**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**Pg31
Kamar yadda Ammi tace haka ko akayi sukaje asibiti aka duba Aisha nan doctor yake sanar mata da matsalan kwakwalwarta yayin da yace.
,,gsky hajiya lamarin ma yazo da sauki,zamu iya bata magunguna taci gaba dasha amma gaskiya bamuda maganin da zamu bata wanda zesa ta warke gabaki daya!, sai dai in zaku jarraba Fita zuwa India shima bazance maku baze yuwu ta iya warke wa ba saboda babu abinda yafi karfin ubangiji.,,
Ammi ta sauke ajiyar yar nun fashi tanajin tausayin ta sosai a ranta domin ta matukar shiga ranta wanda batajin a yanzun zata iya rabuwa da ita.
Juyo da kallon ta tayi ga doctor'n tace.,, dr. ko nawa zan kashe domin inga ta warke zan kashe! .,,
Dr. Yace.,, okk shikenan zamu fara processing , za'a kashe kaman 6 million.
Ammi tajinjina kai.,, koda yafi haka zan kashe! .,,
Tana gama fadan haka ta mike tare da ruko hannun Aisha.
Bayan sun shiga mota suka koma gida.
A parlour suka zauna ta daga waya ta kira Zayyid.
Ba jima sai gashi yafuto sanye da farar jallabiya ya daura rawani wanda yafuto dashi sak balarabe.
Ammi na ganin sa ta hade rai , ya zauna daga cikin kujerun, ya dan jima da zama Ammi batace dashi kome ba hakan yasa yace.
,, Ammi gani.,,
Ta wurgo mai harara kamin tace.,, Zayyid ban hanaka wannan shigarba? Zayyid kafita idona wato saboda ka bata min rai ko.,,
Sam shi ya manta ta hanashi hakan yasa ya mike ya sauya zuwa black shadda, bayan ya zauna ya kura ma bayan tafin hannun sa ido.
Ammi ta dubeshi tace.
,,i think nan da next week mai zuwa zamu je India ni da my new baby, so daman tun yanzun nakeso in gargade ka, Zayyid karka kuskura kace zaka Saudiya, wallahi Zayyid kayi min haka Allah ya isa ban yafe ba.!,,
Da jajayen idanunsa wanda suka rune zuwa ja ya dago ya dubi Ammi.
Cikin rawar murya yace.,, Ammi, gurin mahaifina fa nake zuwa! Toh Ammi kinsan bakyason su me yasa kika aure shi....? .,,
Beyi aune ba yaji saukan mari wanda ba ze iya irga marin dayake sha duk lokacin da magana irin haka ta taso ba.
Jikinta na rawa tace.,, Zayyid ni kake duban idona kake fadin min haka! SaiKa zaba koni ko mahaifinnaka.,,
Tana gama fadin haka ta wuce sashenta.
Ji yake zuciyarsa na tafar fasa barin ma idonsa in yakai kan Aisha sai yaji tsanarta ta kara karuwa a zuci yarsa.
Yaja tsaki kana ya koma dakin sa...Mama ce zaune a dakin Baba, ta dubi baba tace.,, Alh. Niko inaso inyi waya da Aisha amma amma kuma inajin tsoron kar in kirata in tada mata hankali.,,
Baba na shan lemu sai daya kammala kana yace.,, gaskiya ki hakura kin santa da rigima koma kin kira kila Anwar din be gida .,,
Mama ta jinjina amma a zahiri hankalinta atashe yake don kusan kullum sai tayi mafarkinta......Summayya ce zaune da ita da aminiyar ta Salima su kitsa su kwance.
Kofar parlour din aka fara knocking.
Summayyah taja tsaki kana ta kwala ma mairo kiraA hanzar ce ta zo jikin ta na rawa.
ta duka Sumy tace.,, duba waye ne yazo min gida da tsakar rana.,,
Taje ta bude kofa hakan yaba Mufidat daman shugowa.
Sumy ta daka ma mairo tsawa tana bin Mufidat da harara.
Ta kuma kai kallon ta ga Mairo tace.,, matso nan.,,
Jikin mairo na rawa ta isa gabanta ta duka kana Sumy ta wanketa da mari.
,, bace maki nayi duk wanda yazo sai kin sanar dani ba,in ya isa ince ya shugo in bai isa ba ya koma.,,
Hannun mairo a kuncin ta tace.,, hakane hajiya kiyi hakuri hakan baze kara faruwa ba .
,, wuce ki bani guri! .,,
Jiki na rawa mairo ta bar parlour'n tana goge kwalla.
Sumy takai duban ta ga Mufidat wanda mamaki yagama kasheta zama ma ta kasayi.
Sumy tace.,, Mufidat ba gai suwa , zuwa da rana tsaka, gaskiya ki koma in yamma tayi sai ki iya zuwa.,,
Ran Mufidat in yayi dubu to ya baci.
Tace.,, keh !, wacece ke har da zaki hanani zuwa gidan dan uwa na? .,,
Sumy ta mike tsaye tareda kama kugu tana girgiza tace.,, ni a matar sa mana, ni banga abin tada hankali a nan ba tunda ba gidan ubanki bane!.,,
Mufidat tai kwafa.,, Eh!, naji ba gidan ubana bane gwamma ni innada gidan uban kuma gidan uban nawa ya taka nan kayan alatu, wata fa ba gidan uban balle kayan alatun.
Sumy ta dafe kirji.,, cabb!, ni kike wa gori? .,,
Mufidat taja tsaki kana tabar gidan.
Nan Sumy tazauna a kasa tamkar yar bori, tun Salima na bata hakuri har ta zuba mata ido can data gaji ta yayimi gyalenta
Tace.,,uhm kinga tafiyata Summayyah mayi waya.,,
Tana gama fadan haka ta fuce.
Da daddare bayan Anwar ya dawo ta zayyane masa kome harda kari wai Mufidat ta zage babanta da mahaifiyarta takuma cemata shegiya wai bata da uba.
Hakan yasa Anwar ya kudiri aniyan zuwa gidanta.
Haka ko akayi da washe gari ya wuce gidanta ya tarar a kulle hakan yasa ya tafi gidansu.
Ransa a bace yashiga gidan direct dakin Momi ya nufa aiko ya sameta tana zaune a bakin gado.
Ya wanke ta da lafiyar yar mari yana bam bami.
Wanda sanda ta tuna ranan da ya mareta tun suna kananan yara.
Tafashe da kuka Momi dake toillet tafito jin hayaniya yasa ta fito ta tarar suna musayar baki.
Momi ta dubi Anwar tace.,, mekuma ya faru naganka da sassafe haka kuma me ya hadaka da Mufidat?.,,
Saida yagama huci kana yace.,, momi taje gidana taci mutuncin Summayyah wai Sumayyah shegiya ce bata da uba.,,
Momi ta bude baki ta juya ga kallon Mufidat.,, Mifidat bakida hankali ne, ba kamar yaya take a gurin ki ba ?.,,
Mufidat na kuka tace.,, wallahi ba haka bane Momi itace ...,,
Bata ida ba momi ta dakatar da ita da tsawa.
Tace .,, yimin Shuru!, daga yau karki kara zuwa gidansa inba kin kirata kin nemi izinin ta ba, kuma kada in karajin magana makamancin wannan sannan kuma ki dunga yi mata biyayya.,,*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.
YOU ARE READING
Matar Bature
Romance" Mama wannan ma baba nane". Ta shafo sajen shi. "Hmmm! mama kyakkyawane,amma mama bake kika haife wannan ba turawa suka siya miki koh?" mama tayi dariya tace" eyye . lallema Aisha. toh sai ki daga minshi tunda da kudi na siya koh, karki ballashi...