**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarbe.P10
Revers sukayi sannan suka fita daga harabar gidan,a tsaye suka bar Ahmed wanda ke kallon yarda suke kokarin fita daga gidan.
Shiru sukai dukkansu bame magana, sai Aisha da keta faman ture hannun Anwar wanda ya daura akan gurin daura hannu dake tsakanin kujeran.
Kallon yarinyar yake ta gefen ido wanda har yanzun ya kasa gane wace iriyar yarinya ce
tunda yake betaba ganin irinta ba.
Yaso ya tambayi Ahmed Amma sai ya fasa.
Hularsa ya cire ya daura kan Dashboard ,sannan ya dan shafo kwantarciya sumarsa
Jawo hulan tayi ta daura akan yar tsanarta, ta dan lankwasa shi wanda yaba hular daman canzawa daga shape dinsa.
Kallon hular yayi wanda ya rigada ya canza fasali tamkar ba sabuwa ba.
Cigaba da tukinsa yayi tamkar besan da mutum a gefensa ba.Barcine yake shirin awon gaba da ita. Yar tsanarta ta jawo ta kara rungumeta a kirjinta,sannan ta dan langwabe kanta akan kujeran Anwar.
Daidai sun shawo kwana wacce zata sadasu da kofar gidan wata mota ta dallo hasken futular motar sannan yadanyi hon ya wuce hannu mutumin ya daga ma Anwar.
Sauran motocinne suka biyo bayansu hon yayi a daidai lokacin da suka kunno kai izuwa gaban gate din gidan.Daya daga cikin mutanen office dinsu Ahmed wanda ake kira da khalid, ya fito daga motarsa wanda sunne daga baya.
Kwankwasa gilas din motar yayi sannan Anwar ya sauke ta.Khalid dinne yace," toh, zamu barku daganan tunda ga motocin mu a waje".
" toh mungode". Anwar ya fada tareda kai mishi hannu sukai musa baha.
Khalid yace ," a gaishe da Hajiyan".
Anwar ya Amsa da inshaAllah".
Sannan ya zuge gilas din.
Baba Ado ya bude masu gate suka shiga ciki.
Har yayi parking bata tashi ba.
Duk suka shige ciki suka barsu tunani yake yanda ze tasheta don shiyarasa gane kansa jiyake tamkar yana tsoran yarinyar.
Idanunsa yakai kan hularsa wanda ya kasaganewa tamka hular roba don ta yakune.
Rikota yayi sannan ya daura ta a kafadarsa.
Wani abu ya gani wanda ya dan basa mamaki jini yagani akan kujeran, sai a lokacin ya lura da danshin dayake ji a hannusa.
Duk sai ya rasa yadda zeyi da ita.Sallaya ya dauko dayake booth sai ya dan daura a hannusa wanda yadan rufe jikinta.
Ya rufe motar da key sannan ya shiga ciki.
Mama ya sama a kan kujera sanye da rigar bacci.Dubansu tayi tace," najiku shirune, tayi baccine?,ko abinci kirki yau bata ciba ,amma ta bik,zoka shinfideta nan don dakin can a cikeyake har dakin bakinma , kaga nima saide in kwana a nan".
Kan three sitter ya ajiyeta
Tadan lura da dan jinin daya bata masa rigarsa, sai a lokacin ta tunda da bata sa mata audigaba.
Bata de cemasa komeba harya kai dakin Abdul sai ya tuna da akwatinsa wanda ya barta a mota.
Dakin yadan karasa, Abdul kuwa tuni yayi barcin,toilet ya fada sannan ya tube farar malunmalun wanda shi kadaine ya baci.Dukunkuna ta yayi,yama rasa yadda zeyi da ita "oh my God!".
Ya furata a fili.
Ya gama abinda zeyi yafita tareda malunmalun din da niyar in gobe tayi sai ya hada da motar yakai gurin wanki.
Mota ya koma ya ciro kayansa yamaida ya rufe, koda ya dawo sai be samesu a parlour'n ba.
Key yasa ma kofar ya sauya kayansa izuwa wata bakar jallabiya sannan ya kwanta.
Tunani yarinyar ya kamashi a ranshi yana mamaki na irin jikin yarinyar.
Sai yanzunne ya tuna da hularsa wanda ya fadi kafin su shiga gidan.
Murmushi yayi tare da fadin " you are so funny my little...",
my little what ?". Ya tambayi kansa wanda sam da farko bema san me yake furtawa ba, ji yake tamkar ba shiba."Wife?". Ya dan fada a fili.
Murza sumarsa yayi kamar me susa sannan ya furzar da iska.Addu'ar bacci yayi sannan ya gyara kwanciyar sa izuwa hannun damansa.
***
YOU ARE READING
Matar Bature
Romance" Mama wannan ma baba nane". Ta shafo sajen shi. "Hmmm! mama kyakkyawane,amma mama bake kika haife wannan ba turawa suka siya miki koh?" mama tayi dariya tace" eyye . lallema Aisha. toh sai ki daga minshi tunda da kudi na siya koh, karki ballashi...