Na yi mamakin ganin kawata Sa'adatu tana jirana a farkon shiga falona, ko wa nuna mata gidana ma oho ni har na manta da ita a cikin duniyar nan. Tun kam Abdulhamid ya faka motarsa ta mike tsaye tana ta kallon motarmu. Har ya faka motar ya bude ya fita be ce mim komai ba kamar yadda nima ban ce masa ba tun bayan shigowa a motar.
Irin kallon nan da ta saba na yan bariki ta fara yi min kamin ta mikawa Abdulhamid shi tare da gaisuwa. Shi kuma ya amsa mata da fuskarsa ta rashin sakewa da mutane, ma'ana ba yabo ba fallasa ba kamar Aminu ba da idan ya ganta bakinsa har rawa yake wajen amsa mata gaisuwa.“Wa nake ganin kamar Sa'adatu?”
“Ba kamar ba ce ni dince, tun da kin yadani ni ai na nemo ki”
Na yi dariya kamar yadda ita ma tai tana bin Abdulhamid da kallo har ya shige falon sannan ta kalleni.
“Shine angon na mu?”
“Eh shine”
Sai ta tabe baki har da wani lumshe ido ta bude.
“No wonder ake mana rowarsa, ashe kyakkyawa ne mai naira, gaskiya Halima kina dacen auren maza masu kyau da kudi, ko da yake kina da kyau ne shiyasa, da ni ke da kyaunki da yanzu na ci kudi”
‘Yes ina dacen aure a gidan hutun amman ba dan na hutu ba, sai dan na fuskanci wani kabulen’
Na fada a raina a fili kuma sai nai dariya na ce.
“A takaice dai mijina ya burge ki, gashi kuma shi ba kamar Aminu ba ne balle ku kulla”
Kallon rashin fahimta tai min tana yar dariya kamar ta ji kunya.
“Ban gane ba?”
“To ya za'ayi ki gane kuwa? Ke dai zo muje ciki”
Ina gaba tana biye da ni a baya har muka shiga falo. A kujerar da ke kusada kofar ta zauna ta zubawa Abdulhamid ido ni kuma na nufi two seater da yake zaune yana lasa waya na zauna a kusa shi, kamar wanda wani abun ki ya zauna kusa da shi haka yai saurin tashi ya nufi dakinsa, iyakar kokarin da nai na danne damuwar da na ji ne dan kar Sa'adatu ta zargi wani abu. Na tashi na shiga kitchen na dauko mata ruwa da lemun mu na hausa na kawo mata. Sai gashi ya sauko ko inda nake be kalla ba ya nufi kofa ya fice a uzurce.
“Halimatu wane irin zama kike da mijinki?”
Kamar daga sama na ji tambayar Sa'adatu tana mire baki.
“Kamar ya?”
“Ato kin san ni bakina baya shiru, na ga kamar akwai yar matsala a tsakaninku ko kuma shi haka rayuwarsa take?”
“Wai Sa'adatu sakin fuska yasa raini ya shiga tsakaninmu har ta kai kike iya fada min duk abunda ya zo bakin kina mu'amulantata yadda kika ga dama”
Sakin baki tai ganin kamar na taso mata da fada.
“Haba Hajiya ta, makano ne kawai zai shigo gidan nan yace be fahimci akwai rashin jituwa tsakaninki da mijinki ba, kuma wanda ya damu da kai ne ya damu da matsalar ne kawai yake nuna maka damuwarsa, kalle ki Halima Wallahi har kin fi auki a gidan Aminu dama da nan”
“Zuciyarki bata raya miki ko bana da lafiya ba? Babu abunda ya zo kanki sai rashin Jituwa?”
“Hmm yanzu dai Allah ya baki hakuri, mu bar wannan maganar, ya yaranmu ya su Amal?”
“Suna lafiya”
Na amsa mata ina kara hade fuska tare da dauke kai. Shiru ya shiga tsakaninmu kamin ta sake dauko wata maganar.
“Amman wai Halimatu ba kya kewar yayanki? Na ga Aminu ma da ke damu da yaya ba, yanzu yana ta shiga damuwar rashinku balle ke da kike tare da su kullum”
YOU ARE READING
GOBE NA (My Future)
General FictionBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...