**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.P12
"Aisha!". Anwar ya furta can cikin kasan makoshinshi,rawa jikinsa ya fara yi ganin yadda ta canza kamanni gabaki daya, ga kuma wani kumburi a fuskarta,
Gabaki daya ta canza daga kamanninta.
Kusa da ita ya nufa, tana ganinsa ta kara kurma wani ihun wanda zakayi zatan namanta ake yankawa ana soyawa.
Dr.Hafis ya dan riketa sannan yace," haba kanwata kiyi shiri, kinga ba wani zafi yake dashi ba".
Ya fada yana nuna mata alluran dake hannunsa.
Tunkude shi tayi da karfita, sam in ba dadun ka kalli raunu kan jikinta ba bazaka taba cewa wani abu ya sameta ba don yadda take motsinta,
bakinta sam baya rufuwa." ni wallahi karka kara tabani so kake in samu ciki ko!".
Tafada tareda goge hannunnata wanda dr.Hafiz din ya taba a da zanin gadon.Rungume hannayenta tayi a kirjinta.
furucin da tayi ya ba Anwar dariya sosai, yasan mama ce ta fada mata hakan.
ganin yadda take motsits-tsikan ta hakan yasa damuwansa akan halinda take ciki yadan ragu.Kallon Anwar din ta sake yi cinkin tara tsi tace," lah!, yaya Anwar, harda kai".
Da kyar de suka samu suka mata alluran kashe zafi.
Ko cire alluran be gamayiba taji bata jin dan zugin da kafar yake mata.
Gani yadda suke mata da kafar tata yasa ta fara kwarma masu ihu duk da ba wai jin zafin take ba,zagi ko Anwar kam ya shasu duk da jikinta yamutu anma sam bakin na nan.To cikin sa'a suka mata sannan suka komadda ita dakin da take.
Anwar be zaya bata lokaciba ya koma gida ranshi fal, ba kowa a parlourn da alama duk sun fita, dakin mama ya wuce kai tsaye cikin murna.
mama tayi mamakin ganinsa a haka ganin ba yarda ya fita ba,
jinjina kai mama tayi sannan tace," ka dawo, kullum in kuka dawo daga aiki sai inga kamar zaku zomin da Aishata ne, ga maganinta nan,yau kusan kwana uku kenan ba Aisha ba labarinta,.innajin yarinyar a raina wallahi daidai da kwana daya ban taba jin tsanarta a zuciyata ba, kaga anwar naso in haifi mace amma Allah be yiba.
Allah ya jikan mahaifiyarki Aisha,kema gashi sun dauke minke..".
Maganar takeyi cikin kuka,
Gaba daya sai Anwar yaji jikinsa yayi sanyi , shi tsoran karya gaya mata ya gantada irin halin da take ciki.Can de yai ta maza ya fada mata kome harda aikin kafan daya yi mata.
Kuka ta kara saka mai,
" toh me sukayi mata,tashi muje inga yàta inb hakaba hankalina baze taba kwanciya ba".Dauko hijabinta tayi a wardrobe ta saka sannan suka fita tare dakin baba ta wuce.
Shima ta sanar mishi. Yai murna sosai ,tare suka tafi asibitin.
Da shigarsu dakin, sai hankalinsu ya tashi mama tace," mezan gani haka suwa suka yi maki wannan abu haka, Alh. Kalli jikin yarinyar nan".
Tafada tana kallon Alh.musan wanda shima hankalinsha na gurin Aishan ne , gabaki daya sun firgita.
Cikin rawar murya Alh. Musa yace," hatsari tayi?".
Gidakai Anwar din yayi saboda shima abinda dr.Hafiz din ya fada mashi kenan.
sun sameta tana cin abinci wanda ladidi ce ke bata a baki.Tana ganinsu ta hade rai tareda juyadda kanta kefe guda.
Mama tana ganin tayi haka ta fahimci ciwon tane yake kokarin tashi, sam kobi takan ladidi basuyiba.
Matsawa kusa da Aishan tayi sannan tace," mene Aisha su waye sukayi miki haka?".Ko juyowa batayiba balle suyi tsammanin amsa daga gareta.
" Alhaji ka gani wallahi ciwonta ya tashi,shikenan".
" toh kin zo mata damaga nin nata kuwa!"Alh.musa yatambaya.
"A'a namantasai dai in a kira umar sai ya kawo mana".
Tafada tana kokarin sharce wasu hawaye.
Waya baba ya daga ya kira umar din ya sanar masa da kome ya kuma umarceshi daya dauko maganin da kuma asibitin da suke.
Alh.musa ne ya lura da ladidi wacce ke zaune a kujera. Yace," baiwar Allah sannu,kina ta faman dawainiya ,saide bamu shaidekiba".
Ladidi ta amsada "eh Alh.Mukhtar ne ya aikoni da in zauna da ita harta samu lafiya da zun nan ma yashigo asibitin,sai de ba rabon ku hadu dashine don be dade da fita ba.
Jinjina kai yadan yi a ranshi yana nazari akan mutumin.
YOU ARE READING
Matar Bature
Romance" Mama wannan ma baba nane". Ta shafo sajen shi. "Hmmm! mama kyakkyawane,amma mama bake kika haife wannan ba turawa suka siya miki koh?" mama tayi dariya tace" eyye . lallema Aisha. toh sai ki daga minshi tunda da kudi na siya koh, karki ballashi...