SAI NAGA MARUBUCI NASIMAT} P17to 22

15 4 2
                                    

[20/03, 8:00 PM] Haupha✍🏻: ✍🏻✍🏻✍🏻 *SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* ✍🏻✍🏻

           Na

Hauwa'u Salisu (Haupha)

  🌟6Stars Indeed

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

'''Jama'a ku shaida, wannan page baki ɗayansa sadaukarwa ne ga haziƙi kuma manazarci sannan marubuci wato ƙanina Muntasir Shehu marubucin littafin''' *KAZAR AMARCI da JARIRAI*

     Page 17

Inna Kande hankalinta tashe ta isa gun mai goro, sai dai yadda taga yana ta washe mata baki yasa ta ji sanyi a ranta, alamar Lantai ba sosai ta ɓata masa rai ba kenan.

"Sanusi don Allah kai haƙuri da halin Lantai wallahi ba da son raina take wannan iya shegen ba sam, ga goronka ko ɗaya ban ɗauka ba, amma naga ta ruga da wani sai ka gaya man ko na nawa ne na biyaka kuɗinka."

Sanusi mai goro sai lamarin ya ba shi mamaki don bai fahimci inda labarin nata ya dosa ba.

"To wai Kande ni na kasa gane kan maganarki ai, shin kin fasa siyen goron ne koko ?"

Inna Kande ta fiddo ido tana kallon Sanusi mai goro cike da mamaki wai Lantai siyen goron tayi to ina ta samo kuɗin da ta sayi goron ?"

Sanusi mai goro dai ya sauya fuska don yadda yayi ciniki bai jin zai amshi goron nan ya maida kuɗin, ko da Lantai ce kuwa zata maido shi.

Ita kuma Inna Kande sai mamaki take ina Lantai ta samu kuɗin da ta sai goro harda takalma guda uku ?
Baki alaikum ta juyo gida tana jimamin halin da Lantai ke ƙara jefa ta ciki.

Tana zaune tayi shiru lamarin Lantai duk ya ishe ta sai ga Innar Musa ta shigo gidan tana ta zabga sallama amma Inna Kande tana zaune bata san ana yi ba ma tsabar tayi zurfi da tunani.

"Inna Kande lafiya kike kuwa?" Cewar Innarsu Musa bayan  ta dafa ta a kafaɗa.

Firgigit ! Inna Kande tayi ta zabura kamar zata ruga sai kuma taga ashe Lantana ce Innar Musa.

"Lantana na rasa yadda zan da halin Lantai, ko da yaushe abin ta ƙara gaba yake, yau ban san wa ta amshe ma kuɗi ba sai gata da uban goro da takalma taki uku ta siyo ban san wa kuma ta takaita ba yau ni Kande."

Lantana ta gyara zama ta ce, "Ni ma abin da ya kawo ni kenan kan maganar kuɗin, don ta je ta fasa ihu tana bin Musa kuɗi bashi, kuma sai an biya, kin san dai duk wanda ya zubar da hawayen Lantai a cikin ƙauyen nan sunanshi gawa, don haka na bata asusun da Musa ke tarin kuɗin kayan sallarshi nace ta fitar da nata ta kawo sauran idan ma duka ne to ta ɗauka, mu dai fatanmu Lantai tai farin ciki.
To ganin shiru bata dawo ba yasa Babanshi yace na zo na ji daga gare ta shin sun isa kuɗin koko ? Don wallahi tun ɗazun yake zagayawa banɗaki (Toilet) saboda tararrabin ko Lantai bata haƙura ba, kada ta kira Barbushe mu shiga uku mu duka."

Tagumi Inna Kande tayi don batai tsammanin Lantai zata aikatawa Musa haka ba, duk kunya ta kamata ta rasa abin cewa.

Sallamar Hafiz tasa Inna Kande ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske, sai kuma ta dubi Lantana ta ce, "Ba komi ni zan shigo mu ida maganar ai zuwa anjima bari na nema ma Hafizu abin taɓawa." Ba don komi tayi haka ba sai don kada Lantana tai wata maganar Hafizu ya ji, tasan rai sai ya zane Lantai.
Innarsu Musa ta fice tana murna da zuwan Yayan Lantai tasan yanzu kowa zai saki mararsa yayi fitsari.

SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)Where stories live. Discover now