✍🏻✍🏻✍🏻 *SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* ✍🏻✍🏻
Na
Hauwa'u Salisu (Haupha)
🌟6Stars Indeed
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un !*
*Ina miƙa saƙon ta'aziyyar rasuwar da akai ma MARYAM ABDULLAHI (Maman Yusuf ) marubuciyar Jami'in ɗan sanda.*
*Allah Ya jiƙansu ya gafarta masu yasa sun huta.*
**Tabbas an yi maku babban rashi, sai dai mu taru mu da ku mu bisu da addu'ar Allah yasa can ya fi masu nan.*
*Allah Ya baku haƙurin rashin da kukai My Sisi* 😭Page 15
Inna Kande ta ce, "Yo me zata siyo fa, banda taje yawo kawai ? Ai ina ga dai Aljanar nan ce mai tukku bisa kan Lantai, don yawonta yayi yawa Allah."
Lantai ganin Inna Kande ta sako wani labarin wanda ya kautar da tambayar da Barbushe yayi mata sai ta biye ma Inna Kanden tana cewa, "Amma dai ai kin san ni ina zuwa Maraya don duk sanda Yaya Hafiz zai saimun sabuwar rigar kanti tare muke tafiya ana ban wadda tai min."
Wasa-wasa sai da su Barbushe da Malam Muntasir suka jima gidan suna ta fira, wanda duk Lantai ta matsu su tafi domin yau za gaske zata fara karanta masu labarin INA DA HUJJA amma tunda Malam Muntasir ya dawo ta fasa zata ce ya koya masu littafinta na BARI WA BIBA ai na larabci ne sun ƙaru, ita kuma tunda yanzu ta gama haddace duk wata kalma ta cikin littafin sai ta ajiye shi ta fara karanta DORON MAGE tasan shi ma zai mugun daɗi kamar yadda wannan INA DA HUJJA yayi fitinan nen daɗi.
Malam Muntasir sai kallonta yake yana aiyana abin da take tunawa a ransa, tabbas Nuratu nada wayau tare da kafiya Uwa Uba naci ga abin da ta ce sai tayi ko ta samu.
Barbushe ya miƙe su kai bankwana ya kwashi yaransa yana ma Nuratu sai da safe.
Ta dubi Malam Muntasir ta dube shi ta ce, "Gobe zan bika farauta Yayana ka jira ni don Allah."
"Kai ƙanwata gaskiya ki zauna gida mu dawo baki iya wannan wahalar ."
Diddira ƙafa ta fara yi alamar za tai borin data saba yi idan aka hanata yin abin da taga dama.
Sanin tunda ta furta zata je sai ta je yasa yayi sallama da su ya tafi.
Ta dallawa Musa harara so take kawai Malam Muntasir ya bar gidan ta dirar masa da masifa.
Shi kuma ya ƙi tafiya ne kada ta iske shi gida da Barbushe ya shiga tara, sarai yasan haushinsa take ji don haka dole ya samo labari wanda zai faranta mata rai kafin su haɗu, so yake Malam Muntasir ya tashi tafiya su tafi tare, don haka yake zaune ya ƙi tafiya.
Ita kuma gani take tamkar idan ya tafi Malam Muntasir ɗin zai tafi shima, har ga Allah ta gaji da zaman da yake masu a gida ya hanata rawar gaban hantsi.
"Tabbas duk Musa ne ya ja mata wannan masifar, amma zata je farauta gobe don Musa ne, so take ta samo abin da zai dinga firgita shi yana ba shi tsoro ta zo da shi daga dajin.
Ai tunda yayi mata munafurci sai ta rama ta ruwan sanyi , ba zata bari ya sha a basilla ba ta rantse da Allah...
"Nuratu Allah yasa tunanin alheri kike yi yadda ki kai shirun nan akwai matsala fa." Cewar Malam Muntasir.Musa ya samu da ƙyar yace, "Lantai don Allah ki yi haƙuri naga sai hararata kike ban san abin da nayi maki ba."
Wata hararar ta watsa mai ta zumɓura baki ta shige ɗaki.
Malam Muntasir ya miƙe zai tafi yayi bankwana da Inna ya kwaɗama Lantai kira ya nufi ƙofar gida.
Tana jin kiran sai da gabanta ya faɗi, amma sanin waye Malam Muntasir yasa ta fito sai cin ɗaci take ta nufi ƙofar gidan, Musa kuwa ya bi bayanta kamar Kazar da ƙwai ya fashemawa a cikinta.
Lantai na isa inda yake tsaye, ya dubeta ya haɗe rai sosai yace, "Ranar da zan tafi garinmu da dare su wa kika tura gidana suka ɗauko maki Littafina ?
Lantai ta sadda kanta ƙasa, domin dai ƙarya ba halinta bane, ta fi iya haɗa sharri kan ƙarya don haka tai gum ta fara soshe-soshe kamar mai cutar kazwa.
Musa kam harda hanzarinsa ya shige gidansu bai jira komi ba ya cika jakarsa da kaya yace ma iyayensa zai je Maraya ana nemansu makaranta.Kafin ka ce me ? Musa yabar ƙauyen.
Tsawa ya daka mata, "Nuratu tambayarki nake su wa kika tura gidana suka sato maki Littafina ?"
Sai ta nemi fashewa da kuka.
"Malam kai haƙuri wane littafin wai ?
Daman kana karatun littafi ne ?"Kasa bata amsa yayi sai kawai ya miƙe ya nufi hanya ba ko waiwaye.
Lantai na ganin haka ta juya cikin gidan tana dariyar Malam Muntasir.
Yana zuwa gidan ya fito da sabon littafin jarumin nata wato NASIMAT ya fara karantawa yana jin takaicin yadda Nuratu ke son maida shi wani ƙaton ɗan ƙauye.
Inna Kande ta dubi Lantai, "Ki je gidansu Musa ki ce don Allah idan ya je Maraya yace ma Yayanki Hafizu ya zo ina son ganinsa."
Lantai ta zaburo kamar wadda cinnaka ya ciza ta ce, "Ke Inna Kande muna zaman-zamanmu za ki kira shi ya zo yasa ni a masifa, komi nayi ban kyauta ba."
Inna Kande ta rausayar da kanta ta ce, "Lantai gara ya zo don ga dukkan alama aljanu gareki, na gaji da abubuwan da suke yi, gara ya zo a kira malamai su yi maki karatu, kamar yadda Musa yace."
Ido waje take duban Inna Kanden, "Ai ho, daman Musa ne ya baki wannan shawarar Inna Kande ?"
Sai yanzu Inna Kande ta fahimci bata kyauta ba, data ambaci Musa a maganarta ba.
Lantai kuwa bata sake magana ba, ta jawo sabon littafinta DORON MAGE ta buɗe shafin farko ta fara karantawa.
A zuciyarta tana jin tabbas sai Musa ya ƙwammace kiɗi da karatu.
Dole Musa yasan yayi mata laifi kala biyu indai ta cika ita ce Lantan Inna Kande, Nuratu ƙanwar Barbushe da Hafiz .Haupha ✍️
*Please share.*
YOU ARE READING
SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)
Fantasylabarin wata yarinya ce wadda babu abin da take so a rayuwarta irin taga marubuci Nasimat, ansha bata kyautuka tana maidawa akan marubucin tasha kwana da yunwa akan tunanin hanyar da zata gano marubucin ƙarshe wani malaminta ya cika mata burinta ind...