Chapter 8

419 19 1
                                    

    **Matar Bature**
       ** Written by**
       R.S.Balarabe.

   P9

Yau Aka daura Auren Ahmed da Saudat, biki kam yayi armashi , sun gabatar   da duk events din da suka shirya da wasu  al'adun nasu.  gabanin ranar Su Abdul da  Ahmed tare duka  suka tafi Adamawa ana washe garin da  za'a daura auren, mama taso ta biyo su amma Alh.musa ya hana gani cewa zasu kawo amarya nan inyaso su kuma ranar sai ya kasance ranar da zasuyi bikin su. Mama de bataso ba amma hakanan ta hakura.
Ranar ko Ahmed sanye yake da farar shadda kansa dauke da  white din hula da kuma black takalmi,shi mai matukan son fararen kaya ne gashi kuma ba karamin kyau shigar suke mai ba. Wani irin walkiya yake sajen nan nasa yasha gyara sai sheki shima yake.
Ankow sukayi da Anwar sai de shi anwar din an masa aikin rigarsa da bakin zane bayan na  Ahmed fari. Baka iya banban cesu kamar yan biyu kamanninsu ya wuce tsammani sai banban cinsu shine Ahmed yana da fadi anma bashida jiki akasin Anwar akwai fadin da kuma dan jiki amma mai kyau da kuma fasali,sai kuma fara'a dayake dashi wanda Ahmed sam bai ma cika magana balle dariya. 'Yan uwa kuma aminai!'.
  
Saudat kuwa leshine take  sanye dashi blue tsadaddene sai kuma head da akayi mata dauri dashi sky blue, tasha make-up idon ta inka kalla Zakayi tsammanin anyi mata karin eyelashes  don cika da tsawo, na lashes din, Tayi kyau sosai in banda tashin kamshi ba abinda take.
Sunsha hotuna amma fa da kyar ta iya tsayawa sukayi hoton don sai da Anwar yaje ya dauko ta tukuna. don Macece mai alkunya.
Ranar kam ta kasance ma Ahmed rana ta tarihin da baze taba mantawa ba.
hakama bayan an daura auren suka kwaso amarya da wasu  iyyayensu su uku wato inna jummai da gwaggo hassatu wanda sune  kannen Ummi sai inna maryam ita ma kanwar Alh.madun ne. Sannan kuma kawayenta.
Saudat kam tasha nasiha gun ummi. kuka kam kamar Zata bar duniya don da kyar aka iya shawo kanta.
Misalin karfe tara na dare suka isa Kaduna motoci hudu suka cika dayake harda Anwar suka taho daman akwai wasu patients dinsa da zai ma aiki. Hakan yasa yaga gwara ya biyo su.

Gidan ko haka ya cika da yan uwa da abokan arziki.
  Shigarsu gidan keda wuya sai tashin gud'a .

Su Ahmed  duk a waje suka tsaya saboda ba dadewa zasuyiba za a  tafi gidan Amarya.

Ranar kam wuni Aisha tayi tana kuka da kyar mama ta shawo kanta  sannan  ta bata kayan da zata sa shima fa ansha  fama.

Tana cikin daki lokacin da taji shigowar su  kara gyara fuskar ta tayi wai ita amaryace. Dakin Ahmed ta shiga wanda a nanne aka aje kayan drinks hakan ya bata dama ta samu turarensa wanda yake shafawa dan kadan ya rage ganin haka yasa ya dako sabo ya tafi da shi,  raguwan ko ta feffesa don sedataji ko isska be fita tukunna ta aje,jikinta tamkar tayi wanka da turare  don karfinsa .

Cema Abu tayi ta duba ta gani tsakanin su waye ya fi kyau.
Falo ta wuce mutane ta gani masu kama da Baturen ta.
kana   arba da ita kasan tasha kuka ta koshi daidai fuskar saudat ta zuguna sannan ta daga mayafinta tayi wanda in banda tashin kamshi ba  abinda yake , kukan itama taga tanayi. Ganin cewa ita ma kukan take gashi bata biyo kyau din da take tsammanin ganiba don ita a tsammaninta duk kyawun su ze zama daya ne da Baturen ta,saide hancinsu iri dayane duk da yadan fita kasantuwar nashi yadan fi tudu. Hancinta ta dan shafo, daga ido saudut tayi suka hada ido ,harara Aisha ta wurga mata wanda babu wanda  ya lura da hakan.
Saukar da ido saudat tayi daga dan kallon da tayi  ma  Aisha kasa fahimtar ko wacce ittadin.
Mikewa Aisha tayi ta zauna kusa da mama wanda itta ma ba karamin haduwa tayiba nasihar itama  take mata.
   Bayan sun gabatar da sallolinsu suka  cicci abincin
Rike hannun  saudat din mama tayi suka shiga bangaren baba shima nasihan yayi mata.

Daukan waya tayi ta kira Ahmed ba jimawa ya shigo,baba ya hadasu yana masu nasiha mai ratsa jiki. Mama ma a nan tayi masu masihar tata Ahmed kuwa sai a lokacin yatuna da irin nauyin daya hau kansa.

Aisha kuwa dataji maganan zuwa gidan Amarya bata wani bata lokaciba ta kwashi ta kallmanta da yar tsanan ta wanda ako dayaushe take tare da ita.
Ganin su Anwar tayi da Yaya Abdul , kallon Anwar ta tsayayi, idonta kamar tana mata gizo don Ahmed kawai take gani a gurin sai dai kuma yanda taga yana dariya hakan ya tabbatar mata da cewa bashi bane , can kuma ta tuna da mutumin da ta taba ganin Ahmed yana VCall. Da shi.

Matar BatureWhere stories live. Discover now