**Matar Bature**
**Written by**
**R.S.Balarabe**Pg22
Daki tashiga ta dudduba ko zata ganshi, ta nemi bakin gado ta zauna kasantuwar taji motsi a bayi.
Ba jimawa ya fito tareda towel yana goge hannunsa.
Idanunsa a kifa mata a ransa yana mamakin ganinta duk da daman yasan zatazo.bece da ita komeba ya dauko sallaya sannan ya kabbara sallah yana idarwa yadaga hannu sama yana addu'a sannan ya sauke.
Ummice dake parlour da ta gaji da jira ta kwala ma Aisha kira.
Ta amsa Ummi tace. ,, Aisha baki ganshi bane?.,,
Cikin irin maganarta tace.,, na ganshi mana, toh base ki tafi ba.,,
Bude baki Ummi tayi dan maganan tata ta bata dariya sosai.
Hara ra Anwar ya watsa mata.,, daman kina tare da Ummi shine kikayi shugowar ki kuma baki sanar dani ba?.,,
Ya karasa maganan damikewa ya fice daga dakin daman yana kule da ita na rungumar Ahmed da tayi abin ya tsaya masa a rai matuka.
Bayan sun gaisa da Umi sukayi sallama ta koma gida wani wawan hamma ya saki yana shafa cikinsa yunwa yakeji sosai hakan yasa ya kwala ma Aisha kira da gudu kuwa tazo ta haye kan kujera.
Wani kalan razana yayi daya kalli fuskarta datasha eye shadow da janbaki.
,,what!, ke me haka?.,,
Ta kumburo baki.,, kawalliya nayi.,,
,,kwalliya kuma sai kace aljana? .,,
Ta kuma takuma turo bakin tace.,, toh ba Ummi bace tace in runkayin ma kwalliyaba saboda kar wancen yar iskar ta aure ka.,,
Anwar be ce da ita kpmeba illa jinjina kai dayi dan ba karamin razanasa tayi ba sai can kuma yace.,, kin iya girki?,, .
Ta zaro idanu .,, girki kuma? Cabb!! Ai baba baya barina innayi ma kona hannu nakeyi kuma kowa cewa takeyi ba dadi saide babane kade yake cewa yayi dadi shima nasan karya yakeyi.,,
Maganarta ta nabasa dariya amma yunwar da take addabarda tahana sa murmusawa.
Kitchen ya shige ya bude store ya ciro taliyar yara guda uku sannan ya dafa bayan ya kammala ya zuba a plate biyu yafuto da shi ya dire a diningT sannan ya bude freezer ya ciro executive daya tareda cups biyu .
Saida ya zauna ya faraci tukuna ya kirata. bayan sun gama ci yatashi ya dauko maganinta tsiyaya ruwa yayi a cup, tanaganin yayi haka ta bata rai.
Ya hada rai sosai sannan yakai maganin bakinta, ganin ya murtuke fuska yasa bashiri ta bude baki ta hadiyesu da ruwan daya mika mata.
Tana gama sha taja kujeran kefe ta fara kokarin rera masa kuka.
Zuba ido yayi yana kallonta dadai lokacin wayarsa ta dau ruri.
Sunan momine radau a screen din wayar gabansa yai mugun faduwa .Dakyar ya daga yana sallama. Ta amsa a dakile sannan tace.,, Anwar!! Anjima daddynku ze kiraka yarambayi amincewarka na auran Summayah ina so kafadamasa ka amince kuma bakaso auren ya dauki lokaci, kafada masa kai ka bukaci daka aure ta kuma kana son ayi airen ne nan da sati biyu!,wallahi! Wallahi inhar baka aiwatar da abinda na uumarceka ba wallahi! Saina tsine maka albarka!!!,,.
Tana kainan ta katse wayar.
Zufame zafi ya fara kwararo masa, mikewa yayi ya wuce dakinsa yasamu guri ya zuna sannan ya hada kai da gwiwowinsa, sam baze iya cewa kome ke damunsa ba.
Wayarsa ce ta dau ruri duk da be san ko waye me kiran ba amma hakan be hana gabansa mungun faduwa ba dan a tunaninsa Daddy ne
Hannunsa na rawa ya daga wayar sai kuma yaji muryan Ahmed bayan sun gaisa yake fada masa yana gate din gidansa yazo domin suyi sallama.
Suka gama ya katse wayar.
Ba jimawa sai gashi yashigo yai sallama.
Anwar najin sallamansa yai hanzarin futowa dan kar Aisha ta kara kokarin rungumansa.
Ahmed yace.,,wato dr.da kansa yana guduwa daga asibiti, patients kuma suyi mene.,,
Anwar be tankasa ba, juyawan da zeyi yaga Aisha na kici kicin jan akwati.
Ya daka mata tsawa ba shiri taja ta tsaya yace.,, ina kuma zaki?.,,
Tace.,, zanbi yaya Bature ne mu koma gida.,,
Ya wurgo mata harara.
Nan ta kifar da akwatin tana ahirin rera kuka yatsanta a baki tanayi tana shure kafafu.
Ahmed na ganin haka ya mike sukayi sallama dan gobe da safe ze kama hanyar komawa Kaduna.
Kuka takeyi sosai, har beson yajuya ya kalleta dan ba karamin tausaya mata yakeyiba.
Tashi yayi dakyar ya koma dakin sa har bayan sati daya yanata jiran kiran Daddy amma shiru har ya fara tunanin ko momi naso ta firgitasa ne kawai .
Ranan Monday ya tashi ya kimtsa sare yana shirin tafiya office dan yana jin jikinsa sarai , wata motace ta shigo harabar gidan dadai yana kokarin bude murfin motarsa lura dayayi motar Daddy ce yasa ya maida murfin motar ya rufe .
Bayan motar tayi packing yaje ya bude ma Daddy kofa sannan yafiyo sukayi musabaha kana suna shiga cikin gida fuskar Daddy sam ba annuri hakan ya kara karfin buguwan zuciyar Anwar. Bayan Daddy ya zauna Anwar sai ya zauna a kasa gefen Daddy.
Parlour'n ya dauki tsawon mintuna bama zaka iya cewa da mutane a ciki ba, sai da Daddy yaja wani nunfashi tareda gyara muryansa tukuna yace.,, Anwar naji wani magana mara dadi wanda ni bansan kwakwalwar ka da hankalinka zasu iya maradin abinba balle suke zasu kasance da abin, zaka kara aure kuma ba kowa ba illa yarinyar da ta gama raba mutuncinta da darajanta a duniya! , ina so yanzun ka tabnatarmin kana sonta kuma kanason aurenta.,,
Daidai lokacin Anwar yaji makoshinsa ta kakare da kyar ya iya hadiye yawu. Ya dan jima yana nazarin maganan Daddy amma tunawa da furucin Momi besan sadda bakinsa ya fara magana ba.
Cikin rawar murya yace.,, Eh! Hakane Daddy ina sonta kuma da aure, sannan Daddy bana son auren ya wuce nanda sati biyu.,,
Tunda ya fara maganan Daddy ke mamakinsa amma jin ya tabbatar da hakan yasa Daddy ya jinjina kai yace.,, okk shikenan.,,
Yana gama fadin haka yamike yai ficewarsa .
Ko motsi Anwar ya kasa kansa a duke ga wani matsanan ciyar ciwon kai dake addabansa, saurin dafe kansa yayi jiyayi tamkar ana buga masa guduma a kan ga zuciyarsa dake mugun bugawa a hankali yake furta.
,,Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!,,.
Ya maimaita haka har so biyu kana yakuma fadin .,, Allahumma ajirni fi musi bati waklifli khairan minha!,,
Haka ranan ya wuni da zazzabi ko asibitin be iya zuwa ba.A bangaren mama kuwa tunda Ahmed ya dawo ya sanar masu da halin da akeciki hankalinta ya tashi
Cikin kuka tace.,, nikam tunda baze iya rike mana itaba ya saketa kawai kuma ma banda wani wulakancin harda kara aure kuma babu wanda besan yarinyar daze aura ba natsats tsiya bace, nikam Alhaju jabarnu inje in taho da ita kwai ai bace masu akayi mun gaji da itabane , wallahi koda ace zata mutu bamr auranta ni me riketane har karshen rayuwata, haba Alhaji sekace bata da gata.,,
Baba ya katseta da cewa.,, haba wani irin magana kike jikikayi ance besonta kobe kula da ita?, aurw fa kawai akace ze kara ni banga abindamuwa ba kuma ai akwai addu'a insha Allahu Allah ze tsareta daga dukkan masu sharri.
YOU ARE READING
Matar Bature
Romans" Mama wannan ma baba nane". Ta shafo sajen shi. "Hmmm! mama kyakkyawane,amma mama bake kika haife wannan ba turawa suka siya miki koh?" mama tayi dariya tace" eyye . lallema Aisha. toh sai ki daga minshi tunda da kudi na siya koh, karki ballashi...