✍🏻✍🏻✍🏻 *SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* ✍🏻✍🏻
Na
Hauwa'u Salisu (Haupha)
🌟6Stars Indeed
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
~Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai.
~
~Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad sallahu alaihi Wasallam.
~*Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne idan wani ko wata yaga abin da ya zo daidai da shi to akasi ne.*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga dukkan masoyan Hauwa'u Salisu (Haupha) a duk inda suke a faɗin duniyar nan._Page 1
"Lantai don mai garinku ki maza ki fito daga cikin ɗakin nan ki wuce makaranta, kafin masifaffen Yayanki Hafizu ya zo ya kama min mitar na hanaki zuwa makaranta."
Wata dattijuwa ce ke maganar tana kallon ɗakin dake kallonta.
Sai da ga alama wadda ake kiran ko a jikinta, domin ko alamar fitowa bata yi ba daga ɗakin duk da cewar dattijuwar ta jima tana mata magana.Sai da dattijuwar ta ce, "Yawwa Hafizu gara daka shigo ai yanzu ta fito ta wuce tunda ni ta rainani ai."
Kamar an jehota wata yarinya da bazata wuce shekaru takwas ba tai fitar burgu daga ɗakin tana cewa, "Inna Kande sai na dawo, kuma na iske ana zane ƴan makara na rantse dawowa zan ba malamin da zai dakeni."
Kallonta tayi dattijuwar tana cewa, "Ho ja'ira da ban ce haka ba, baki fitowa daga ɗakin nan daman nasan ai."
Lantai tunda ta fito da gudu bata zame ko ina ba sai makarantarsu, ko da ta je ta hango ana taran latti, aikuwa ta juya da gudun tsiya da zummar komawa inda ta fito.
Karaf Malam Muntasir ya hango ta, yasa yara yace su tabbatar sun kamota.Ai sai aka fara ƴar tsere tsakanin Lantai da masu kamata.
Sai da suka ci gudu iyakar gudu sannan suka iso gidansu Lantai domin kwana ta dinga shiga tana yawo da su har dai ta gaji ta kama hanyar gidansu duk suna biye da ita.
Tana zuwa ta tsallake Inna Kande ta afka ɗaki tana cewa, "Inna Kande ki takanki wallahi suka kamaki ba ruwana kinga nima da ƙyar na sha."
Ta faɗa ɗaki ta rufe garam !Inna Kande da tsabar tashin hankali yasa ta kasa tashi tsaye da rarrafe ta samu ta isa bayan darnin makewayensu ta ɓoye tana nishin tsorata, ga duk ta gurje guyawunta gun rarrafe.
Su kuwa yaran da aka tura kama Lantai sun cirko-cirko a ƙofar gidan, don sun san indai Inna Kande ta kama mutum akan jikarta Lantai sai ya ji jiki, domin bata duka bata zagi illa mintsinin mutum kawai da ranƙwashi a kai har sai yayi kuka.
Sannan idan Yayan Hafiz na nan ba ƙaramin duka yake haɗa ku yayi maku ba harda Lantai ɗin.
Wannan yasa yaran su kai tsaye ƙofar gidan cirko-cirko an rasa wanda zai shiga ya kamo Lantai a cikin gidan.Sun san kuma ko dawa suke yawo ba zasu koma makaranta babu Lantai ba, Malam Muntasir ba zai ƙyalesu ba, sai ya dake su.
Inna Kande ta lafe sai kiran sunan Allah take tana ƙarawa,domin ƙauyen nasu ya lalace ko da yaushe ƴan daban dake maƙwabtaka da su suna shigowa su yi masu ɓarna su fice babu mai iya tanka masu domin duk ƙauraye ne, addu'ar da take Allah Ya sa basu bane Lantai ta jawo faɗa ba, idan kuwa su ne tabbas yau kashin kowa ya bushe a ƙauyen ga shi Yayanta Hafizu na maraya (Birni).
YOU ARE READING
SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)
Fantasylabarin wata yarinya ce wadda babu abin da take so a rayuwarta irin taga marubuci Nasimat, ansha bata kyautuka tana maidawa akan marubucin tasha kwana da yunwa akan tunanin hanyar da zata gano marubucin ƙarshe wani malaminta ya cika mata burinta ind...