**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**Pg28
.....bazan taba ha'intarki ba, Saudat inaso ki kasance mai fahimta da natsuwa akan abinda zan fada miki...
Na fito daga bank zan dawo gida nayi dare sosai,ina cikin tafiya bayan na tsaya nayi mana shopping na danyi gaba kadan na hadu da wata yarinya,kasantuwar ganinta ita kade kuma mace gakuma ga dukkan alamu ba Zata wuce 18yrs ba nai parking domin in rage mata hanya, nace ta shigo muje batayi musu ba kuwa tashigo muka soma tafiya,jin bata fadamin inda zata ba yasa na tambaye ta nace mata.,, baiwar Allah ina zan kaiki.,,
Ga mamakina sai naga ta yi fari da idanu tace.,, ba matsala ko wani hotel ka gadaman kai ni.,,
Cikin mamaki nace .,,Hotel kuma ?,,
,,Eh, hotel ya naga ka razana ko kai baka saba da hotel bane, ko da yake irin ku sai a gida koh.,,
Ba shiri naja nayi packing a gefe domin in ajiyeta. Nayi tafita ta ki dana tursasata sai tace zatayi min ihum barawo .
Jin haka sai nace mata.,, okk shi ke nan muje hotel din.,,
Bayan muje na kama mana daki. Mun shiga sai nake ce mata na manta da wallet dina a moto har na kai bakin kofa sai naji an riko ni , na juyo tace.,, gasky ban yarda da kai ba, kaban numbern ka in ba haka ba baxaka fita ba sai mun gama abinda ya kawo mu.
Ganin bani da choice sai na bata.
A haka na samu na wuto gida..
Kirannan kuma dakika dauka, bayan faruwan abinne da kwana biyu . da washe gari takirani tana shedamin na yaudareta da sauran su sai na bata hakuri nai mata kuma alkhawarin haduwarmu hakan yasa takirani sai kika dauka har take fadamiki tajini shuru gashi kuma ta kama mana hotel .
Naje hotel din muka hadu nace mata zan zagaya da ita, ban taba zatan ba musulmace ba sai da muka je wani restaurant muna cin abinci spoon din ta yai kokarin fadi sai tace.,,Jesus,,.
Hakan ya tabbatar min da cewa ba musulma bace duk da shigarta irinta musulmai ga harsheta tanajin hausa sosai.
Bayan mun gama cin abinci ta dube ni tace.,, nayi mamaki daka tsaya duk da duk wanda ya ganka yaga kamili mai natsuwa sai kuma naga ba haka ba hakan ya tuna sardani cewa akwai fuska biyu.,,
Nai murmushin nace.,, amma meyasa kikace haka? .,,
Tace.,, saboda ni tunda aka hai feni ban taba haduwa da natsatstse mutum ba koda na ganka daga nesa sai nai tunanin kanada kirki sai kuma dagabaya nai tuna dacewa ni ba me sa'a bace kuma ni bazan taba haduwa da mutumin arziki ba tun daga mahaifina har zuwa ranan da zan mutu.,,
Ta goge wani kwalla da yake kokarin futowa daga idanunta.
Cikin mamaki da maganganun ta nace.,, amma meyasa kiketa fadan haka.,,
Tace.,, labarina me tsawo ne , abin katsanta mummuna , mahaifina shiyasani a harkan karuwanci...,,
Tafada tana rufe bakinta ayayinda kuka ke kokarin kubuce mata.
Jin haka nasan daman da dalili hakan yasa na dunga mata wasu tambayoyi cikin dubara har ta fara bani labarin ta kamar haka.
Tace.,, mahaifiyata bafullatana ce musulma, kakana wato mahaifin mamana sun gudo daga karkarane kasantuwar fada da akeyi tsakanin manoma da makiyaya suka taho cikin gari Kaduna. Hakan yasa mahaifiyata take tallan nono da fura a kasuwaKamar yadda mahaifiyata ta taba ban labari ta saba da ta fito za'a saye tas. Watarana ta hadu da wanimutum yazo a mashin yace mata shi maginine dan haka ta biyo shi don taga gurin da mahaifiyata taki sai kuma daga baya ta amince . haka sukata tafiya har dare tayi basu bar tafiya ba ,ya kaita wani kauye nan ya ajiyeta , ya maida ita tamkar matarsa kuma shi ba musulmi bane.har aka haifeni' alokacin mahaifiyata ta gane cewa mahaifina dan fashi da makamine bayan na girma sosai inada shekara goma shabiyu alokacin mahaifiyata ta rasu sakamakon ciwon kansa , tabarni dagani sai mahaifina a daki guda muke kwana, rasuwanta yasa muka runka zuwa church da mahaifina har na juya na zama Christian.
Wata rana mahaifina yashawu yayi tatul nan ya afkamin daga nan sai na maye makwafin mahaifiya ta.
Har na saba sai kuma aka kashe shi yanzun shekaranshi daya kenan da mutuwa hakan yasa na dawo nan cikin gari naci gaba da harkan barikancin da mahaifina ya bamin gadonsa.....,,
Tana kai nan kuka ya kubce mata sai da tayi mai isarta tukuna tai shuru.
Ni kuwa daurewa nayi dan labarin nata ya taba min zuciya alokacin nai shuru nai nazarin cewa zan iya mata nasiha har ta koma musulunci tunda karamar yarinya ce.
Najima ina nazari kana nace.,, amma me yasa ba zaki koma musulunci ba?.,,
Tai saurin girgiza ka tace.,, bazan koma ba saboda musul mai basu da tausayi , tun da nake karuwanci bayan mahaifina ban tabayi da wani Christian ba sai musulmi dan haka babu anfanin musulunta ta ga addinin da basu da adalci.
Najinjina kaina nace.,, shi kuma mahaifinnaki fah.,,
Sai tai shuru .
Nacigaba da cewa.,, adalcin ne yasa yayi miki haka?.,,
Tace. ,,Ah'ah, amma ni a ganina duk dayane saboda duk abu daya suke aikatawa.,,
Na girgiza kai nace mata.,, ba daya bane tabbas akwai bata gari a cikin both musulmi da Christian amma hakan ba yana nufin duk musulmi haka suke ba, inaso ki fahimta yanzun ba mahai fiyarki musulma bace?, itadin ba tagari bace?, hakan ze sheda miki a kwai na gari akwai bata gari.,,
Ta dukar da kanta tana kallon yan yatsunta kamar tana nazarin wani abun.
,, me yasa bazaki tuba ba ki musulunta?.,,
Tai saurin girgixa kai.,, taya zan musulunta bayan inada tarin zunubi ?.,,
Nai mrmushi nace.,, a lokacin da kika musulunta Allah ze kankare miki zunubin ki bakida maraba da jaririn da akahaifa yau koda zaki musulunta a yanzun ki mutu to tabbas Aljannace makomarki. Amma fa dasharadin in zaki musulunta ne don Allah kuma ba zaki kara komawa zuwa rauyar ki ta baya ba.,,
Nan ta amince zata musulunta, nan take na musuluntar da ita na kama mata gida na kuma sata a islamiya.,,Yana kainan yayi ajiyan nun fashi wanda atare suka yi da Saudat wanda tausayinta ya cika mata zuciya da tausayin mijin nata..
Nan ta sauko daga gadon ta duka kan gwiwarta hannunta rungume da Safiyat cikin kuka tace.,, mijina kayi hakuri tabbas na kasance me rashin adalci a gareka me zato da zargi a gare, dan Allah ka yafemin.,,
Ta karasa tana kuka me tsanani, ya sauko kasa ya zauna yana fuskan tarta yasa hannu ya share hawayenta.,, Saudat na yafe maki bakimin kome ba, nine da banmiki bayani ba amma Saudat ina rokon alfarma daya a gurinki please Saudat...*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.
YOU ARE READING
Matar Bature
Romance" Mama wannan ma baba nane". Ta shafo sajen shi. "Hmmm! mama kyakkyawane,amma mama bake kika haife wannan ba turawa suka siya miki koh?" mama tayi dariya tace" eyye . lallema Aisha. toh sai ki daga minshi tunda da kudi na siya koh, karki ballashi...