chapter 25

304 8 4
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg26.

Mikewa yayi yashiga ya watsa ruwa itako Summayyah tanarigingine a kan gadon bayan ya fito ya sauya wasu kayayyakin bayan ya kammala ya kalleta yace.,,Kitashi kije ki dan watsaruwa ko.,,
Tai wani fari da ido tana kallonsa tace.,, nikam bazan iya tashiba don jikina ba kwari yanzun,  ko zaka daukenine ka kaini toilet? .,,
Aiko jikinsa narawa ya sabata ya kaita toilet din.
A gogonsa ya daura a tsintsiyar hannunshi yana dubawa tamkar me neman wani abu .
Ba jimawa ta fito. Ta kimtsa tareda shigan kananun kaya ta dubeshi ta kashe mai ido daya aranta ko murna takeyi tasameshi a hannu.
Mikewa tayi daga gaban mirror tana gyara rigarta kana ta riko hannunsa. ,, kaga babyna ka tashi muje parlour ko.,,
Ya mike suka wuto parlour. Aisha ko tun data kammala cin abincinta ta wuto parlour ta zauna tana jiransa ya fito ya bata maganinta kamar yadda ya saba mata shuru shuru taji sai kuma bacci ya kwasheta.
Nan suka sameta tana bacci  Summayyah takai hannu ta daka mata duka .,, ke dallah tashi.,,
Ta daka mata tsawa bashiri ko tamike ta zauna .  Summayyah  ta jefa mata harara..,, toh ai sai ki tashi ki koma  daki kibarni nida miji na .,,
Aisha takai dubanta ga Anwar amma tamkar bejin  abinda sukeyi. Nan ko haushi ya kamata ta kuma duban Anwar din tace.,, kace mata karta kara dukana.,,
Anwar yace.,, toh base ki tashi ba ko bata isa tace dake ki tashi bane?.,,
Jinhaka Aisha tai kwafa ta cakumo wuyan Summayyah takai bakinta saitin kumatunta ta rangada mata cizo wanda da   kyar Anwar ya jawota daga jikin Summayyah.
Summayyah tai baya baya zata fadi hannunta  rike da kuncin nata tana faman kurma ihu.
Ta shafo kuncin taduba ganin ji yasata sake kurma wani ihun.,, wallahi bazan yaddaba mahaukaciya   yar dangin mayu.
Anwar ya riketa suka wuce daki yai mata dressing.
Tana huci da kyar  Anwar ya lallabeta ta kwanta.
Aisha ko dakinta  ta  koma ta kwanta.
Da washe gari tanata jira ko zata gansa yazo tada ita sallah amma shuru duk da ba sallan zatayi ba.
Ganin shuru bezoba ta tashi ta fito parlour   taje kitchen ta tadda mairo nata kicikicin kirki.
Mairo taduka  ta gaidata.
Sai kuma tace.,, hajiya me kikeso ne?.,,
Aisha ta bata .,, yunwa   nakeji.,,
Tafada tana bude wasu kuloli datagani anjerasu a guri daya ta fara budewa wani tagani anyi Pepe soup din kan kifi ta saka hanu ta gutsira zata kai baki. Mairo tai saurin dakatar da ita.,, hajiya Suayyah tace ayi mata , dan Allah karki taba danta gargadeni.,,
Ko sauraranta batayiba ta cigaba dacin abinta harda daukan kulan ta koma diningT ta zauna sai da tamaidasu 'kaya tas tukuna ta dire kulan ta jawo goran Swan ta sha harda getsa kana ta dire.
Summayyah ta fito daga daki kumatunta yasha bandage kanta ko ba bako dankwali ta shiga kitchen ta dubi Mairo . Tace.,, keh ina aikin dana saka ki? ,,
Mairo ta nuna mata .,, gasu nan.,,
Ta duka tafara budewa sai kuma ta mike ta dau hannu ta sharara ma Mairo mari tace.,, ina pepe soup din kifin dana ce kimin? .,,
Mairo rike da kuncinta tana share hawaye tace.,, hajiya nayi miki sai kuma hajiya uwargida tace in bata...,,
Bata ida ba Summayyah ta kara daga hannu takai mata lafiyayyar mari

,,keh!  Wacece kike kira da uwargida?,  toh bari in gaya miki nice uwar gidan ba wancen mahaukaciyar ba,  kuma wallahi na sakejin kin kira wata da uwargida a gidannan bani ba toh a bakin aikinki! .,,
Mairo jiki na rawa tace.,, hajiya insha Allahu hakan ma baze sake faruwa ba.
,, sai ai kimin wani kamin mijina ya fito.,,
Jiki na rawa  Mairo ta amsa. Summayya taja tsaki tabar kitchen din.
saida tazo daidai   zata shiga dakin Anwar sai kuma ta fara kuka.
Da sauri ya dubeta yace.,, lafiya Summy , meya faru? .,,
Ta goge idonta daya ciko da kukan munafirci tace .,, kawai nasa Mairo tai maka pepe soup din kan kifi shins Aisha ta cinye harda zagina wai yunwa ya kawoni gidanka harra zagin mahaifina wai meshan taba.,,
Ran Anwar iyayi dubu to ya baci sam  beso ko kadan yaga ran Summyn sa yana baci ya maida ita tamkar gold..
Yana huci ya mike ya nufi dining din nan be sameta ba sai ya wuto dakin ta , da karfi ya bude kofar daida tana sanye da towel tana shrin shiga wanka.
Bata ma san da shigowarsa ba ta bayan kunninta ya dauke ta da mari wanda saida dakin ya bada sauti.
Ta fadi kasa ta fara kuka. Ya kuma kai kafansa  ya shureta ta bugi bayanta da bakin gado ta fara saka ihu tana rike cikinta , saboda tsaban zafinda cikinta yake mata ta kasa koda nunfashi kwakkwara illa hawaye da suke biyo daya bayan daya. Jijiyoyin kansa suka dago idonsa yai jajur yana hucci.
Ya zaro belt ya fara dukanta da gurin karfen sai da yayi ya gaji tukuna ya barta a gurin  a sume.
Summayya ko dadi tamkar ya kasheta ta latda waya ta kira haj.ladidi ta  zayyana mata kome. Sannan ta ajiye ta shiga dakin ta sameta tai jina jina. Sannan ta koma dakin Anwar ta samesa ya dafa kansa ta dafa kafadarsa tace.,,    haba   babyna me kuma yake damunka mifa tuni na manta da abinda mahaukaciyar matarka   takemin,  kaga  dago mucigaba da soyayyar  mu.
Sai ya dago  jajayen ida nuwansa ya sakin mata murmushi kana yace.,, Summy taya hankalina ze kwanta bayan naki a tashe yake,  wallahi naso in babballata,   ni wallahi yanzun na tsaneta kwata kwata tamkar in saketa dan ni babu abinda ya taba shiga tsakanina da ita sai in sake ta ta tafi can.,,
Summayya taji tamkar ansama  tuwan sanyi a jikinta dandadi . cikin kisisina tace.,, haba babyna baza ayi haka ba amma why not ka kori mai aikinka sai ita ta maye makwafinta?    Ko kuma ka barta ita Mairon ta ruka girki kawai inyaso Aisha sai ta dunga sauran aiyukan.,,
Ya jinjina kai.,, toh shike nan haka za'ayi,  yanzun ki tashi kije ki fada ma Mairon Daga gobe sai Aishan ta fara.,,
Sai kuma ta bata rai, ya dubeta.,,  mena kuma bata rai ?.,,
Tace.,, kaman ya gobe!,  gasky daga yau zefi.,,
,, toh ai shikenan    wannan   ba wani abun damuwa bane  abinda kikace haka za'ayi...

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now