SAI NAGA MARUBUCI NASIMAT p 23

3 1 0
                                    

Kawai bin ta ya yi bai san inda zata kai su ba, sai dai har a ƙasan ransa yana jin takaicin yadda bai ga wanda ya mare ta.

Lantai kuwa bata zame ko'ina ba sai inda ta ɗebo karara wadda ta zuba ma matar Maigari ta nuna mai tana murmushi tace, "Kaga wannan ganyen? To da shi zan rama abin da ya yi min wallahi ba zan yafe mai marin da ya yi min ba, kuma sai yasan ya mari Lanta a ƙauyen nan indai nice Lantai to kace na gaya maka sai na rama abin da su Garba su kai min... Tana maganar tana diɓar ganyen a leda ta ƙulle ta jawo hannunsa suka dawo kamar wani ƙaramin yaro haka Malam Muntasir ya biyo Lantai yana jin ta birge shi yadda tana mace take jajircewa idan aka cuce ta sai ta rama.

Har suka iso ƙofar gidansa ta zube shi tace, "Yawwa Malam ka shige gidanka Ni zan ruga namu gidan nasan yanzu Inna nacan na dubar hanyar komawa ta gidan kuma ban san Yaya Barbushe ya je ya iske ban nan zai faɗa ne." Duk a cikin maganarta ba abin da ya ɓata mai rai sai sunan Barbushe da ta kira kawai ya sosa mai rai, ya tsani shige mata da yaron ke yi ita kuma tana biye mai, sai kawai ya fasa shiga gidan ya kama hannunta ya ce, "Mu je na kai ki gidan kar da ki wuce gun shi."
Dariya tai ta wuce gaba ya biyo ta baya, ta tsinke da ba shi labari shi kadai jinta kawai yake amma sam bai fahimci me take cewa ba a labarin nata ba har suka isa gidan.

Inna Kande na zaune ta sha faɗanta an gaya mata an mari Lantai har fuskarta ta kumbura tace ba zata yadda ba, don idan tai sake sai a kashe mata yarinya haka kawai marainiyar Allah za a saka a gaba sai an ga bayanta don mugunta, sai ga Lantan ta shigo Malam Muntasir na biye da ita, da sauri ta kama Lantan tana duba fuskarta ai kuwa ta fashe da kuka ta rungume Lantan tana Jan Allah Ya isa ga duk wanda yai ma jikarta wannan marin sauya fuskar.

Malam Muntasir ya yi murmushi ya dubi Inna Kande dake fyace majina ya ce, "Ki daina kuka Inna don ta rama."
Inna Kande ta goge hawayenta tace, "Yaro na rasa abin da jikata ta tsare ma mutanen garin nan sun tsane ta."
Yaya Hafiz ne ya shigo da sallama riƙe da leda a hannunsa babba.

Kai tsaye suka gaisa da Malam Muntasir ya miƙa ma Lantai ledar ya ce, "Kayan makarantarki ne gobe za ki fara zuwa a huta da masifarki a ƙauyen nan."
Lantai tai tsalle ta dire ta yada ledar kayan makarantar tace, ita ta fasa zuwa kowace makaranta balle ta je gobe.

Yaya Hafiz ya fusata zai bugeta ta shige ɗaki ta rufe tana ihu kamar wadda aka buga.

Malam Muntasir yai ajiyar zuciya ya ji daɗin rashin kamata da Hafiz ɗin bai ba ya ce, "Kar ka damu ai an maidani can makarantar tasu don haka goben zan zo na tafi da ita, dama an kawo min sabon mashin ɗina saboda zuwa cikin garin kullum.

Yaya Hafiz ya washe baki saboda ya ji daɗin hakan, don yana tunanin yadda shiriritar Lantai zata bar ta kullum ta je tasha ta hau mota zuwa cikin garin Funtua makaranta dama.

Inna Kande tai bulum don ita ma zuwa makarantar Maraya ba wani daɗa ta da ƙasa tai ba, da dai ace Lantan na so ne za tai farin ciki amma tun da bata so ita ma bata so sam.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 30, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)Where stories live. Discover now