Iyayena na gari abun alfahari idan kai dace da iyaye hakika ka yi babban dace, bayan su kuma sai miji shi ma idan kai dace da miji na gari ka samu ingantacciyar rayuwa idan Allah yai maka falala ka sake dace da yayana nagari ko kai an gama maka komai a rayuwarka. Al-hamdulillah ban san yanda tarbiyar yarana zata kasance ba bayan girmansu amman ina fatar su tashi akan tafarkin da na dora su akai, idan na samu haka ko da shi kadai zan iya gode Allah, duk kuwa da na san babbar jarabawar duniya ita ce ta rashin dacen miji.
Ban taba jin kewar budurci ba irin yau, ji nake kamar ace yau ni din budurwa ce da na sake zaben wani mijin ba Aminu ba, na kwana rungume da sakon wani a kirjina saboda rashin kulawar mijina, da ace na san rayuwa zata sauya min haka bayan aure da na zabi zama a budurcin har na bar duniyar nan, bachi be dauke ni da wuri ba, haka kuma ban dade ina bachin ba na farka, kaina har wani nauyi nake jin yana min ga wani uban ciwon zuciya da nake jinsa har cikin kashin bayana.After sallah nai addu'o'in da na saba sannan na nufi kitchen domin hada ma yarana abincin zuwa makaranta, misalin bakwai saura na safe ya shigo kitchen din rike da jakarsa sai ya tsaya a jikin kofa, ni kuma nai kamar ba san da mutum a gurin ba har sai da yai gyaran murya sannan na juyo na kalleshi
“Ina kwana?”
“Lafiya kalau, ga wannan ki rike da wuri zan tafi saboda bana son rana yai min”
Ya fada yana miko min dubu uku, kallon kudin nai na girgiza masa kai.
“Ka kara akwai kudin da za su ishemu har ka dawo”
Be ce min komai ba, ya aje kudin saman kitchen cabinet ya juya, a karon farko yau zai tafi wani gari amman na kasa ce masa Allah ya tsare sai binsa da nai da kallo. Juyowa yai ya kalleni.
“Da ki min addu'a da karki min duka uwarsu daya ubansu daya, sai abunda Allah ya rubuto zai same ni, mugun nufinki ya koma kanki”
Yana fadar hakan ya juya ya fice, ni kuma nai murmushi ina jin bakar maganar da ya fada min har cikin raina. Kaina na daga ina kallon kitchen din yadda tsarin gidanmu yake da siffar masu arziki ko kyautar rabin miliyan nai ba za ayi mamaki ba saboda ana ganin mai arzikin nake aure, amman yau zai yi tafiya saboda bakar keta irin nasa ya dauki dubu uku ya bani.
Dauke kai nai domin na san idan na ce zan cigaba da tunani zan iya faduwa a gurin ko kuma wani abun ya same ni.Bakwai da rabi na shiga na tashi yarana nai musu wanka sukai alwala sukai sallah sannan na shirya su cikin uniform dinsu na makarantar boko ban da Namra da har yanzu bachi take jikinta kuma da dan zafi. Kasa suka sauko suka karya tare da Amal sannan na shiga dakina na saka hijab na fito na saka su gaba muka nufi gate. Sai dai mun yi sa'ar haduwa da mijin Hajara kamar jiya.
“Ina Namra yau?”
“Bata jindadi”
“Subhanallahi Allah ya sauwake”
“Amin”
Sai ya saka yaran a motarsa har da Amal suka tafi, daman ta saba idan yan kwarai suna kanta tana yarda ta bisu su tafi idan ya dawo sai ya kaita gurin Hajara.
Juyowa nai na dawo cikin gidan, sai na shiga dakina nai wanka ina cikin shiryawa wayarta tai ringing, dauka nai na duba sai ga number Abdulhamid hakan yasa ni picking na kara a kunne.“Hello”
“Good morning Halima ya gida ya yaran?”
“Lafiya kalau”
“Na miki sako ta whatsapp wai baki hau ba so i decided na kira ki”
“Lafiya dai?”
“Account number dinki na k so dan Allah zan dan saka miki wani a ciki”
Dauke wayar nai daga kunnena na duba dan kara tabbatarwa idab Abdulhamid din ne, ganin shi ne yasa na maida wayar a kunne na ce.
“Abdallah yace ka saka min?”
YOU ARE READING
GOBE NA (My Future)
General FictionBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...