin komai daidai ba, kuma ga alama nan kina ganin bayan rage min mukami da akai yanzu an min transfer zuwa enugu, duka duka yaushe ne rabuwar mu? Idan aka kara dadewa kila ma bara zan koma, tun da sun ce ita ke da kashin arzikin duk abunda na samu saboda ina tare da ita ne, ni da farko ma na dauka ko sammu ne kai mi shiyasa ma har na biye ta Alfa ya kai ni gurin ashe ba asiri ba ne rabuwar da mu kai ce, Hajiya ki duba fa ki ga abun hawa ma neman gagara ta yake, motata na mata gyara uku abunda ban taba ba, yanzu na siye sabuwa ita ma engine dinta ya tsaya, sabuwar mota fa Hajiya Motar miliyan biyar ace engine dinta ya tsaya”
“Wai kana nufin ba da motar ka zo ba?”
“Wallahi Alfa ne ya sauke ni bakin gate, tun jiya motar ta tsaya tana can gurin ma su gyara”
“To abun nan fa d daure kai ni na fi zargin sammu gaskiya, asiri ne akai maka, ko ita ai zata iya maka asirin na ka lalace tun da ta ga ka sake ta, ko kuma abokan aiki ko makota”
“Hajiya Malami hudu msgana daya suke, babu wanda yace asiri ne, ni dai ki taimaka min ta dawo dan Allah”
“To ai ban ga ta inda zan iya taimaka maka ba, matar nan fa ma aure tai gidan wani take”
YOU ARE READING
GOBE NA (My Future)
General FictionBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...