Labarin GOBE NA ba labari irin wanda na saba yi ba, shiyasa tun kamin na fara sakinsa na fada muku cewar rayuwar aure ce mai cike da kalubale, idan ba ku manta ba inkiyar labarin ZAWARCIN HALIMATU, labari ne na rayuwar kala kala ta gidan aure da zawarci, da kuma rikon yara da kula da tarbiyarsu, zancen dan Allah Candy kar ayi kaza ko ki canja kaza be taso ba, matukar ana son labarin ya tafi a yadda aka tsara kuma a isar da sakon da ake son isarwa.
GOBE NA ba labarine na zallar soyayya ba, yana tafe ne da kalubalen na rayuwa, duk irin halin da Halimatu take ciki ko zata kasance a ciki akwai mata da yawa da suka dade da shiga cikin wannan halin, ko suka fita shiga matsala ma. Wallahi a three weeks ago akwai wacce ta kirani tana kuka tana fada min abunda akai wa Namra a labarin haka akai wa yarta kuma har yau babu wanda ya sani mijinta ya hanata magana, secondly mijinta kamar Aminu yake, a lokacin da ta ba ni labarin mijinta sai da kaina ya daure Wallahi. So akwai mata da yawa da suke fuskantar rayuwar gida aure kala kala, ko da ba mu tabo duka ba ya kamata ace muna taba wani bangaren na rayuwarmu ta yau da kullum ai.
Labarin zai tafi a yadda na tsara shi ga wanda yaji zai iya bi fine.
*** *** ***
“Aa Gwarzo wace uwar ce zata jefar da yarta haka nan kawai? Ka taba ganin bolar yaya?”
Momy ta fada bayan ta zauna tana kallon Namra.
“Oh Momy ba ki ji inda na samo ta ba, uwarta na son ta zata jefar da ita”
“Idan ma haka ne ai ba laifi uwar ba ne, na uban ne akan me zaka bar yarinya na tsawon lokaci ba ka neme su ba? Taya ma zaka bar ma mace dawainiyar yara bayan ba da su ta zo ba?”
“Ita na fa uwar da laifinta”
“Baka san abunda ya fito da ita daga gidan mijin ba, ba duk mace ce bata son yaranta ba ni ban yarda akwai mace da bata son yaranta ba, wata kila ma hankalinta yana can tashe”
“Ko dai zan maida ita sai gobe sai jikinsu ya fada musu, ko goben ma sai da maraice”
Ya fada yana shafa kan Namra.
“Yarinya kyakkyawa suna son wufintar da ita”
Momy ta yi murmushi.
“Ya sunanki?”
“Namra”
Ta amsa hankalinta kwance kamar ta san su.
“Allah sarki Baby Namra kin samu takwara”
Baby Namra dai bata komai ba sai wani shigewa take jikin Momy.
“Sai gobe zan bada cigiyarta a radio idan sun ga dama su zo nan su dauke ta”
Ya fada yana mikewa tsaye. Sai ita Namra ta mike tsaye zata bi shi.
“Zauna nan Momy zata kula da ke”
Momy ta mika mata hannu tana murmushi.
“Zo nan jikata yar albarka”
Ba musu taje ta zauna saman kujerar sai Momy ta dorata a kafafuwanta.
“Ajikin nawa?”
“Uku”
“Wace makaranta kike?”
“Gwarzo International school”
Momy ta yi dariya, Ahmad ma da ke kokarin fita juyowa yai ya kalleta.
“Wow i feel it tun farko na ji kamar ina da alaka da ita, ashe yarinya yar makarantar mu ce shiyasa take da natsuwa”
Ya fada yana wani miskilin murmushi. Momy dai ta girgiza kai tana kwantar da Namra a ciyarta.
YOU ARE READING
GOBE NA (My Future)
General FictionBabu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni...